"Yazeed ne........!" Kalaman da bakinta suka faɗa yayin da maganar ta tsaya cak ganin wani irin mugun kallo da Abba ke watsawa Yazeed yana nuna shi da yatsa.
Yaseer mutuwar tsaye ya yi yana tunanin Abunda Afnan ke nufi na ɗorawa yazeed alhali bashi ya aikata ba.
Cikin sauri Afnan ta yi saurin zuwa gaban Daddy ta riƙe kafafunwansa.
"Tabbas Yazeed ya ce min sunansa sai dai ba wallahi ba wannan Yazeed ɗin ne ba"
Wani mugun kallo Daddy ya watsa mata yana furzar da iska mai zafi.
"believe me. Wallahi tallahi ba wannan Yazeed ɗin ne ba, hasali ma Wanda ya yi min ba Yazeed ne sunansa ba, sai yanzu na gane haka"
Wannan karon kallon mamaki Daddy da duk wanda ke cikin ɗakin yake suke mata.
Ibrahim kuwa, cikinta ya yi da niyar marinta yaseer ya tare sa yana bashi haƙuri.
Ci gaba ta yi da maganarta tana shafe kwalla.
"Yaudara ta ne ya yi tsawon lokaci mai tsawo yana amsa sunan Yazeed. Sannan gidanka ne gidan da ya nuna min matsayin gidansu shiyasa nakai iyayena"
Kuka ta fashe dashi mai tsanani tana cewa
"Dan Allah ka yi haƙuri ka gafarta min na bata sunan zuri'ar ka da na yi ta hanyar yi masu sharri. na yi ne kawai dan in kare kaina. bana cikin hayyacina abun ya faru. Wallahi nan gidan ya nuna min ya ce nan ne gidan su, Dan girman Allah Ku yafe mun. Wallahi cikin yaranka ba wanda na taɓa gani sai jiya" ta faɗa murayarta sarƙe.
Wani sanyi Daddy ya jiya. At list ko bata faɗi gaskiya ba dai ta fitar da yaransa cikin shirmenta.
Hannu ya sanya ya taddo ta tsaye saboda ta basa tausayi ganin irin kukan da take yi.
"Ya a isa haka nan daina kuka, na yafe miki amma kada ki sake aikata irin haka ba kyau kin ji ko?"
Gyaɗa mishi kai ta yi tana jan ruwan hancinta.
Kafin ta ƙarasa gurin Yazeed da ke tsaye kamar icce. A hankali ta duƙa tare da cewa. "Dan Allah ka yafe mun abunda na yi maka, bani da wani zaɓi ne a wannan lokacin"
Ko kallonta bai yi ba saboda yanda yake jin tamkar ya je ya shaƙeta sai ta faɗi gaskiya, dan shi sam bai yarda da kalma ko ɗaya da ta faɗa ba.
"Bakaji ana baka haƙuri ba ne Yazeed?" Ammi ta faɗa fuskarta na nuna alamar gargaɗi zuwa garesa.
Taɓe baki ya yi tare da cewa"na ji mana. Na yafe mata ai"
Bata ce komai ba ta ƙarasa gaban Yaseer da ya zubo mata shanyayyun idanuwansa. Wani kallo yake mata, na ina son ki, kin rufa min asiri,kin kuma birge ni.
Ita kuwa wani kallo ta watsa masa, na, sai na ɗau fansa, sai ka gane kuren ka, daga gare ni ka ƙare yaudarar wata DIYA MACE.
Gabansa shima ta gurfana
"Ka yi haƙuri da sharrin da na yi maka. Sharrin shaidan ne"
Ji ya yi tamkar ya tashi ya rungumeta saboda yanda yake jin daɗin rufa masa asiri da ta yi.
Cikin zuciyarsa kuwa sai cewa yake 'what a good drama! Kai gaskiya yarinyar ta birgeni nasan ba don komai ta rufa min asiri ba sai don tana sona har yanzu'.
"Thank you so very much beb" ya faɗa cikin muryar da ita kadai zata iya ji. Kafin daga baya ya ce, "Allah ya yafe mana baki ɗaya"
Harara ta watsa masa sannan ta miƙe tana kallon Ibrahim da ke mata kallon karma ki matso nan.
Ganin haka ya sanya ta samu guri ta can kusa da Ammie ta rakuɓe tana matsar kwalla.
Gyaran murya Daddy ya yi tare da cewa "shi yaron da ya yi maki fyaden ina yake? Saboda nima ina da buƙatar sanin dalilin da yasa ya danganta kansa da gidana"
A hankali ta ce. "Ba San inda ya ke ba, saboda jiya na amshe wayar Ammi na kirashi. Ya tbbatar min da ba zan sake ganinsa ba don ba ma ɗan garin nan ne ba"
Jinjina kai Daddy ya yi yana mamakin yaudara irin wannan.
"Allah ya bi miki hakkink to" ya faɗa cikin nuna tausayawa kafin ya yi musu sallama ya tafiyarsa.
Saida suka fita Dukansu sannan Afnan ta kalle Ammie.
"Ammie me yasa kika hana ni faɗin gaskiya, anya ban cuce kaina ba kuwa?"
Murmuahi Ammi ta yi,
"Ba zaki gane abunda yasa na ce miki kada ki faɗa ba. Toh bari ki ji in gaya miki abunda baki sani ba. Ko kin ce Yaseer ne ya yi maki fyaɗe mahaifiyarsa ba zata taɓa bari Alhaji ya yarda ba, saboda wannan aika aikar da ya yi miki sai da ya tsara kayansa ta yanda ko kin neme gidansu ba za a yarda da maganar ki ba.
Wane namiji ne zai aikata alfasha da mace a cikin gidansu ba tare da yardarta ba idan har bai san abunda ya taka ba?
An yi maki fyaɗe na wata biyu kamar yanda cikin jikinki ya nuna. A gurin Alhaji kuwa Yaseer ya yi tafiya ne ta wata huɗu inda nake sa ran jiya satinsa ɗaya da dawowa.
Ni kaina da ba don nagansa kusan sau biyu ba wurin yarinyar abokiyar kasuwanci na da ba zan yarda ba, saboda nasan ance baya ƙasar. Kuma na tambaye Yazeed ya nuna min lallai bai dawo daga tafiyar da yayi ba. Saboda ranarma Alhaji ya sanya shi ya tura masa kuɗin wasu kaya da zai yi oder. Jin haka yasa na gane cewa ba wanda ya san yana gari kenan.
Bayan na sake ganinsa ne na tambaye yarinyar ta ce min Lagos yake zama gurin Amininsa wai bai samu bizar inda zai je ba shiyasa ya barwa wani ya yi masa aikin a can. Kuma ba zai iya gayawa mahaifinsa ba shiyasa ya zaɓi ya zauna can har lokacin da kayan zasu iso. Amma ta shaida min mahaifiyarsa na sane da inda yake.
Ni kuwa ba komai yasa na tsaurara bincike ba sai don kar a yi wata maƙarkashiyar da zata koma kan yarona da bai ji ba bai gani ba saboda nasan waye mahaifiyarsa.
Shiyasa na gaya maki kar ki kuskura ki ce shi ya yi maki fyaɗe saboda ko kin ce shi ya yi miki ba yanda za ayi kowa ya yarda da ke saboda baya gari lokacin da abun ya faru a tunanin mutane.
Kasa ƙwaƙwaran motsi Afnan ta yi jin maganar Ammie. rasa ma me zata yi ta yi. kukan ma kasa yinsa ta yi. Ta zuba ma Ammi ido tana jin wani abu mai kama da almara...........!!!!
Wato namiji a barsa kawai idan yana son cimma burinsa a kan macce toh komai zai iya Allah dai ya tsare mu da zuri'ar mu baki ɗaya.
Addu'a kaɗai zata cece ki daga mazan zamani saboda komai wayon ki wallahi namiji ya dame ki ya shanye. Ba a iya yima namiji wayo, addu'a kaɗai ce magani. Dan Allah mu kula mata. Bincike kafin ki tsunduma son namiji abu ne mai matuƙar kyau. Ke da kan ki zaki iya binciken wasu abubuwa ba sai kin jira an yi maki ba. Biyar diddigi kan namijin da kike so abu ne mai matuƙar amfani.
Allah yasa mu dace Ameen
