Yazeed ko Yaseer
Ayshart Farouq
6
Sosai Afnan ta kagu Abba ya sallameta
ta je ta fadawa Yazid ɗinta wannan good news ɗin ta san zai fi kowa farin ciki idan ya ji sa.Kaman Abba yashiga ranta. Ya dubeta. "To uwata aje a gayawa surikin nawa ko?"
Kunya ce takama ta ta ce cikin in-inniya.
"uhm ni fa Abba na fasa a bari kawai sa na kammala"Ibrahim dake zaune ya galla Mata harara "Ka ji min algunguman yarinya. Haka zaki ce ai yanzu. Ƙaryar da kike yiwa Mommy kina satar hanya kuna haɗuwa ce ƙila ba ki gaji da ita ba right?"
'Ya subhanallah! Wai me suke nufi ne Ba dai duk abinda take yi suna hankalce da ita ba' ta faɗa a zuciya tare da sanya kukan shagwaba "Abba ka ganshi ko?"
"Kyaleshi uwata shima na bashi nan da sati biyu ya fadi yarinyar da yake so aje ayi mishi tambaya"
Rabon idanuwa ya yi yana sosa ƙeya, "uuhm dama wlh Abba Ina so mu yi magana da kai kan wata yarinya amma ban San ta inda zan fara ba ne."
Dariya ya basu dukan su saboda yanda ya yi maganar kamar wanda ke jiraye.
Cikin dariya Mommy ta ce. "Ai yanzu kanwarku ta buda maku ta inda zaku fara, don ga dukkan alamu ko Sagir can aka yi"
Sagir ya ce, "Tab Mommy rufa min asiri ni ai har yanzu yaro ne. Ga dai su big bros nan masu
Shema'u da Hauwa'u" Ya faɗa yana ƙunshe dariyarsa.Harara Ibrahim ya watsa mishi. "Kaga gadon baccina ko Sagir?"
"Afuwan likita" ya ce yana ci gaba da dariyarsa.
Murmushi kawai Daddy ya yi tare da kallon Ibrahim ya ce. "kasameni anjima muyi maganar idan da gaske kake yi." Ya fada tare da miƙewa ya shige warsa ɗakinsa.
Momy ma mikewa ta yi ta bi bayansa tana masa magana.
Afnan kam kasa mikewa ta yi don gudun tsokanar Sagir, saboda ta san tana mikewa zai hauta da tsoknar da ya saba.
Kallonta Ibrahim ya yi tare da harararta. "To ai sai ki tashi ko! kin wani saka mu gaba kina muna kinibibi"
Zunburo baki ta yi tare da mikewa. Dama abunda take so kenan,
Dariya suka hauta da ita don sun riga sun gano kunya take ji.
Bata kulasu ba dai ta wuce abunta tana murna.Tana shiga ɗaki kan gado kawai ta fada tare da kiran number Yazid.
Bugu daya ya dauka tamkar dama jiraye yake da kiran nata."Albishirinka habibina" yanda ta yi maganar saida ya lumshe idonsa saboda dadin muryarta da ya ratsa shi.
A kasalance ya ce. "Goro. Amma Allah yasa bani ke akayi?"
Dariya ta yi, "kai wani lokaci haka kake tamkar aljani."
Mikewa ya yi daga kwancen da yake don jin me zata fada
"Ina jinki plz na kagara in ji fa sweetheart"Dariya ta yi kafin ta kwashe duk yanda suka yi da Abbanta ta gaya mishi.
Yanda ya ji maganar yana tunanin a duniya ba wanda yakaishi jin dadi.
"Afnan da gaske kike yi
kuwa ko tsokana na kikeyi" ya fada cikin tsantsar
farin ciki."Allah dagaske nake yi Yazid Abba ya ce ka turo magabatan ka"
"Alhamdulillahi Afnan na yi farin cikin jin wannan maganar taki sosai. Insha allahu nan da 1 week zasu Amman kafin nan yau ina so zan zo zance gidanku, nasan dai ba wata matsala ko?" Ya fada tamkar ya yi tsale ya gansa wurinta.
"Zan sanarda Abba duk yanda yace sai in sanar da kai, duk da bana tunanin zai hana, amma sanar da shi yanada amfani."
"Toh ba damuwa sai naji ki".
Haka dai suka yita waya suna jin su tamkar sunfi kowa farin ciki a fadin duniyar nan.
Bama kaman Yazid da yake ganin ya kusa cimma burin shi kan Afnan don yana ganin wannan hanyar ce kadai zai samu abinda yake nema a gurinta.
![](https://img.wattpad.com/cover/95453973-288-k589738.jpg)