Babi na goma

705 46 1
                                    

          
Sai da ya samu biyan bukatar kansa sannan ya saurara mata.
Banda kuka ba abunda Afnan din ke yi saboda ba karamar wahala tasha hannunsa ba.

Gogan kuwa kwance ya yi reran yana maida nunfashi sabida wata kasala da ta rufesa.

Ganin kukan nata ba mai karewa ba ne ya sanya ya dan janyota  jikinshi da niyar ya lallasheta.

Turesa ta yi jikinta tana mai jin wata irin tsanarsa mai girma a cikin zuciyarta.

"Plz Afnan Dan Allah ki yi hakuri ki yafe min wlh bada son raina na yi maki haka ba,  i don't have any other option ne, shi yasa na aikata haka agare ki.
Wallahi Afnan ina cikin tsananin bukata ne wadda idan ban kasance da mace ba zan iya rasa rayuwata, that is why naga ke kadai ya dace ki taimaka min keda zan aura.  To believe me or not Afnan wlh ban taba aikata zina ba. Wannan ma tsautsayi ne dan Allah ki yafe min"
ya karashe maganarsa cikin kuka,

Sosai Afnan ta kara harzuka saboda ganin yanda yake so ya raina mata wayo, duk da ta tabbatar da bata da wayon. Amma wannan ai rainin hankali ne yake yi mata.

Wani kallo ta watsa masa mai tattare da ma'anoni masu yawa.
Murayarta a shake take magana.

"Mahaifiyarka zaka rainawa wayo Yazid bani ba. Kai har Ka na da bakin da zaka ce min in yarda da kai ne? Hmm abunda ka yi min Allah yana ganinka kuma ka sani Alla zai saka min.  Ba zan taɓa yafe ma ba Yazeed. Allah ya isa tsakanina da kai".
Ta fada tare da dafa bangon ɗakin ta miƙe. Azababben ciyon da taji ne ya sanya ta sake komawa zaune tana fitar da ruwan hawaye.

Da sauri Yazid ya yunkuro don ya taimaka mata sai dai cikin zafin nama ta bige mishi hannu tana mai bashi gargadi na musamman da idanuwanta.

A hankali ta sake tashi cikin cije baki da daureya ta taka a hankali. "Buɗe min kofa in fita tunda ka biya bukatarki" ta faɗa ba tare da ta kallesa ba saboda kallonsa kaɗai wata fitina ce mai yawa a ƙahon zuciyarta.
 

Marairaicewa ya yi yana cewa"Dan Allah Afnan ki yi hakuri ki gyara jikinki sannan ki je dan Allah, ba Dan halina ba"

Wani wahaltaccen murmushi ta saki wanda ya fito direct daga ƙasan tafasasshiyar zuciyarta.
"Bai dace sunan Allah yana fitowa daga bakinka ba. Saboda bana tunanin  kasan Allah, dan da kasan shi da bakayimun abunda kayimin ba. ka bude mun kofa in fita nace!" Ta faɗa cikin tsawa.

Miƙewa ya yi jikinshi duk a mace yaje ya bude Mata kofar yana kallonta.

A hankali ta riƙa tattakawa tana dingishi, hawaye na fita a danuwanta har tabar gidan.

Allah ya taimaketa bata jima ba ta samu keke napep ta shiga ta isa gida, amma fa  kallo daya zaka yi mata ka gane cewa ba lafiya a tare da ita.

Cikin faduwar gaba tana bin gini ta  isa falon gidansu, mahaifiyarta ce kaɗai ta taras a falon zaune tana kallon sunnah tv.

"Subhanallah Afnan lafiya kuwa? Me yake damunki ne?" Cewar Mommy lokacin da ta yi arba da ita.

Kasa cewa komai Afnan ɗin ta yi sai kawai ta fashe da kuka.

Hankalin Mommy ya yi matukar tashi ta miƙe tsaye ta isa gurinta tana girgiza kafaɗɗunta.

"Ki faɗa min Afnan me yake damunki?"
Ta ce tana mai ƙarewa jikinta kallo.
"lahaula walakuwati illah billa, Afnan miye a zanenki haka?"

Jin wannan tambarya ne ya sake jefa Afnan cikin tsananin ruɗani da tashin hankali.

K'ank'ame momy ta yi lokaci ɗaya tare da sake fashewa da kuka tana cewa.
"Wayyo Mommy mutuwa zan yi marata ciyo take yi min sosai gashi period ɗin nan ya kunyata ni a cikin bus"

  Ajiyar zuciya Mommy ta sauke  tana dubanta cikin tausayawa " kai wannan ciyon mara naki yana bani tsoro. Allah dai ya yi miki maganinsa,  ki je ciki ki wanke jikin ki kisha maganinki ai akwai bai ƙare ba ko?"

Gayda kanta kawai ta yi Alamar Eh.

Mommy da kanta  ta jata ta kaita har daki tare da fitar mata da magungunanta sannan ta ce taje ta yi wanka da ruwan ɗimi, saboda ta riga ta san sosai ciyon mara ke azabtar da ita tun inda aka fito. Sai da taga ta shiga wankan ne sannan ta fita tana ƙara jin jina wahalar da take sha idan wata ya yi.

Afnan kuwa ba abunda take yi a toilet idan ba kuka ba.  rayuwarta ta mata zafi, ji take tamkar Allah ya dauki ranta ta mutu ta huta da wannan rayuwar da take ciki.
Ganin kuka ba zai yi mata magani ba ya san ya ta daure ta gasa jikinta a ruwan zafi sannan ta yi wanka ta fito.
Pain relief ta samu ta sake sha sannan ta kwanta.  Cikin kankanen lokaci bacci ya dauketa wanda ya kasance baccin bakin ciki mafi muni a rayuwarta.

Sai bayan la'asar ta falka, jikinta ba laifi ta ji sauki sosai sai abunda ba'a rasa ba. Arwalla ta ɗoro  ta yi sallah sannan ta sake kwantawa, sam bata damu da yunwar cikinta ba saboda ta san ko kaɗan ba zata iya cin abinci ba
.
Miss call din Yazid ta gani sun fi a kirga a wayarta tare da texts dinshi na ban hakuri, sai dai ganin su ma ba  karamin ƙara  tunzurata ya yi ba. Wata irin  tsanar shi take ji a cikin zuciiyarta.
kashe wayar kawai ta yi baki daya sannan ta kwanta, sai gab da magrib ta tashi, daƙyar Mommy ta  matsa mata taci abinci.

           
             

Yazeed ko YaseerWhere stories live. Discover now