Babi na biyar

813 51 0
                                        

Yazeed ko Yaseer

Ayshart Farouq

Nagarta writers association.

5

Guri ta samu ta zauna tare da cewa. "Abba Ina wuni. Gani Ya Sageer ya ce nemana"

"lafiya kalau Afnan" ya karɓa yana kallonta cikin fari'a da kulawa irin ta ɗa da mahaifi duk da ta ɗan fuskance akwai wani abu shimfiɗe kan fuskarsa.

Gyaran murya ya yi kafin yayi magana yana kallon Ibrahim da
Sagir.
"Dama ba komai ya sanya na taraku anan ba face ina so ku zamo shaida a gare ni akan Afnan a matsayinku na yayunta"

Gaban Afnan ya yi wata irin faɗuwa mai tsanani. To me Abbanta ke nufi ne da su zamo shaida a kanta?.

Tsura mishi ido ta yi cikin
tsanani tashin hankali don jin me zai faɗa. Sai dai wannan Karon kafin ya ce komai  baki ɗaya saida  annaurin fuskar shi ya chanj.

  "Alhamdulillahi, na san dai dukan ku na ba ku tarbiya gwargwadon ikona musamman ma ke Afnan" ya faɗa yana nuna ta da yatsa.

Cigaba ya yi da magana. "Allah ne shaidata babu wani dare da zan runtsa face nayi tunani matsayin hakkinki da ya rataya a kaina ba. Wasu lokuta da dama har  banma sanin lokacin da hawaye suke zubo min idan na tuna cewa ke ɗiya mace ce kuma tarbiyantar dake yanada
matukar wahala, saboda idan kika lalace tamkar duka al'umma ne  suka lalace. Haka kuma idan kika gyaru tamkar duka al'umma ne suka gyaru.

Ban fahimce abunda nake mi ki ina  shiga hakkin ki ba sai jiya
da mahaifiyarki take ƙara tunasar da ni. Ban gane maganarta gaskiya ce ba  saida na ji kina waya jiya da misalin ƙarfe biyu na dare"

Wannan karon kam Afnan fashewa ta yi da kuka tana kallon mahaifinta. Cikin ranta kuwa sai cewa ta
ke yi.
'Na shiga uku ni Afnan yanxu duk Abba ya ji maganar da muke yi jiya da Yazid?'

'Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un' ta faɗa cikin ranta tana mai tuna firar
da suka yi jiya  da Yazeed duka akan aure ne. Sai dai damarta ɗaya hakurin da ta riƙa baiwa Yazid akan cewa su yima iyayen su biyayya
suyi abunda suke so, ita kanta tana bukatar aure dan dai ba yanda zata yi ne,.....

Katse Mata tunani Abba ya yi da cewa, "Hakika sai jiya na tabbatar da cewa aure shine mutuncin duk wata ɗiya macce da take rayuwa a doron kasar nan. Tabbas Afnan na tauye miki incinki kuma na shiga rayuwarki da yawa na hanaki walwala da sukuni, akan kawai in gina miki  rayuwarki dan zamowa Mai dogaro da Kai ko bayan kin rasa ni ko yayunki.

Ashe ban san ƙara ruguza miki rayuwa na yi ba. Ta hanyar tsananin
da nake yi miki gashi kin koyi yin ƙarya. Haka ma karatun da nake so ki yi shi kansa yanzun ba yi kike yi ba
soyaya kike yi right?"
Ya faɗa idanuwansa na kanta.

Girgiza mishi Kai ta shiga yi tamkar ƙadangaruwa. "A'a Abba dan Allah
ka yi haƙuri ka yi mini rai wlh Allah bazan ƙaraba. Wayar tawa ma ka karɓe. Dan Allah Abba duk wani Abu
da zaka yi min kamin amma Dan Allah Abbana kada ka yi fushi dani. Na yarda ka hukunta ni ta ko wace
hanya amma Abba kada ka hukuntani ta hanyar yin fushi Dani da Allah" ta ce tana mai fashewa da  kuka mai tsananin gaske.

Mikewa mahaifin nata ya yi tare da komawa kusa da ita ya jawota jikinsa
"Yi shiru Afnan baki yi min laifin Komai ba, facema birgeni da kika yi da kika nuna biyayya ga iyayenki yafi komai muhimmanci a gurin ki duk da
cewa wani wuri kin  kaucewa iyayen naki. Tabbas nafi kowa laifin akan abunda kika aikata na saving number namiji da sunan mace"

Juyawa yayi tare da kallon Mommy tare da su Ibrahim "Ku zama shaida a kaina. Daga yau  ni Usman na baiwa
Afnan damar
ta gayawa wanda take so ya turomin magabatansa ayi magana. Ko gobe suka tashi kuma zan aurar da ita goben".

Wata irin ɗagowa ta yi tana kallon mahaifin nata. Duk da cewa maganar tayi mata daɗii amma ita har ga Allah ba haka ta so ba.

Gyaɗaa mata Kai ya yi yana murmushi.  "Am serious Afnan ki ce masa ya turo min magabatansa saboda  infita hakkinki.

Ganin bata ce komai ba yasa ya ce.
Koda bai shirya ba kawai ina so inga magabatansa hakan  zai sanya in
yadda da cewa da gaske yake neman ki.

Wata irin kunya ce  ta Kama Afnan "A'a Abba ni kam nafasa karatuna zanyi"

"Ka ji min ja'irar yarinya? karatun ma da kika jawa baya ta yaya za ki yi karatun?. Ai karatu kuma sai dai idan mijin naki ya amince. Saboda a yanda kika buɗe idon nan idan muka barki zamu tabka babban kuskure a rayuwarmu.  Cewar Mommy.

Abba ya ce, "A'a zainab ko gaba bama ganin komai da yardar Allah. Afnan ai aure baya hana boko hakama boko baya
hana aure kaman yanda mahaifiyar ki ta gayamin.
Idan har minjin ki ya baki damar kici gaba da karatu walillahil hamdu, idan ma hanaki ci gaba
yayi duk daya ne. Allah dai yamana jagora a rayuwarmu kawai"
Dukan su suka karba da "Amin"


Yazeed ko YaseerOpowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz