'''GADAR ZARE!!!'''
_(IT'S ABOUT DESTINY, HYPOCRITES, BETRAYALS)_
~NA~
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh
Gmail: jiddarh012@gmail.com
Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh
*GARGAD'I*
'''MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES , SU KARANTA BA'''
~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*5
Sanu ahankali Cikin ikon Allah na samu gurbin karatuna anan University of Gombe, kullum k'orarin iyayen Mu shine suka inganta rayuwarmu tare da son faranta mana.ni da umar musamman sbd
, muguwar shak'uwar dake tsakanina dashi . dan duk inda ka ganni dole zaka ganshi, komai namu iri d'aya ake mana bbu wani bambanci atsakaninmu shiya wasu suke kiran mu 'yan biyu, babu wani sirri na da Umar bai sani ba.
haka Nina babu wani sirrin sa daban sani ba. Sosai nake matsanancin kaunarsa tare da maidashi tamkar Dan uwana Na jini .yadda nake jin umar acikin raina ko kanina da muka fito ciki guda bana yi masa irin son da nakeyiwa umar ..Akwai wata yarinya a unguwar mu mai suna Yasmeen k'awar k'anwata tace sosai, sun yi masifar shak'uwa da junan su abin ma har ya wuce tunani, rana d'aya na tsinci kaina da mugun k'aunar Yasmeen amma babu wanda na baiyanawa .
Har Umar, nabar dai bar abin a raina. Ina cigaba da renan soyayyarta acikin zuciyata.Haka zalika a b'angaren Umar ashe tuni sun tsunduma cikin soyayya shi da tilon k'anwa ta Ramlat, batare da wanda ya sani,b a.
tuni km har soyayya rsu tayi nisa."Umar wai bazaka raka ni bane, a 'yan kwanakin nan na rasa me kake yi a gida da dare idan nace kazo mu fita sai ka k'i,.Ko meyasa hk ?
murmushi kawai Umar yayi hade da yatsina fusakarsa yana kallon Abdul kasa kasa kana yace " kawai dai ban san fitar ne.
, nafisan na zauna gida tare da Mama da Baba ina taya su hira.
, kallon sa Abdul yayi da alamar rashin yarda atare dashi da km maganar sa.
" kai dai ka san dalilin dayasa kake kunshe kanka ciki gida yana maganar yana tafiya har dai yakarasa fice Daga gidan gabadaya.Sakamakon ruwan saman da ake tsulawa yasa Abdul dawowa gida da wuri, yana danna kai 'cikin d'akinsu yaji hirar soyayya tsakanin Umar da Ramlat, d'an b'ata rai Abdul yayi sosai sannan yace " ke tashi ki fita, da fara'a Ramlat tace" Yaya mai ya faru?
"Nace ki fita ko, da sauri Ramlat ta fita,tana mamakin abinda yayanta yayi .
kallon Abdul, Umar yayi yana shafa sumar kanshi , Abdul yayi dariya yace"Ok dama wannan ne da yake hanaka fita kullum ko ?
ka lik'e a gida,kana sacewa kanwata zuciya ko ?
munafiki to Allah ya kamaka.Dariya shima Umar yayi yace " kodai Allah ya kamamu, "kai da wa?
" ni kai cewar Umar yana dariya, shima Abdul dariya yayi sosai yace " kamar ya ban gane ba.
Kallosa Umar yayi da alamar zolaya ya fara wak'a "Yasmeen abar k'auna ta, dariya Abdul yayi sosai yakai mai duka, suka shiga wasa suna tsokanar junan su, Umar yace " haba d'an uwa har akwai abinda zaka iya b'oye man to ai har na tura mata sak'onka, ta kuma amince, ido Abdul ya zaro waje yace " kai haba?" Wallahi da gaske nake maka sosai Abdul yaji dad'i had'i da rungome Umar ajikinshi yana yi masa godiya.
Washe gari Baba da Mama, da Umar da Abdul da kuma Ramlat da Auta duk muna zaune a parlor, muna hira Abdul ya kalli Mama yace " Mama d'anki fa ya fad'a soyayya, Ramlat naji haka ta zaro ido da alamar tsoro.
, Mama tayi dariya tace" ikon Allah ina kuma ya samu min sirikar?
YOU ARE READING
GADAR ZARE
RomanceA firgice ya mik'e daga inda yake zaune, yana kallon sauran abokanan nasa fuska cike da hawaye idonsa yayi ja sosai Buga kansa ya fara yi ajikin bango yana ihu yana cewa " sun kashe min kowa bani da kowa yanzu, zaman dirshan yayi a k'asa, yana ihu...