'''GADAR ZARE!!!'''
_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_
~NA~
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh
Gmail: Jiddarh012@gmail.com
Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh
*GARGAD'I*
'''MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA'''
~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO**BEST FRIEND FOREVER & EVER*
'''ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA'''
*~(UMMU AMAN)~*49
A haukace Naseer ya k'asa wajen yasa hannu ya fisge Zarah daga hannun Mannir ya kalle shi ido cikin ido yace " wallahi duk abinda ya same ta bazan tab'a yarda ba sai nayi shari'a dakai, tsabar baka da imani ka zage iya k'arfinka da Allah ya baka a matsayinka na namiji kayiwa mutum wannan mummunan dukan sai kace ka samu dabba.
Murmushi Mannir had'i da cewa " ai dole kaci haka tunda ka lallab'a ka d'urwa 'yar mutane ciki, shege munafuki mazinaci, masik'i kawai, abinda dama damai bak'ar zuciya, gadan-gadan Naseer yayi kan Mannir dai-dai lokacin da iyayen nasu ke k'arasowa, tsawa Dady ya dakawa Naseer had'i cewa " stop! Karka soma ina ruwanka da shiga tsakanin su ba tare ka gansu ba, yayi mata duk abinda zai iya, idan ma kashe ta zayyi gashi nan gata, tunda bashi da hankali yaga idan hukuma zata kyale shi, yayi maganar yana kallan Mannir dake ta faman huci.
Aunty Zainab dake tsaye tunda aka fara abin bata motsa ba sai taga Naseer ya sumgumi Zarah yana niyyar yin waje da ita, da sauri tasha gabansa tana jefansa da kallan tsana tace " ina kuma zaka kaita? bayan ka riga da ka gama lalata, kallanta yayi ido cikin ido yace " kamar yayafa?
"Ni zaka kalli ido na kace min kamar yayafa? sau nawa ina kama da ita, a zabure Dady ya juyo yana kallan ta yace " Zainab mekike kice?
Hawayen fuskarta ta fara sharewa sannan tace " eh Dady gashi nan ku tambaye shi idan k'arya nake masa, wallahi sau uku ina kamashi yana romancing d'inta, kafin Dady yayi magana Naseer yace " da kika ganni ina romancing d'inta, kin ganni a kanta ne? ko kuma kin tab'a kamani akan ruwan cikinta ina sex da ita ya fad'a idansa cikin nata, dama Naseer akwai bak'ar zuciya, ganin ransa yayi masifar b'aci kuma sun san idan ransa ya b'aci haka idonsa rufewa yake yana iyayin komai yasa kuwa yin shiru, a hankali ya sunkuya ya sab'i Zarah a kafad'a yayi waje, Dady da Momy suka bi bayansa.
Amma kafin su iske shi ya figi motar a 360, da sauri suka shiga mota suka bi bayansa, a k'ofar wani had'add'e private hospital yayi parking, da hanzarinsa ya fito ya shiga cikin hospital d'in bai jima suka fito da Doctor da nursing, kai tsaye emergency aka wuce da Zarah, tsaye Naseer yayi a k'ofar emergency room d'in yana safa da marwa, a haka su Dady suka k'araso, da sauri suka nufe shi, Dady yace " ya ake ciki ne?
Naseer ya bud'e baki zayyi magana Doctor ya fito a gigice da sauri Naseer ya tare shi, Doctor yace " ina mijinta? batare da fargabar komai ba Naseer yace " nine?
" accident d'in data samu gaskiya ya munana dan harda karaya biyu, a razane Naseer yace " what!!! KARAYA!!! a d'an tsorace doctor yace " eh k'afa da hannu, zaman dirshan Naseer yayi a wajen a k'asa ya fasa gigitaccen kuka, Kallan sa Doctor kawai yake yana mamakin namiji kamar Naseer amma da karyayyar.
'''Ni ko nace hmmmmm Doctor baka san so bane'''
Sosai zuciyar Dady da Momy ta karaya, a hankali Dady ya cewa Doctor " kuyi duk abinda ya kamata kawai, ku d'orata, "ok doctor kawai yace ya juya ya koma cikin Emergency room, a hankali Dady ya durk'usa a gaban Naseer ya rungumo shi jikinsa yana lallashi yayinda Momy ke shafa kansa, a zuciyar Dady yana jinjina tsantsan rashin imani irin na Mannir, cikin kuka Naseer yace " Dady kana jin Doctor ma cewa had'ari ta samu dan shi a tunanin sa accident ne, babu wanda zayyi tsammanin wannan duka ne, Dady Mannir kwata-kwata bashi da imani, baya ganin akwai ciki a jikinta idan wani abu ya same ta fa, wallahi Momy bazan yarda ba sai nayi shari'a dashi kona rama mata, daga Momy har Dady babu wanda yace k'ala.
YOU ARE READING
GADAR ZARE
RomanceA firgice ya mik'e daga inda yake zaune, yana kallon sauran abokanan nasa fuska cike da hawaye idonsa yayi ja sosai Buga kansa ya fara yi ajikin bango yana ihu yana cewa " sun kashe min kowa bani da kowa yanzu, zaman dirshan yayi a k'asa, yana ihu...