Afnan ba ta yi ƙasa a guiwa ba ta je ta sanar da mahaifinta yanda
suka yi da Yazid ɗin, saboda yanzu sam bata son wata harakar ɓoye ɓoye a tsakaninta da shi.Abban nata ya ji daɗi sosai na yanda ta gaya masa, nan take ya bata damar ta gaya masa ya zo. Sai dai bai aminta da yawan zuwa ba tare da an tsayar da magana ba.
Haka dai Afnan ta je ta sanar da Yazid. Ya yi murna sosai da jin maganar da ta gaya masa, ai kuwa ƙarfe takwas daidai ya iso gidansu.
Lokacin Afnan ta ci kwalliya tamkar
wadda za ta je wajen gasar kyau. Falon baƙi ta kaishi yayin da ta haɗa
masa kayan motsa baki iri iri.Suma ne kawai Yazeed baiyi ba, wurin kallon Afnan, lokacin da ta shigo cikin falon tana takunta mai jan hankali, da ya zamo halitta a gareta.
Sosai ta tafi da tunaninsa, da Imaninsa saboda tunda yake tare da ita bata taɓa yi masa kyau irin na yau ba.
Sam bai san ya miƙe daga inda yake zaune ba sai da yagansa daf da ita ta zuba masa fitinannun idanuwan nan nata tana kallonsa.
Yasan kallon da take masa. Ya kuma san ma'anarsa amma sam bazai fasa abunda ya yi niya ba.
Cikin daƙiƙu ƙalilan sai gata kwance saman ƙirjinsa. Rungumeta yayi sosai yana shinshinar kamshinta, duk ilahirin jikinsa rawa yake yi. Idanuwansa sun yi jajur tamkar
mayunwacin maye.Cikin tsananin tashin hanakali Afnan ta tureshi daga jikinta, saboda sosai abun nashi ya girme tunaninta.
Cikin ɓacin rai take magana. Mi ye haka ne Yazid? Me yasa kai sam baka tsoron aikata abunda Allah ya yi hani da shi ne? ni ba matarka ba ce, me yasa ko da yaushe kake son taɓa min jikina ne?"
Dafe kansa ya yi da hannayensa duka biyu. "O my God! Me nake shirin yi ne Afnan? Me nake shirin aikatawa? Ya illahi! Am totally out of my control. Wallahi jina nake yi yau tamkar
an kawo min ke ne a matsayin matata. Please Habibaty am so sorry, ki yi hakuri wlh shaiɗan ne ya ruɗeni kin san na daina ko riƙa hannunki ko? Please Afnan"Yanda ya yi maganar tamkar zai yi kuka, sosai ya ruɗe ganin yanda ta ɓata ranta.
Abunka da so, nan take tausayinsa ya kamata har bata san lokacin da ta yi murumushi ba, tare da harararsa.
"Toh na ji amma kar ka sake yi min
irin haka dan Allah""Insha Allahu ba zan sake ba sweetheart" ya faɗa yana sosa
ƙeya. "But Please ki yi min alfarma in riƙa hannunki in kaiki ki zauna" ya faɗa cikin sigar zolaya, harda kanne mata ido,Dariya ta yi tare da wucewa tana harararsa. "Idan zaka zo ka
zauna ka zo, idan kuma ba za ka zo ba ga hanya nan Allah ya raka taki gona"Dariya ya yi. Ya zo ya zauna kusa da ita yana kallonta "Wai kin ganki kuwa? Allah tamkar wata amarya"
"Uhhm! Allah ko?" Ta faɗa cikin jin kunyar kallon da yake yi mata
Gyada Mata Kai ya yi. "Sosai kuwa my Afnan"
Agogon hannunta ta duba. "kaga ma lokaci na wucewa, gashi ba ka ci komai ba" ta faɗa tare da miƙewa ta fara zuba masa abincin da aka girka dominsa.
Bai wani cin abincin da yawa ba saboda baya jin yunwa. Ya dai ci ne kawai saboda idan ya ce ba zai ci ba rigima kawai za su yi da ita.
Bayan ya kammala ne suka shiga yin fira tamkar ba za su rabu ba.
Ba shi ya bar gidan ba sai kusan ƙarfe goma da rabi na dare, shima ba
don ya so ba ,sai dai don ba yanda zai yi ne. Saboda abunda yake ji game da Afnan a daren wani abu ne mai girman gaske...........?Yau tsawon sati biyu kenan da faruwar wannan. Amma ba Yazid ba samatarsa. Hankalin Afnan ya yi matuƙar tashi gashi ko ta Kira wayarsa bata zuwa.
Kwance take kan gado idanuwanta na kallon sama, hawaye ne ke ta sintiri a fuskarta. Tunani da yawa a zuciyarta 'to me ya same Yazid ne? Ko kuwa dama tun can bayada ra'ayin aurena ne? Kai wannan ba zai ma yiyu ba. Yazid yana sona, na san ba zai min haka ba'
Wata zuciya ta ce, ki ka sani ko matsala ya samu daga wurin iyayensa?'
Wata zuciyar kuwa cewa ta yi,
'Ƙila kuwa wani Abu ne ya sameshi. Kai kilama mutuwa ya yi baki sani ba'Ai kuwa tamkar wani ne ya gayamata, ta shiga rera kuka tamkar ranta zai fita.
Wayarta ce ta yi ringing. Da sauri ta miƙa hannu ta dauko tana addu'ar Allah yasa Yazid dinta ne.
Sai dai kash! Ba Yazid idanuwanta suka gani ba
sunana mahaifinta ta gani.Nan take hankalinta ya sake matukar tashi saboda tana da yaƙinin wannan kiran ba na lafiya ne ba.
Cikin muryarta da ta dusashe ta dauki wayar.
Sallama kawai Abban nata ya karba tare da cewa, "Kizo Ina neman ki yanzunnan" bai tsaya ya ji Mai za ta ce ba kawai ya kashe wayar.
![](https://img.wattpad.com/cover/95453973-288-k589738.jpg)