Babi na arba'in da biyu

536 42 6
                                    

Ganin text ɗin ba guda ba sun fi goma yasa ya bi conversation ɗin nasu da kallo yana karantawa.

Wasu hawaye ne masu matuƙar zafi da ƙona zuciya ke zubo masa a idanu ganin irin saƙonnin da suke turama junansu.

Wani saƙo ne ya ja hankalinsa.
"Sweetheart ki sani duk lokacin da kika bari mijinki ya kusance ki ranar mutuwa zan yi Afnan. Kin san yanda ƙaunarki da kishinki ke gudana a cikin jini da gangar jikina. Kin san ke ta daban ce shi yasa na kasa haƙura dake har na lashi zumar ki kafin in bar ƙasar nan. Ki sani na yi baƙin cikin abunda ya faru da ke lokacin da bana nan a tare dake. Gashi har da rabon gudan jininmu da  ya zube duk saboda ni.

Nasan irin ɗinbir ƙaunar da kike min ne yasa kika rainawa mutanen can hakali kika ce fyaɗe aka yi miki. Ina ƙara godiya sosai a gare ki da kika tafiyar da plan ɗinmu yanda ya kamata ba tare da kowa ya fahimta ba. Ki dubi hanyata cikin kwanan nan komai zai kammala zan dawo gare ki insha allahu habbibty.
Your Yazeed.

Ita kuma sai ta tura masa wannan.
"Kaima  ka san ba don ina son Yazeed na aure sa ba. Kai kan ka, ka san rashinka ne, da kuma tsoron irin mutumin da  Abbana zai haɗani da shi yasa na amince zan aure sa.  Shima kuma  dan kawai ya ci albarkacin sunanka ne da naci irin na mahaifiyarshi.

Amma nayi maka alƙawarin ba zan taɓa bari wani abu ya shiga tsakanina dashi na mu'amular aure ba.
Sannan na yi  maka  alƙawarin zan kashe aurena da shi nan bada daɗewa ba domin in mallaka maka kaina kai kaɗi saboda kaine zaɓina.

Duk lokacin da na tuna ranar da muka kasance tare da juna  nakan yi farin ciki marar misiltuwa. Dan haka a shirya nake daga yanzu zuwa ko wani lokaci zaka dawo dan ka ɗebe min ƙishin da ke damuna.
Yours Afnan.

Massege din karshe da ya turo ce mata ya yi.
"Na yi ta kiran ki baki ɗaga ba ko kina tare da mijinki ne? Ki tabbatar da cikin satin nan  duk yanda za a yi mu haɗu saboda ina son jin dumin jikinki. Na yi kewar ki da yawa Afnan. Gashi na dawo kin ƙi bani damar ganinki har yanzu. Pls ki ƙoƙarta ki samu dama kafin raina ya fita daga gangar jikina saboda rashinki a tare da ni. Ina tsananin  missing lips dinki masu taushi da zaƙi idan zaki zo ki saka min pink lipstic.
Sannan kuma na zo mana da wata hanya mafi sauƙin da zaki kashe aurenki ba tare da mahaifiyar mijinki ko  mahaifinki sun  zargeki ba.

Yazeed Mahmud .

Buɗe kofar bathroom ɗin da aka yi ne, Ya sanya Yazeed ya miƙe tsaye cikin wani irin yanayi mai wuyar Fassarawa yana dafe dukkanin ƙirjinsa.

Wani mugun kallo ya shiga jifan ta da shi tare da tunkararta ba tare da ya saki zuciyarshi ba.  Wani irin huci yake yi mai nuna ruruwar wuta a ƙasan zuciyarsa.

Sosai hankalin Afnan ya yi matuƙar tashi ganin wutar dake cikin idanuwansa. Neman ɓacin ran da Nabeela ta haddasa mata ta yi ta rasa saboda bala'in da take gani a gabnta.
"Yaa Yazeed.........."

Bata ƙarasa ba ta ji saukar wani irin gigitaccen marin da bata san lokacin da ta kai ƙasa ba. Wata irin wahaltatta ƙara ta saki  saboda azaba.

Idanuwansa rufe ya shiga shuri da ita hawaye na zuba a idanuwansa.

"Kin cuce ni Afnan,  kin cuce ni, kin cuci ƙauna da soyayyar da na nuna miki. Na tsaneki  na tsaneki ki......."

Ya ji wani abu mai tsananin nauyi ya tokare mishi zuciya. Harshensa tuni ya kare.  jikinsa kuwa nan taki ya saki baki ɗaya. Ya faɗi ƙasa ba bu alamar nunfashi a tare da shi.

Yanayin zafin zazzaɓin da ya taso mata da na wahalar da ta sha bai hana mata sakin wata razanannar ƙara mai tafiya da sunanasa a maƙoshinta ba.

Jin haka yasa Nabeela ta shigo da gudu tana salati. Ganin ba alamar nunfashi a tare da shi yasa, ta fita da gudu tamkar mahaukaciya ta yi sashen Mamie tana kiranta.

Cikin ƙanƙanen lokaci suka tallabesa tare da Yaseer suka fita da shi cikin tsananin tsoron da ya mamaye zuciyoyinsu dukan su.

Sai bayan an shiga da shi emergency ne, sannan Afnan ta yi ƙarfin halin kiran Ammie da karamar wayarta da ba ta san ta yanda  aka yi  ta daukota ba.

Cikin ƙanƙanen lokaci su Ammie suka iso assibitin. Afnan na ganinta ta faɗa jikinta tana wani irin kuka mai bata wahala a zuciya.

cikin kalamia masu daɗi Ammie ta shiga lallashinta tana kwantar mata da hankali.

Sai da likitoci suka shafe hour ɗaya kan Yazeed sannan suka samu nunfashinsa ya dawo. Allurar bacci aka yi mishi mai ƙarfi don ya samu nutsuwa.

Suna fitowa su Ammie sukayi saurin miƙewa suna tambayarsu halin da Yazeed ɗin yake ciki,

Duban su likitan ya yi yana shafe zufa tare da cewa.
"Ku kwantar da hankalinku he's out of danger now. Sai dai yanzu mun yi mishi allurar bacci sabida yan buƙatar hutu sosai da nutsuwar ƙwaƙwalwa, saboda shock ɗin da ya shiga saura kiris jininsa ya wuce yanda zamu iya controlling ɗinsa. Amma yanzu alhamdulillahi komai ya zo da sauƙi, dan haka idan ya farka zuwa anjima ma za a iya sallamarshi idan anga ba wata matsala"

Hamdala suka yi dukan su tare da yima likitan godiya.

Sosai Yaseer ya so ace zuciyar Yazeed  ta buga saboda ya ɗanɗana makamanciyar azabar da ya danɗana lokacin da ya raba shi da Afnan.
wani murmushin samun nasara ya yi saboda ya san yana daf da cika burinsa.

Ammie ce ta katse mishi tunaninsa da cewa. "Ai kuwa Yaseer da kun wuce gida tun da abun ya zo da sauƙi, idan ya so ni da Afnan sai mu jira har zuwa lokacin da zai tashi."
Ta  faɗi haka ne saboda tana so ta keɓe da Afnan don jin abunda ya faru da Yazeed ɗin saboda har yanzu bata tambayeta abunda ya faru da shi ba har ya faɗi.

Sosa ƙeya Yaseer ya yi saboda ba zai iya wucewa ba har sai yaji hukuncin da Yazeed  ɗin zai yankewa Afnan.

"Ba komai Ammie za mu jira muma har zuwa lokacin da zai tashi"

Cikin sauri Mamie ta ce. "Da dai mun wuce zuwa anjima sai mu dawo, ka san halin yan Asibitin nan basa son ana zama haka da yawa yanzu nan sai su yiwa mutane rashin mutunci su ce ab cika masu wuri."

Nabeela ta yi saurin cewa. "Ni kam Mamie ba in da zanje sai Yaa Yazeed ya tashi."

Murmushi Mamie ta yi saboda dama haka take so. Ta fi son duk hukuncin da Yazeed zai yanke ya zamana wani daga cikinsu yana kusa. Ita kanta da ba don ganin kallon da Ammie ke yi mata mai tattare da zargi da rashin yarda ba da ba zata wuce ba.
Amma da yake ta san halin Ammie da sun bari sun zauna sai ta yi suspecting wani abu a tare da su.

Kallon Nabeela ta yi cikin kissa. "Ai dama ba tare da ke za mu je ba. Dan na san bama zuwa za ki yi ba kin ga yayanki cikin wannan halin. Ki zauna kawai har lokacin da zai tashi ko hankalinki zai kwanta"
Ta ƙarashe maganarta tana  kallon Ammie da Afnan.

Taɓe baki Ammie ta yi saboda ta riga ta san shu'umanci da makirci irin na Mamie. Sannan ta tabbatar da ko me ne ne akwai hannunta ciki ganin yanda fuskarta ta kasa ɓoye farincikinta.

Yazeed ko YaseerTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang