Babi na sha biyu

819 54 6
                                    


"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un" Abba ya shiga nanatawa tare da kwalawa momy kira.
jin kiran da yake mata ne yasa ta tashigo ɗakin nasa cikin sauri.
ganin Afnan kwance tamkar matatta yasa ta ruɗe ta shiga tambayar Abba "me ya faru da ita ne Alhaji"

Cikin dakakkiyar murya ya ce "maganar yaron nan ce na gaya mata"

"Innalillahi wainna ilaihirraji'un ni Zainab yau naga ta kaina, amma wannan yaron wallahi anyi tsinanne yanzu kirikiri yana so ya kaimu ya baro, wallahi idan ya kashe min yarinya sai na yi dhari'a dashi"

Ganin tamkar momy ta fita hayyacinta tana ƙara ɗaga masa hankali yasanya ya yi saurin rarume ruwan da ke kusa da shi ya shiga zuba mata yana kiran sunanta.

A hankali ta buɗe idanuwanta tar kan mahaifinta, kanta take ji wani irin gingirigim da shi. Yunƙurawa ta yi zata tashi Mommy ta yi saurin kamata ta tayar da ita tana mata sannu. Kallonsu ta shiga yi tamkar ranar ta fara ganinsu kafin abubuwan da suka faru su fara dawo mata.

Kallon Mommy ta yi idanuwanta cike da hawaye. "Mommy kin ji wai Yazid yafasa aure na"

Shafa kanta Mommy ta yi tare da shafe mata kwallar da ta zubo saman fuskarta.
"Ki yi hakuri Afnan komai mukaddari ne daga Allah. Kar ki damu Insha Allahu sai Allah ya saka miki tunda baki mishi kumai ba. Ki yi haƙuri ki barwa Allah komai kin ji"

Gyaɗa kanta ta yi hawaye na sake silalowa daga fuskarta. "Mommy Yazid ya cuce ni ya cuce rayuwata ya........... "
Bata ida faɗa ba ta ji zuciyarta ta hautsine, wani irin amai ya taso mata, da gudu ta yi waje tana sheƙasa tamkar zata amaye 'ya'yan hanjinta gashi dama cikin ba komai a cikin sa.

Momy da ke bayanta sai sannu take yi mata cikin ranta tana matukar jin tausayin ɗiyar tata s da ta fada tarkon soyayya gashi kuma an yi breaking heart ɗinta. Tabbas ta san yanda breaking heart yake da tsananin zafi da baƙin ciki saboda itama ta taɓa experience ɗinsa.

Sai da Afnan ta ƙare aman baki ɗaya sannan momy ta riƙata ta kaita ɗaki. Cikin ƙanƙanen lokaci jikinta duk ya gashe yayi zafi sosai. Ƙallo ɗaya zaka mata ka fahimce tana cikin matsanancin hali.

Ɗakin Abba Mommy ta koma ta ce. "Alhaji ina ganin fa ya kamata aje da yarinyar nan asibiti a dubata don naga jikinta ya yi zafi sosai saboda dama can ba lafiya gareta ba ga kuma ƙarin wannan matsalar, kar a zuba ido a ƙyaleta wani abu yazo ya sameta daga baya"

Abba ya ce, "maganar da na gama yi kenan. Yanzu dai abunda za'ayi ki je ki bata abinci ta ci nama Ibrahim waya tun ɗazu yace zai zo ya dubata da ya kammala aikinsa"

Wurinta Mommy ta koma ta samu da ƙyar ta tilasta ta ta ci abinci. Amma tana kammala cin abincin ko minti biyu masu kyau bai samu yi cikin hanjinta ba ta amayar da shi. Ba ƙaramin tashin hankali Mommy tashiga ba, zama ta yi sosai ta shiga yi mata nasifa don a ganinta duk saboda damuwar da ta sawa kanta ne ta sanyata shiga wannan halin. Saida taga hankalinta ya ɗan kwanta sannan ta tashi tabar ɗakin tana mai yi mata addu'ar samun sauƙin zuciya.

Tana fita Afnan ta ɗora daga inda ta tsaya, saboda kuka ta shiga yi sosai tamkar ranta zai fita.
wata irin tsanar Yazid da soyayyar shi suka riƙa bijiro mata lokaci ɗaya.

Haka wata zuciya ta riƙa faɗa mata cewa dama can ba sonki yake yi ba cutar ki kawai ya yi, ya raba ki da mutuncinki. Dama can jikinki kawai yake so kuma ya samu.
A hankali ta furta "Allah ya isa tsakanina da kai Yazeed"
Haka dai taci gaba da kuka da surutai kala kala ita kaɗai tamkar wata mahaukaciya.
Cikin wannan halin ne Ibrahim ya zo ya sameta, shi kanshi ba karamin tausayi ta bashi ba, allura kawai ya yi mata tare da wasu magungunna sannan ya tafi.

Abba da momy kuwa haka suka sanyata gaba sunata kwantar mata da hankali da magangannu masu daɗi har ta ji ta ɗan fara samun relief cikin ranta.
(Iyaye kenan Allah ya ƙara mana son iyayen mu baki daya. Ameen)

Bayan kwana biyu da faruwar wannan. Sosai ta ragewa kanta damuwa sai dai ba wani chanji da aka samu kan rashin lafiyarta, saima abunda ya ke ƙara yin gaba.
Zazzaɓi da amaye amaye ba a ma magana.
Abin ba ƙaramin tayar da hankalin iyayenta ya yi ba. Shi yasa yau Abba ya yanke shawarar kawai ya kira likitansu don ya dubata yaga abunda ke damunta kasancewar Ibrahim ya yi tafiya duk da cewa ga yau ɗin shima zai dawo.
Su baban tashin hankalinsu bai wuce ace ciyon zuciya ne ya kamata ba kan damuwar da ta sanya kanta a ciki.


Yazeed ko YaseerWhere stories live. Discover now