Babi na sha takwas

553 38 0
                                        

Bugu ɗaya yi mata ta dauka.
Cikin ladabi da biyayya yake magana hadi da yi mata magiya.
"Dan Allah Ammi ki yi haƙuri ki zo ki kwana da yarinyar nan wlh bamu san ya zamu yi da ita ba tunda mu ba muharamanta ba ne ballantana wani ya kwanta da ita.

Ammie kin san ke kika tursasani kan na tsaya na taimaketa, me yasa ba zaki zo kema ki taimaka ba?

OK Ammi mungode sosai, yanzu zan miki text din room number din, tau  sai kin zo" ya faɗa tare da kashe wayar.
Bai sake kallon inda  yaseer  yake ba kuma bai ce masa komai ba.
shima Yaseer ɗin bai ce komai ba saboda ya riga yaji abunda aka faɗa.
      
 
Sai kusan ƙarfe tara da rabi mahaifiyar yazeed ɗin ta shigo ɗakin dauke da food warmers da flaks din ruwan zafi.
cikin ladabi yazeed da yaseer  suka gaidata, ta amsa musu ba yabo ba fallasa.
Yaseer ne ya karɓi kayan hannunta ya dora kan bedside drawer, yayin da ita kuma ta zauna kan gadon da Afnan ta ke tana kallon fuskarta, tare da cewa.
"Ikon Allah yarinya kyakkyawa an ɓata mata rayuwa"

Taɓe baki Yazeed ya yi tare da cewa. "Ko dai ta ɓatawa kanta ba"

"Ai duk ɗan Adam ba ya wuce kaddararsa"
yaseer ya faɗa yana kallon fuskar Afnan da ta ke ta sharar bacci abunta.

"Hakane kam, bawa bai isa ya wuce ƙaddararsa ba sai dai muce Allah ya kawo mana kaddara mai kyau" cewar Ammi.

Shiru  ne ya ratsa na 'yan wasu daƙiƙu kafin Ammi ta soma magana.

"Da ban yi niyar yin magana ba amma yanzu ganin wannan yarinyar yasa nake son in yi.  Babban bunda nake gargadinku da shi dukkanku shine ku ji tsoron Allah  idan  akwai wanda ya yi ma wannan boyar Allah fin karfi da ya faɗi.  Saboda ga alama tabbas cikinku dole ne akwai wanda ya aikata"

Baki dayan su kallon junan su suka yi kowa da abunda yake sakawa a ransa.

Ci gaba da magana Ammie ta yi "Dukan ku nan maza ne, kuma kuna da kanne kuna da iyaye. Wallahi summa tallahi duk abunda ka yi wa ɗiyar wani, kanwar wani, matar wani,  kaima sai an yi ma taka.
Da wannan nake gargadin ku da ku ji tsoron mahaliccinku  ku tausayawa wannan boyar Allah ku faɗi gskiyar lamarin  ko Allah nasa ta sasanta da iyayenta. I will ask you for d first and last time. Dan Allah  wa ye ya yiwa wannan yarinya ciki a cikin ku?" Ammie ta faɗa tana mai kafesu da idanuwa.

Kallo ɗaya zaka yi wa yazeed da yaseer ka tabbatar da suna cikin ruɗani. Sosai  hankalinsu ya yi matukar tashi. Magangannun Ammi sun ratsa su ta ko ina.

"Ku nake saurare" Ammie ta katse musu tunanin da suke yi.

Cikin azama Yazeed ya fara magana da dakakkiyar muryarnan tasa.
"Wallahi  Ammie  kamar yanda na gaya maki wallahi ban taɓa ganin yarinyar nan ba sai yau, don haka wallahi  banida masaniya kan abunda take zargina da shi" ya faɗa a karo na farko da fuskarsa ta nuna raunin da ke tare da shi.
Sai da Ammie ta kafesa da idanuwa na tsawon lokaci kafin ta juya ga Yaseer.

"Kai fah yaseer?" Ta tambaya tana kafesa shima da idanuwanta.

Natsuwar shi ya tattaro duka batare da ya daina kallon innocent face ɗin Afnan ba ya ce.
"Wallahi Ammie bani na yi ba, nima ban taɓa ganinta ba sai yau"
  
    Murmushi Ammie ta yi tare da furzar da wani iska mai zafin gaske. Ita kaɗai ta san abunda take ji game da yarinyar nan ba don komai ba sai don kasancewar ta DIYA MACE kamarta.

Ba tare da ta sake kallon su ba ta ce "Allah ya bi maki hakkinki ga duk wanda ya aikata miki wannan abun" ta fada tare da dan shafe kwallar da ta tarar mata cikin idanu.

Haka suka zauna har karfe 10 sannan suka yi ma Ammie sallama suka wuce zuciyarsu duka ba dadi kowa da abunda ke damunsa cikin ransa.

Waye yazeed da yaseer,

Yazeed ko YaseerDes histoires addictives. Découvrez maintenant