75

4.3K 219 3
                                    

'''GADAR ZARE!!!'''

_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_

           ~NA~

*HAUWA A USMAN*
       _JIDDARH_

*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*

Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: Jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh

*GARGAD'I*

'''MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA'''

~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*

*BEST FRIEND FOREVER & EVER*
'''ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA'''
             *~(UMMU AMAN)~*



75

Cikin mutuwar jiki Naseer  ya d'aga masa hannu had'i da matsar da ita gefe,
ba tare da yace masa komai ba,
ita ko duk ta rirrik'e Naseer kamar wacce za'a kashe,
Zainab dake durk'ushe a k'asa tana kuka ta mik'e cikin zafin nama taje gabansa,,
tace " da kake mik'a hannu me zaka kuma yi mata?

Ko..... shiru tayi saboda yadda take jin yanayin jikinta ya canja,
k'irjinta na sama da k'asa da kyar tace " tsakani na da kai Mannir Allah ya isa, Ubangiji yayi mana sakayya ni da Zarah, da Ikram,
a hankali numfashinta datake iyakar k'ok'arin fisgowa ya d'auke gaba d'aya ta zube k'asa a sume,
mik'ewa Naseer yayi da Zarah tsaye a jikinsa, ya fita ba tare daya furta koda kalma d'aya ba,
da sauri Mannir ya bi su suna gaf da barin parlorn ya durk'ushe had'i da rik'o k'afafuwan su,
cikin matsanancin kuka yace " please ku yafe min, idan baku yafe min ba wallahi na shiga uku, yanzu ma kuna ganin yadda Allah yayi dani da rayuwa ta,
a hankaki Nasser ya durk'usa yasa hannunsa ya zame rik'on da Mannir yayiwa k'afuwansu,
Dady da Momy kasa motsi su kayi saboda kunya da tashin hankali,
Alhaji Abdullahi da Abban Zarah sauran mutane suka mik'e jiki a sanyaye,
a hankali Abban Zarah ya sunkuya ya sungumi Zainab dake kwance a sume yayi waje da ita ba tare da kowa yayiwa kowa magana ba,
suka fita ko a mota babu wanda yayi magana har suka k'arasa hospital da Zainab.

Da sauri aka karb'e ta aka shigar da ita emergency an d'auki lokaci mai tsayi kafin Doctor ya fito ya sanar da su,
ta samu mutuwar b'arin jiki saboda tsananin tashin hankalin data shiga,
sosai hankalin su yayi masifar tashi, Abban Zarah yayi kuka a b'oye har ya godewa Allah,
bak'in cikinsa biyu na farko halin da Zainab ke ciki,
na biyu abinda mannir yayiwa Zarah,
lalle Mannir ya cika cikkekken maci amana butulu, mugu macuci azzalumi,
amma ba komai shida Allah, tunda gashi nan tun yanzu ya fara girbar abinda ya shuka,
bedroom Nasser yakai Zarah, ya ajiye ta akan bed sannan ya d'auko mata ruwa a fridge ya bata tasha jikinta sai rawa yake yana tsuma, a hankali Naseer ya zauna a kusa da ita ya jawo ta jikinsa ya rungume ba tare dayace komai ba,
sai ajiyar zuciya da yake ta faman saukewa, ya k'i yin magana ne tun a parlor saboda yasan halinsa da bak'ar zuciya,
muddin yace zayyi magana to komai ma b'aci zaiyi, dan ba'a k'are lafiya ba,
dan haka ya zab'i yayi shirun dan shi ya fiye masa sauk'i.

A gigice Zarah ta d'ago kai ta kalli Naseer tace " dama na fad'a maka Na'eem ba d'anka bane,
ko sau d'aya ban tab'a alak'anta ka dashi ba, kwata-kwata zuciya ta tak'i yarda shi d'anka ne,
dan nasan bazaka tab'a yi min haka ba, ina da cikekken yak'ini akan ka Uncle,
na yarda dakai d'ari bisa d'ari, nasan bazaka tab'a cutar da ni da rayuwa ta ba,
dan Allah Uncle ka d'auke mu bar nan, muma tafi ko'ina ne, Uncle bazan iya ci gaba da zama anan ba,
na tsani garin nan, na tsani kowa da yake ciki, ni kai na ma na tsani kai na,
ganin yadda take magana a burkice duk ta fita daga hayyacinta yasa Naseer mai da ita k'irjinsa ya rungume,
had'i da runtse idansa da k'arfen tsiya, yana shafa kanta,
yana tunanin yadda rayuwa da duniya ta canja,
da yadda mutanen cikin duniya suka zama marasa amana, da alk'awari,
ashe duk yadda kake da mutum yana iya cin amanar ka,
duk kusancinka da d'an Adam da alak'ar dake tsakanin ku yana iya cutar dakai,
to kau idai haka ne duniya da mutum ba abin yarda bane,
Dady da Momy sun kai magrib anan babu wanda iya furta koda kalma d'aya a cikin su,
kowanne yayi jugum yana sak'a abubuwa da dama a ransa,
kiran sallar magrib da akayi ne yasa dukkan su mik'ewa jiki a matuk'ar sanyaye suka bar parlor'n.

GADAR ZAREWhere stories live. Discover now