Yazeed ko Yazeed
Ayshart Farouq
Nagarta writes association
2
Aisha Afnan 'ya ce gun Alh Umar Adam, Wanda
ainihin shi mutumin kano ne, yana da ɗiya uku
Ibrahim, Sagir sai Aisha Afnan.
Matar shi daya
wato Hjy Zainab.
Akwai tazarar haihuwa sosai tsakanin yaransu. Haka kuma tun bayan haihuwar Afnan basu sake
samun haihuwa ba. Shiyasa suka dauke son
duniya suka daura Mata matsayinta na auta kuma ɗiya macce.
Tun Afnan tana karama burin mahaifinta ta zamo
lawyer, shi yasa kwata kwata bata kula samari. har Afnan ta kammala secondary school batada wani
saurayi ko wani Wanda take so. Ba kuma don babu masoyan ba sai dai don wannan ne ra'ayinta da na mahaifinta, kuma sosai take girmama hakan a gareta.Ibrahim kuma ya ƙare karatun shi na medicine a jami'ar england. Yayin da sagir yake karatun business admin a malesia. Afnan kuma yanzu take UG2 a jami'ar bayaro da ke jahar kano tana karatun law.
Tunda ta ke karatunta Kawai ta sama gaba, sam bata damu da harakar kowa ba sai ta karatunta. Tun lokacin da Ya kyalla ido ya ganta
yake bibiyar ta amma Ina. ya yi duk yanda zai yi don ya ga ko kallonsa ta yi ta kyasa amma ya kasa, saboda ita
ba irin matan nan ne ba da suke shiga harakar da tasu ba. Haka kuma ba irin matan da zaka samu ba ne a lokaci ɗaya ba ka sanar da su da bukatar ka ba.Wata Rana ta fita shopping tare da driver sai
motarsu ta samu matsala ta tsaya musu kan hanya, ganin lokaci zai kuremata kafin a gyara
ya sanya ta yanke shawarar shiga adai daita. Bayan ta shiga shoprite din ne, ta fara diban kayan
da take so. Ta kai hannunta gurin wani turare kenan sai aka dauka. Da sauri ta juya don ganin ko waye. Lokaci ɗaya idanuwanta suka shiga cikin nasa. Nan take ta sauke kwayar
idanuwanta kasa saboda kwarjinin da yayi mata da kuma tsabar
haduwarsa.
murmushi yayi mata tare da cewa,
"Wannan turaren nawa ne nariga ki ganinsa ki zabi wani" ganin bara ce komai ba ya sake cewa
"ko in zabar miki ne? don Sam wannan bai dace da kyakkyawar halitta irin taki ba"
Karo na farko a rayuwarta da ta ji wani ɗa namiji ya burgeta.
Ji tayi sam ba zata iya yi masa musu ba.
Samun kanta tayi da gyada masa kai. Murmushi ya sake sakar mata kafin ya ɗauko wani colour.
"Wannan shi yafi dacewa da ke" ya miƙa mata yana sake kasheta da murmushinsa.karɓa ta yi tare da yi mishi godiya ta wuce abunta tana ci gaba da dibar abunda take so.
saida ta kammala kaf sannan ta je gurin biyan kuddin.
ATM card dinta ta cire ta miƙa don cire iya adadin kuɗin kayanta. Ba zato ta ji ance ai an riga da an biya Mata. Sosai mamaki ya kamata ganin kusan
kayan 40k ta saya. "Waye ya biya min?"
Ta tambaya. Nuna mata shi aka yi yana tsaye yana danna wayarsa.Ɗaure fuska ta yi tare da isa kusa da shi.
Cikin isgilanci ta ce. "Malam mi ye na biya min kuɗi alhalin ba roƙon ka na yi ba?"Murmushi yayi tare da cewa,
"Afnan kenan"Zare idanuwa ta yi tana kallon sa jin ya ambaci sunanta.
"Kar ki damu na san baki san ni ba amma ni na san ki.
Wani kallo ta masa na rashin yarda.
Mika hannunsa ya yi
"Kawo kayan in riƙa ma ki. Ba nan ya dace muyi magana ba kinga mutane suna wucewa a gurin"
Yanda yayi maganar sai taji ya burgeta saboda da alama ya san mutuncin kansa da kuma darajar ɗiya
macce.
Samun kanta ta yi da sake mishi kayan, tare da bin bayanshi har bakin motarsa.
Sanya kayan yayi a mota tare da cewa, "oya shiga mu je"Girgiza kanta ta yi. "A'a ba zan shiga motarka ba ba tare da na sanka ba. Hasali ma tare nake da driver"
Murmushi ya yi mata.
"Kar ki damu mintuna biyar sunyi yawa da zaki sanni. Mota kuwa har yanzun Malam Sani bai gyra ba" ya faɗa yana kallonta.'Anya kuwa wannan mutum ba aljani ne ba! Ta faɗa cikin ranta.
Kamar ya san abunda ta ke tunani ya ce. "Ba fa aljani nake ba Afnan ki shiga dan Allah mu tafi" ya ce idanuwansa na nuna alamar rok'o.
Ganin ba sarki sai Allah ne ya sanya ta Afnan ta shiga motar tasa tare da jero masa tambayoyi "Kai
waye? Kuma a Ina kasanni?"Murmushi ya yi. "Sunana Yazeed kuma na sanki da jimawa ya bata amesa ba tare da ya kalleta ba.
"So why did u do all this to me?" Ta sake tambayar shi.
Kai tsaye yabata amsa da "Saboda Ina kaunar ki. Am in love with u Afnan. Soyayyar ki ta Daɗe cikin raina ban
San ta yanda Zan gaya maki ba ne saboda naga ba ki damu da kowa ba"Ya nisa tare da kallonta ta gefen idanunsa ganin yanda tayi tamkar wadda ruwa sunka ci.
ci gaba yayi da magana.
"Kamar yanda na gaya ma ki sunana Yazeed Ahmad Abdulrahman. Amma mutane ko in ce abokanina suna kirana da Ahmad Y Abdulrahman. Na kammala masters d'ina a Singapore watannin da suka wuce.
Na kuma san ki ne a BUK ta sanadiyar ziyarar da na ke kaiwa wani abokina da ke masters nan faculty ɗin da ki ke. Hope bayanina ya gamsar da ke?"Ita dai Afnan kasa cewa komai ta yi saboda mamakin shi da ya kama ta.
Har bakin motarsu ya kawota dan ya ƙara kwantar mata da hankali. Ya kuma nuna mata tabbas ya santan.
Daƙyar ya samu ya karɓe numberta da sharaɗin ba zai dameta ba.
Sannu sannu suka fara waya har ya kai sun fara haɗuwa a school tun dai Afnan tana ɗari ɗari da shi har ta
daina. Ta saki jikinta da shi. Nan ta ke soyayya mai tsanani ta shiga tsakanin su.
Lokacin ne kuma ta fayyace mai ra'ayin mahaifinta akan ta.
Inda Shima aka yi sa'a iyayen shi sunada wannan
ra'ayin na ganin sai yaro ya gina kansa kafin yayi aure. Wannan ne yasa ba wanda ya kai maganar gurin magabatansa. Sanin su dai suna kaunar junansu kuma duk wuya duk rintsi suna tare da juna.............Back to labari.
Next chapterAyshart one
