54

4.2K 266 12
                                    

'''GADAR ZARE!!!'''

_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_

           ~NA~

*HAUWA A USMAN*
       _JIDDARH_

*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*

Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: Jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh

*GARGAD'I*

'''MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA'''

~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*

*BEST FRIEND FOREVER & EVER*
'''ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA'''
             *~(UMMU AMAN)~*


54

Jin an banko k'ofa yasa Naseer saurin sauka daga kan Zarah had'i gyara zaman blanket d'in a jikin su, ganin Momy yasa Zarah rufe idonta had'i da jan blanket d'in har kanta ta rufe ruf,  a fusace Momy tace " in my rupe?

Kansa ya shafa, had'i da luma hannunsa a cikin sumar kansa a kunyace yace  " I'm sorry Momy, but Momy kema ai ya kamata ace kinyi nocking before ki shigo, tunda kinsan we are husband and wife, bai kamata ki shigo kai tsaye ba, cikin b'acin rai tace " tashi ka fita dan ubanka, shiru yayi baiko matsa ba, tsawa ta daka masa tace " ba magana nake maka ba, i said get out.

" Momy ta yaya za'ayi na fita bayan I'm naked yabi yakan su dake yade a k'asa da kallo, kayan itama tabi da kallo, had'i yin tsaki ta fita, kuka Zarah ta saka mai cin rai, da sauri Naseer ya jawo ta jikinsa yana cewa " ke meye haka, meye na kuka? cikin kuka tace " yanzu da wanne idon zan kuma sake kallan Momy? murmushi yayi had'i da cewa " karki damu kinji duk ma'auta abinda suke yi kenan, itama da Dady kullum sai sunyi, ta yaya duk aka same mu, duk wanda kika ga yazo duniya ta wannan hanyar zo, so karki wani damu dan tazo ta gan mu, dan yanzu zanci gaba da juna sirdi ya k'arasa maganar yana kanne mata ido d'aya.

Da sauri ta d'auki pillow ta jefa mishi tana kuka tace " ni dai please ka fita kar Momy taga ka dad'e kuma ta zata ko ci gaba akayi dariya ya tuntsure da ita yana maida kayan jikinsa,ya fita,  a parlor ya tarar da Momy zaune, suna had'a ido ta zabga masa uwar harara, k'eyarsa ya shafa yana murmushi, sai da ya bari yakai k'ofar bedroom d'insa yace " kije ki rarrashi 'yarki dan tana can tana kuka, sannan ya shige bedroom d'insa, murmushi Momy tayi had'i da mik'ewa ta nufi bedroom d'in Zarah, fuskarta cike da fara'a ta shiga d'akin, a zaune ta iske Zarah tana kuka, bata ko motsa ba balle ta mayar da kayan jikinta, ta dai ja blanket d'in zuwa k'irjinta.

Zama Momy tayi a bakin gadon tana murmushi ta kira sunanta " Zarah, k'ara sunne kanta Zarah tayi batare data amsa ba taci gaba da kukanta, dafa ta Momy tayi tace " karki damu kinji Zarah, hakan shine aure, dan gaba d'aya aure abinda ya k'unsa kenan, duk wata mace da kike gani abinda takeyi da mijinta kenan, kuma abinda yasa kika ga na shigo kuma har na kore shi nayi dan abu biyu, a na farko kece Zarah, saboda ina san nayi miki gatan da kowacce uwa take yiwa d'iyarta a lokacin aurenta, magungunan danake baki ne nake so subi jikin su gama ratsa miki ko'ina na jikinki,  yadda zaki tsumu sosai, ta yadda idan ya kusance ki zai rud'e sosai ya fita daga hayyacinsa, da sauri Zarah ta d'ago kanta tana kallan Momy.

Murmushi Momy tayi mata had'i da cewa " yes my daughter, ni 'yata ta ciki na d'auke ki, ina miki kallan 'yar dana durk'usa na haife ta da kai ne, ba wai ina miki kallan suruka ta ba, kuma in sha Allah ni zan maye miki gurbin Momynk Zainab da mahaifiyar ki, dan ina tsananin jin tausayinki Zarah, ina matuk'ar tausayawa rayuwarki,, dan Allah ya jarrabeki da abubuwa da dama Zarah, Momy ta k'arasa maganar hawaye na zubo mata.

GADAR ZAREWhere stories live. Discover now