'''GADAR ZARE!!!'''
_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_
~NA~
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh
Gmail: Jiddarh012@gmail.com
Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh
*GARGAD'I*
'''MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA'''
~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO**BEST FRIEND FOREVER & EVER*
'''ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA'''
*~(UMMU AMAN)~*55
A haukace Naseer ya mik'e yace " waye ya mutum? please karku ce min Zarah, dafa shi Doctor d'in yayi had'i da cewa " am sorry, zuciyarta ce ta buga, cikin tashin hankali Momy ta kalli Doctor, batare datace komai ba, tun daga nan Naseer bai kuma cewa komai ba, ya koma ya zauna kamar wani sakarai, ganin an fito da Zarah daga emergency room fuskarta da jikinta rufe da farin k'yalle yasa Ikram d'ora hannu aka had'i da karma uban ihu ta sulale k'asa sumammiya, da sauri nursing sukayi kanta suka shiga bata taimakon gaggawa, Dady na hawaye ya ciro wayarsa daga aljihu ya kira Alhaji Abdullahi murya Dady na rawa yace " Assalamu Alaikum, jin yanayin muryarsa yasa Alhaji Abdullahi dake kishingid'e saurin tashi zaune, ba tare daya amsa sallmar ba yace.
" El-Mustapha lafiya kuwa naji ka haka?
Da kyar Dady ya daure yace " Allah ya yiywa Zarah rasuwa, cikin mummunan tashin hankali ya mik'e tsaye yana cewa " innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, cikin rawar murya yace " kuna ina yanzu?
" Muna asibiti amma yanzu zamu karb'i gawarta mu koma gida, "ka sanar da iyayen nata?
" No ban sanarwa da kowa illa kai dana sanar yanzu, " to shikenan mu had'u a gidan, a rud'e Alhaji Abdullahi ya mik'e yana sanarwa da Kakar Zarah, tana jin rasuwar Zarah ta fasa kuka, yana fituwa harabar gidan ya fara kwalawa driver kira kamar zai tashi sama, ana tafiya yana yiwa driver magana akan ya k'ara taka motar dan shi gani yake kamar ba tuk'in yake ba, a d'imauce Alhaji Abdullahi ya kira Abban Zarah yace su had'u yanzu a gidan El-Mustapha.
Duk wasu k'adoji da ake bi wajen karb'ar gawa Dady ne yayi aka basu gawar Zarah suka nufi gida da ita, har lokacin Naseer yayi jigum kamar wani tab'ab'b'e koda za'a shiga mota sai Momy ta rik'o hannunsa ta shigar dashi.
Haka kawai Abban Zarah yaci gabansa na muguwar fad'uwa, kwata-kwata hankacinsa yak'i kwanciya, tsoro da fargaba sun dirar masa a cikin k'ank'anin lokaci, dan haka ya kasa tuk'in yasa driver ya tuk'a shi.
A mota Dady ya kira Mannir yace masa duk abinda yake yi ya bashi nan da 10 minutes su had'u a gida dashi da Zainab su zo yanzu, a tare Dady da Alhaji Abdullahi, Abban Zarah suka isa gidan, ana yin parking Naseer ya fito sukuku ya shige bedroom d'insa ya rufe, yayi zaman dirshan a k'asa, ya kasa yin komai dan kwakwalwarsa ta daina aiki, shi bai ma san waye shi ba, da gudu Ikram ta fito ta fad'a jikin Alhaji Abdullahi tana gunjin kuka, fito da gawar Zarah akayi daga cikin mota aka shigar da ita main parlor gidan, shi dai Abban Zarah tsaye yayi cikin mutuwar dan har yanzu bai san takamai-mai abinda ke faruwa ba.
Cike da matsanancin farin ciki Mannir ya shigo gidan yana d'okin ganin Na'eem, Zainab ko sai cika take matsewa, tun daga harabar gidan take jiyo ihuuuu Ikram tana kuka, da sauri Mannir da Zainab suka k'arasa shiga gidan cikin matsanancin firgici, da sauri Ikram ta saki jikin Alhaji Abdullahi tayi wajen Zainab tana kuka tace " shikenan Momy Zarah ta tafi ta barmu, Momy ZARAH TA MUTU!!!.
YOU ARE READING
GADAR ZARE
RomanceA firgice ya mik'e daga inda yake zaune, yana kallon sauran abokanan nasa fuska cike da hawaye idonsa yayi ja sosai Buga kansa ya fara yi ajikin bango yana ihu yana cewa " sun kashe min kowa bani da kowa yanzu, zaman dirshan yayi a k'asa, yana ihu...