14

4.2K 211 2
                                    

'''GADAR ZARE!!!'''

_(IT'S ABOUT DESTINY, HYPOCRITES, BETRAYALS)_

          ~NA~

*HAUWA A USMAN*
        _JIDDARH_

*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*

Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh

*GARGAD'I*

'''MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO  UNDER AGES , SU KARANTA BA'''


~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*

14

A falo yayi zaman dirshan yasa kuka kamar wani k'aramin yaro, sautin kukan sa Hajiya da Hamza suka ji suka fito, " subhanallahi Yaya lafiya meke faruwa?  jajayen idonsa ya d'ago ya zubawa Hajiya da Hamza ya kasa koda furta kalma d'aya, sosai hankalin Hamza yayi mugun tashi, Hajiya tayiwa Khamal tambayar duniya amma yak'i magana sai faman aikin kuka yake.

Hakan ne yasa Hamza fashewa da matsanancin kuka, cikin kuka yace " Yaya duk duniya bamu da kowa daya wuce mu ukun nan, mu kad'ai  mu kad'ai muka mallaki junan mu, Yaya idan baka fad'a  mana damuwarka ba wazaka sanarwa, Yaya please ka sanar damu matsalarka tun kan mu shiga fiye da damuwarka.

Kallon Hamza Khamal yayi, cikin kuka yace " Bro wai yau ni ake kira da cima zaune, k'aton banza, wanda har yanzu ba'a yaye shi ba, ya k'ara fashewa da wani kuka yace " wai bani da aikin yi sai yawon majalisa,.
nine zauna gari banza, yadda yake kukan ne ya bawa Hajiya tausayi itama ta fashe da kuka ta rungume shi tana tambayarsa waya jefe shi da wad'annan bak'ak'en maganganun, cikin kuka ya sanar da Hajiya da Hamza duk abinda ya faru tsakaninsa da Dadyn Fateeha,  bai b'oye musu komai ba, cikin kuka Hamza ya rungume Hajiya da Khamal, yace " Yaya kayi hak'uri in sha Allah wata rana sai labari.

" Nasani Bro, Khamal ya fad'a yana gogewa Hamza da Hajiya hawayensu, sosai su Hamza suka lallashi Khamal, sai da suka kwantar mishi da hankali sosai, har suka saka shi dariya,  cikin barkwanci Hamza ya mik'e yace " Yaya banci abince ba kai nake jira ka dawo ka bani a baki, nace Hajiya ta bani tace wai nayi girma, shine na bari ka dawo ka bani dan nasan Yaya na bazaice nayi girma ba ko?

Dariya Khamal yace " ah ina ni ina cewa Bro yayi girma ai da kaina ma zan d'anko na baka abakin, ya fad'a yana shirin mik'ewa, da sauri Hmaza ya mik'e yace " a'a Yaya ni zan d'auko kuma na baka a biki, Hajiya na kallonsu tana dariya, a baki Hamza ya rink'a bawa Khamal abincin har ya k'oshi, haka suke tun suna yara, duk wanda yayi fushi to ranar a baki za'a  bashi abinci, gidan ya taso cikin farin ciki da walwala.

Fateeha kuwa da taji  ne yasata komawa part Dady, bata iske kowa ba a falon, dan haka da sauri ta koma d'akinta dan ta kira Khamal a waya, ta kira shi ya kai sau 30  amma bai d'aga ba, iyakar tashi hankalin Fateeha ta tashiga sosai, don tasan tabbas ba lafiya,ba hankalinta duk yak'i kwanciya, gabanta sai fad'uwa, yake .
Allah .
Allah kawai take gari ya waye, dan ko bacci ta kasa.

Washe gari kowa a falo ya iske Fateeha tana ta faman jiran fitowar Dady, dan ko kayan jikin ta bata canja ba, duk wanda ya ganta yasan bata cikin nutsuwarta, kwana tayi tana kiran Khamal amma yak'i picking, zama ma gagarar ta yayi ta mik'e tana ta kai kawo a falo, tana cikin hakan taji motsin saukkowar Dady, ido ta k'urawa step d'in, Dady yana d'ora idonsa akan Fateeha ya murtuke fuska wai dan kar tayi masa maganar Khamal.

Sosai ya b'ata rai, a dining table ya zauna ko kallon inda take bayyi ba, ga mamakinsa ko zama bai k'ara yi ba, balle akai ga cin abinci, bata ko gaidashi ba cikin murya mai rauni yaji tace "  Dady ya kukayi da Khamal ne please?

GADAR ZAREWhere stories live. Discover now