Babi na arba'in da shidda

759 61 24
                                    

Kwance tashi asarar mai rai su Yazeed har sun kammala seminarsu.

Ranar  Friday misalin ƙarfe bakwai na dare jirginsu ya iso Nigeria.
Tun da suka sauka ya ɗauki drop ɗin mota sai gidan Ammie kasancewar wannan na ɗaya daga cikin ɗabi'arsa.

Duk lokacin da ya yi tafiya ya dawo sai ya fara zuwa gurin Ammie kafin ya je ko ina. shi yasa yake yawan barin motarshi a gidan idan zai yi tafiya.

Koda ya shiga ɗakin Ammie ta sallame sallar isha'i kenan tana lazimie.

Zama ya yi bakin gadonta ya ɗan kishingiɗa saboda gajiyar da yake jin tana taso masa.

  "Maraba da mutanen Germany. Saukar yaushe dawowa haka babu notice?" Ta faɗa lokacin da ta kammala tana kallonsa.

Murmushi ya yi tare da gaidata.
"Wallahi Ammie ƙasar ce sai a slow. Na yi kewar gida sosai shi yasa muna ƙarewa ban tsaya komai ba na biyo jirgi na dawo"

"Masha Allahu Allah yasa an yi cikin  sa'a. Babu wani abu da aka tanadar maka nan tunda ba mu san da dawowar ka ba amma nasan can gidan su ba zasu rasa sani ba ƙila an tanadar ma da wani abu sai kasa himma kar su yi ta jira" ta faɗa ba tare da ta kallesa ba, ta cigaba da yin laziminta.

Jikinsa ya ji duk ya yi sanyi ganin irin kallon da Ammie ke yi masa da yanda take masa magana tamkar ba ita ba.

Bai samu damar cewa komai ba ya ɗan kishingida har tsawon mintuna talatin sannan ya miƙe.

"Zan wuce sai zuwa gobe insha Allahu"
Ya faɗa tare da juyawa ya tafi.

"Yazeed!" Ammie ta kira shi cikin ɗacin murya.

"Na'am Ammie" ya amsa tare da juyowa ya kalleta cikin wani ruɗaɗen yanayi.

"Ina so gobe idan za ka dawo ka dawo min da takardar sakin Afnan, na janye buƙatata ta son sanin abunda ya haɗa ka da ita.

Ni dai wallahi nagaji da ganin yarinyar mutane cikin ƙunci, da rashin sanin makomarta a nan gidan. Ka kawo mata takardarta kawai ta koma gidansu Allah ya haɗa kowa da rabonsa.

Amma  ba baki na yi ma ba wallahi muddun ka rabu da Afnan sai ka yi nadamar da baka taɓa yin irinta cikin duniyarka ba.

Ba zaka taɓa gane me nake so ka gane ba sai lokacin da ka ɗora alƙalaminka a kan takarda, ko ka furta mata mafi munin kalma da miji zai gayawa matarsa.
Nabeela kuma da ake nema a kakkaɓa ma ka je ga tanan ga ka"
Tana kaiwa nan ta miƙe tare da lunke dardumarta ta shiga bathroom ta barsa tsaye kamar iccin durumi.

Zufa ne keta karyo mishi ta ko ina cikin jikinsa. Gajiyar da ya kwaso tuni ta sake koma mishi sabuwa.

Kalamanta yake jin na yi masa yawo ta ko ina a cikin jikinsa.
Dakyar ya iya ɗaga ƙafafuwansa ya wuce yana tunanin magangannun Ammie. Ya rasa gane abunda yake ji na sukarsa game da kalaman nata.

Yana cikin saukowa kan step ne ya ji ya yi karo da mutum.

Idanuwansa da suka chanja kala ya watsa ma Afnan dake ƙoƙarin shiga gurin ammie dan samo maganin ciyon kai.

Baya ta yi cikin kaɗuwa za ta faɗi saboda tsoratar da ta yi.
cikin zafin nama ya yi saurin riƙota har sai da ta buge  kirjinsa saboda rashin ƙarfin da ke tattare da ita.

Wani abu ya ji ya tsargar mishi  tun daga kanshi har zuwa yatsarsa. Hannu ya sa ya yi saurin tureta daga jikinsa yana mai watsa mata wani irin kallon mai matuƙar tsoratar da halittarta da daƙushe ƙarfin guiwarta a garesa.

Allah ya taimaketa ta yi saurin dafe ƙarfe da tuni ta yi ƙasa.

Bai sake kallon inda take ba ya raɓa ta gefenta da niyar ya wuce.

Cikin sauri ta riƙo hannunshi.
"Ya Yazeed". Ta faɗa cikin wahaltacciyar muryarta.

Janye hannunshi ya yi yana mai jin wani yanayi na daban a tattare da shi.

Idan ya tsaya komai zai iya faruwa ga zuciyarsa shi yasa ya ƙyaleta kawai  ya ci gaba da tafiyarsa.

"Dan girman Allah ka saurareni ba dan halina ba"

Cak ƙafafuwansa suka tsaya ba tare da ya basu umurnin yin hakan ba.

Juya mata baya ya yi zuciyarshi na bugawa da tsananin sonta da ƙaunarta da ke bijiro masa a cikin ko wace daƙiƙa da zai kasance tare da ita.

A hankali ta matso kusa da shi.
"Ya Yazeed na roƙeƙa da girman Allah da ka yi haƙuri ka yafe min laifin da na yi maka.

zuciyata ba za ta iya cigaba da jurar wannan hukunci naka a gareta ba. Dan Allah ka daure ko yaya ne ka fitar dani daga cikin duhun da nake ciki ka sanar dani abunda na yi maka.

Zan iya jurar ko wane irin hukunci daga gareka koda kuwa hukuncin rabuwa dani ne, Amma ba zan iya jurar hukkuncin wannan kallon tsanar da tuhuma da kake yi a gareni ba"

Wani murmushi Ya saki wanda ƙara ciyon kuka da ciyonsa.
"Kukanki da mayaudaran kalamanki sun daina tasiri a gareni.
Ki sani ba ki ma fara kuka ba sai lokacin da zan bayyana mugun halinki da kuma baƙaƙeb  ayukanki a idanuwan duniya, saboda kin ci Amanar Allah, kin ci amanar iyayenki, kin ci Amanar mijinki da duk wani wanda ya yarda dake.

Ina mai tabbatar miki da cewa kin kusa zama abun kwatance a cikin mutane.

Haƙiƙa  hankalina ba zai taɓa kwanciya ba har sai ranar da na ganki dake da wannan mutumin da kika baiwa damar saɓawa mahaliccinku  kun wulaƙanta a idon duniya ba"

Yana kaiwa nan ya juya ya ci gaba da tafiyarshi zuciyarshi na matukar yi mishi ƙuna ganin abubuwan da ta yi na dawo masa ɗaya bayan daya a ƙwaƙwalwarsa.

Kasa ƙwakkwaran motsi Afnan ta yi sai hawayen da ke zubar mata masu tsananin zafi.

Dakyar ta iya juyawa ta koma ɗakinta saboda yanda take jin kanta na bala'in sara mata.
kafin ka ce me har zazzaɓi mai tsananin ya rufeta sai kakkarwar sanyi take yi.

Shi kuwa Yazeed sai da ya bari ya dai daita kanshi tare da samar ma kansa nutsuwa ƙalilan sannan ya iya jan motarshi ya wuce.

Bayan ya yi parking  cikin gidan ya fito ne, ya hange motar mahaifinsa da shima shigowarsa kenan. Tsayawa ya yi har ya fito daga motar sannan ya isa gurinshi dan su gaisa.

Bayan sun gaisa Daddy yake tambayarshi da cewa.
"Saukar yaushe kai baka sanar da mutane zaka dawo ba. Ko shekaranjiya na yi waya da kai amma baka gaya min zaka dawo yau ba lafiya dai ko?"

"Lafiya lau Daddy. Ai banma daɗe da isowa ba na ɗan tsaya gurisu Ammie ne"

"Masha Allahu to ya gurinsu Aminar da fatar duk suna lafiya"

"Lafiya lau suke"

Ƙare masa kallo daddy ya yi kasancewar haske ne a gidan kamar safiya.
"Lafiyarka kuwa naga duk ka wani ƙanjamewa haka da kai ka yi wani zuru zuru?  hope dai ba Auren Nabeela ne ke damunka haka ba"

Murmushin yaƙe Yazeed ya yi tare da gyaɗa kai "gajiya ce kawai dad" ya faɗa yana mamakin kulawar da yake samu kwanan nan daga mahaifinsa.

"Ya kamata ka je ka gaida Mamienku kafin ka shiga gida dan nasan ƙila ba zaka sake samun damar fitowa ba idan ka shige sai gobe dan naga alamar gajiyar nan ta yi maka yawa. Gashi ita kuma gobe na ji ta ce za su je biki Abuja ita da Aina'u ina ga kuma kamar sammako za su yi. Dan haka ka shiga ku gaisa yanzu.

Yazeed bai yi gardama ba duk da ba haka ya so ba. Bayan mahaifinshi ya bi suna tafiya suna taɓa 'yar firar da ta shafe seminar da ya je.

Sun taka step ɗin da zai sada su da falon Mamie kenan suka ji wani  faɗuwar gaba ya riske su dukansu.

Ba wanda ya sake  magana cikin su har suka isa bakin ƙofar falon.
Har Daddy ya kama handle ɗin ƙofar da niyar boɗewa ya fasa sakamakon  maganar da ya ji.

Sakin ƙofar  ya yi da sauri tare da kallon Yazeed cikin tsananin tashin hankali.

Vote
Comment and
Share

Yazeed ko YaseerDonde viven las historias. Descúbrelo ahora