'''GADAR ZARE!!!'''
_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_
~NA~
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh
Gmail: Jiddarh012@gmail.com
Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh
*GARGAD'I*
'''MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA'''
~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO**BEST FRIEND FOREVER & EVER*
'''ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA'''
*~(UMMU AMAN)~*50
Da k'arfi Naseer ya kira sunanta yana jijjiga ta ZARAH!!!!!, a haukace yake kwalawa likita kira iya k'arfinsa yana ihuuuun hauka, a wajen Aunty Zainab ta zube a k'asa akan gwiwoyinta tana hawaye amma ta kasa kukan, a razane Mannir ya fita yana kwalawa Doctor kira a matuk'ar firgice, da sauri Doctor da Nursing suka shigo, gam Naseer ya rik'e tana ihuuu, sai da kyar aka b'amb'are daga jikinta aka shigar da ita emergency.
Shak'ar wuyan Mannir yayi yana ihuuu, kwata-kwata baya cikin hayyacinsa da nutsuwarsa ya gama fita daga hankalinsa, ya shak'e shi iya k'arfinsa yana cewa " wallahi idan Zarah ta mutu kai ma sai ka bita, matuk'ar ina raye bazan bar makashin Zarah yaci gaba da rayuwa cikin farin ciki da kwanciyar hankali, sai dai nima a kashe ni, kakarin mutuwa Mannir ya shigayi yana kokawar kwace kansa amma ya kasa, Dady da Momy na zaune babu wanda yayi yunk'urin komai balle yayi magana, sai Abban Zarah ne yaje yana k'ok'arin kwace shi, amma ina ya kasa, wani gigitaccen mari Abba ya yarfawa Naseer, a kid'ime Naseer ya saki Mannir yayi kan Abban, ganin Abba ne yasa shi sakinsa da sauri yana yarfa hannu.
Ya durk'ushe a wajen yana kukan mutuwa, gaba d'aya wajen kowa tunanin wannan wanne irin ne Naseer yake yiwa Zarah, duk anyi jugum-jugum a k'ofar emergency room d'in, babu mai cewa k'ala, illa Naseer dake ta faman hawaye yana jin zuciyar sa kamar zata buga.
Iya wuya kam Zarah tasha kamar zata mutu dan sai da ta gwammaci mutuwarta akan ci gaba da rayuwarta, su kan su Doctors d'in sai da suka sha bak'ar wahala kafin su samu numfashinta ya dawo dai-dai, su kansu sun tausaya mata ganin irin bak'ar wuyar dataci, sai akayi 3hrs sannan aka fito da ita, da sauri Naseer ya mik'e ya nufi gadan da ake turata a ciki, yana binsu a baya har suka mayar da ita d'akinta, da sauri Naseer ya k'arasa bakin gadon ya zauna ya rik'o hannunta cikin nasa, kowa ya tsaya cak yana kallan ikon Allah, Doctor ya sauke ajiyar zuciya yace " jininta ne ya hau sosai, kuma tana cikin matsananciyar damuwa ayi k'ok'ari arink'a kwantar mata da hanklinta da zuciyarta nagaf da tab'uwa.
A hankali Zainab taje bakin gadon ta shafa kan Zarah tana hawaye, zuciyarta nayi matuk'ar k'una da tafasa, tana jin k'irjinta kamar zai fashe saboda tsananin zafin dayake yi mata, ita kanta tasan tana tsannin k'aunar Zarah, amma dole tayi nisa da ita, mayar da kallanta tayi wajen Mannir tace " muje, cikin muryar kuka ta kalli Ikram tace " ki tsaya kiyi jinyar 'yar uwarki har ranar za'a sallameta zan sa driver ya kawo miki kayanki da duk abinda kike buk'ata kinji, cikin sanyin jiki Ikram tace " to Momy, dan tana tsananin san Zarah itama a ranta fiye da tunanin.
Harta kai bakin k'ofa ta juyo ta kuma kallan Ikram tace " karki anyi haka kice zakiyiwa Zarah wani abu marar kyau, idan har naji kona gani nida kai na zan kashe ki wallahi, dan har yau har gobe Zarah tananan a zuciyata daram kamar da babu abinda ya ragu dan Zarah bata da uwa sama da ni Zainab ta fad'a kallan saitin Naseer, kuma har bada baza'a tab'a canjawa tuwo suna ba, murmushi Ikram tayi tace " haba Momy yanzu har kina tunanin zan iya yiwa wani abu mummuna, duk duniya fa bani da 'yar uwa ko d'an uwa kamar ta, tare muka taso kamar twice muka sha nono d'aya, Momy Duk duniya Zarah bata da kamar mu muna bamu da wanda yafita duk wanda yake tak'amar yana santa ko sanin ciwonta a bayan mu yake Momy dan munfi kowa sanin zafinta.
YOU ARE READING
GADAR ZARE
RomanceA firgice ya mik'e daga inda yake zaune, yana kallon sauran abokanan nasa fuska cike da hawaye idonsa yayi ja sosai Buga kansa ya fara yi ajikin bango yana ihu yana cewa " sun kashe min kowa bani da kowa yanzu, zaman dirshan yayi a k'asa, yana ihu...