Shiru Yazeed ya yi saboda yanda yake jin kansa sam ba zai iya cewa ba zai yi masa ba matsayinsa na Amininsa, kuma haka yake jin ba zai iya yi masa ba saboda abinda ya faru.
Ganin yaƙi cewa komai yasa Yaseer ya kalle Ibrahim tare da saurin cewa.
"Kada ka damu zamu taimaketa insha Allahu" Ya fada yana kallon fuskar Yazeed da ta sake chanja yana yi zuwa ɓacin rai.
"Thank you very much guys am really appreciate, zamu yi waya idan Ana bukatar wani abu Nagode sosai" Ibrahim ya faɗa yana basu hannu ya fita da sauri dan sake amsa kiran wayar mahaifinsa.
Cikin tsananin ɓacin rai Yazeed ya juyo ya dube Yaseer. "Me yasa ka yi haka? Ko Kai kana da maccen da zata zauna ma da ita ne?"
Shima Yaseer ɗaure fuskarsa ya yi kafin ya yi magana. "ko babu ni zan zauna da ita saboda ba zan iya ganin wani yana neman taimako ba alhali kuma ina da halin taimakamasa in barsa ba, zaka iya tafiyar ka idan ba zaka iya ba"
Tsaki Yazeed din yaja yana mai saƙa wani abu a ransa amma kuma lokaci ɗaya ya watsar tare da cewa. "Wa ya sani ma ko Kai ne ka yi aika aikan" ya faɗa idanuwansa sarƙe cikin na Yaseer.
Murmushi Yaseer ya yi, "nagode Allah dai da kowa yasan waye tace ya yi mata. na tabbatar da ko yanzu ta sake buɗa baki zata ce Yazeed ne ya yi mata fyaɗe ba Yaseer ba. Sannan daɗi da ƙari ba a taɓa kawo ƙarata na yiwa wata ciki ba ko something like that so nasan ko miye ma kai ne zaka haɗa mata cox at the first place Kai............."
"Just shout up crazy boy" Yazeed ya katse Yaseer cikin tsawa. Idanuwan nan nashi sun yi jajur kallo ɗaya zaka yi mishi kasan yana cikin ɓacin rai mai yawan gaske.
Tsaki Yaseer ya yi tare da fita waje saboda yasan komai zai iya faruwa idan Yazeed ya yi irin fushin nan. Yana fita direct massalaci ya nufa saboda an fara kiraye kirayen sallar magrib.
Bayan sallar isha'i duka su biyu suna dakin ba wanda ya ce da wani ci kanka kowa dannar wayarsa kawai yake yi. Duk da sosai Yaseer ya yi mamakin ganin Yazeed ɗin amma sam bai nuna ba sai ya sharesa kamar yanda shima ya sharesa.
Sun ɗan daɗe zaune kafin Nurse ta shigo. Sai da ta ɗan ƙare mata dube dubenta kafin ta ce.
''Yakamata ace mace ta zo ta tsaya da ita if possible if saboda akwai abubuwan da ake bukatar mace ta yi mata duba da yanayinta"
Yaseer ya ce. "Dole ne sai mace zata iya tsayawa da ita ne?" Ya tambaya cikin ƙarin son jin bayani.
"No ba dole ba ne tunda ita kaɗai take cikin ɗakin, amma gaskiya idan da mace zai fi. Any way ko mijinta ma ai zai iya tunda dole mutum ɗaya ne zai rika kwana da ita. Kai Doctor Yazeed ai kasan da dokar ai ko?"
Gyada mata kai kawai ya yi, alamar eh.
Sai da ta yi 'yan rubuce rubucenta da zata yi sannan ta wuce abunta.
Yazeed yaja tsaki yafi ɗari kafin ya yi magana.
"Duk tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka. Nasan dai ka ji abunda Nurse ta faɗ yanzu sai ka faɗi yanda kake so ayi da ita yanzu"
Ajiyar zuciya Yaseer ya yi yana hango wata irin chakwakiya mai yawa cikin lamarin. Amma saboda yana son ya daɓawa Yazeed haushi sai ya yi murmushi tare da cewa.
"Mai uwa a gindin murhu ba ya kukan bai koshi ba. Let me call my mother nasan she can't deny me"
Ya faɗa yana zaro wayar shi a aljihu.
Bugu ɗaya ta ɗauka cikin shagwaɓa da sakuwa yake yi mata magna.
"Pls mom wlh yarinyar tana cikin mawuyacin hali ne, haba mom ko Nusaiba ce to sai ki turo dan Allah. oh my God yaushe fadeelan ta tafi ne?"
Banji me ake cewa bangaren can ba amma ga alama bai samu nasarar convincing mahaifiyar tashi ba ko dan ganin yanda ya ajiye wayar jikinsa ba ƙwari.
Yazeed kuwa dama ya san waye Mahaifiyar Yaseer kallonsa kawai ya yi suka haɗa idanuwa. Ya ce.
"Na san ba zata zo ba ko?" Ya faɗa yana ya mutsar fuska saboda baki ɗaya asibitin ta gunduresa.
"Ba zata zo ba saboda ba zata bar mijinta shi kaɗai ba" Yaseer ya bashi amsa.
cikin son yaƙara masa haushi ya kara da cewa why not ka kira Ammie kamar yanda Yayanta ya roƙa tunda kuma ma ita ba wanda take kula dashi, dana ita yafi cancanta ta zo ta kula da ita tunda babu nauyin wani bisa kanta"
Sosai Yazeed ya san magana ce Yaseer ya gaya masa amma sam bashida lokacin kulasa dan haka bai ce komai ba ya lalubo sunan Ammie a wayasrsa ya kira.
