Ganin har dare bata samowa kanta wata mafita ba ya sanya ta je, ta ɗoro alwala ta fara sallah tana kai kukanta ga mahalicinta.
Ba ita ta tashi kan dardumar ba sai da aka kira sallar asuba. Bayan ta yi sallah ne ta samu bacci ya kwasheta mai cike da mafalkai iri iri.
Misalin sha biyun rana ta samu ta tashi ta yi wanka ta yi breakfast sannan ta nufe d'akin Ammi domin ta gaidata.
Da sallama ta shiga ɗakin.
Kallo ɗaya ta yi wa Yazeed da ke zaune gefen Ammi ta kauda kanta gefe tana dana sanin shigowarta, samakon wata uwar harara da ya watsa mata.Gurin Ammi ta nufa ta rusuna cikin ladabi ta gaidata.
cikin fari'a Ammi ta kamo hannunta.
"Yau kam Afnan kin sha bacci. Ni da naga har goma ta wuce baki fito ba na yi zaton ko ba lafiyaba sai da na leƙa na tarar kina ta sharar baccinki, sannan hankalina ya kwanta"Murmushi Afnan ta yi. "Ban ma san lokaci ya ja haka sosai ba"
"Ai ƙara ki riƙa samun hutu da fatar dai dai kin yi breakfast?" Ammi ta tambayeta cikin kulawa.
"Eh na yi Ammi"
Ganin kaman bata kyauta ba na rashin gaidasa gaban mahaifiyarsa yasa ta juya wurinsa ta ce "Ina kwana"
Bai so amsawa ba saboda ya tsani irin gaisuwarta amma gannin Ammie ta kallesa yasa ya ce. "Lafiya"
Ganin wurin ya dan yi shiru ne yasa Ammie ta dubi sa. "Me za ka ci ne sai Afnan ta girkama tunda aiki nake yi?"
Taɓe baki ya yi. "Babu na fasa ci idan na fita waje zan ci." ya ce tare da miƙewa.
Kallonsa Ammi ta yi galala. "Ina za ka je ne ba mu ƙare magana ba?
"Wucewa zan yi Ammie naga yanzu kika yi waya za ki fita"
"Koma ka zauna ka jirani, ai ba daɗewa zan yi ba, nan cikin unguwa ne zan je in dawo"
Bai yi musu ba ya koma ya zauna yana dannar wayarsa.
Ganin Ammi nata shirin fitar ne ya sanya Afnan miƙewa ta ce. "Ammi zan biki dan Allah in ɗan miƙe ƙafa"
Murmushi Ammi ta yi. "A'a Afnan ga kayana can da aka karɓo min wurin wanki ki haɗa min su a wardrobe ba daɗewa zan yi ba yanzu zan dawo. Idan kuma kika ƙare haɗawa ban dawo ba sai Yazeed ya kai ki nan gidan hajiya safiya ina can. Kin ji?"
Amsata kawai Afnan ta yi amma sam wannan abun bai yi mata daɗi ba.
Ɗagowa Yazeed ya yi ya kalle Ammi cikin mamaki dan shi tsaf ya gane inda ta dosa. Cikin sa'a itama ta kallesa idanuwanta ɗauke da gargaɗi mai girma.
"Ni na tafi sai nadawo, idan ka canja shawara ko indomie ce sai ta dafa maka"
"Adawo lafiya" kawai ya ce ya maida kansa ƙasa yana ci gaba da danna wayarsa.
'Wato dai ammi so take in saba da yarinyar nan ko ta ƙarfin tsiya ne' Ya faɗa a zuciyarsa tare da sakin wani malalacin murmushi.Ita kuwa Afnan ba ta ma samu damar magana ba saboda haushin da take ji. kawai gurin kayan Ammien ta je ta fara haɗawa da sauri.
Tsawon lokaci ba ka jin motsin komai ɗakin sai kukan a.c da fanka dake aiki.Ɗago kansa ya yi, ya kalle ta a karo na farko da ta shigo ɗakin. Ganin yanda take ta sauri ta haɗa ta fita ne yasa ya ji yana son ya ɓata mata lokaci.
"Ke" Ya kirata cikin gadara
Sosai ta ji sa amma ta yi banza da shi.
"Ke hala kurma ce ba kya jin ina kiranki ne?"
Sai lokacin ta juyo ta ɗan kallesa.
"Ni ba ke ne sunana ba" ta faɗa tana turo baki."Oh haka ne fa. To ya sunanki? Dan ni ban sani ba"
"Ai ba dole ne ka san suna na ba saboda sanin sunana ba shida amfani a gare ka. Idan kuma ka damu da sani sai kaje ka tambaye wanda ya raɗa min sunan" ta faɗa kanta tsaye.
Jin abunda tace ne yasa ya miƙe ya isa kusa da inda take. Nan take ta ji jikinta ya ɗauki rawa sai zarar ido take yi tamkar (zee kaura).
Kunneta ya kama ya matse shi sosai cikin salon ƙeta ya ce. "Sake maimaita abunda kika ce""Wash Allah zafi! Dan Allah ka sake min kunnena"
K'ara matse kunnen ya yi. "Baki da kunya ko? Zan nuna maki na fiki ji da rashin kunya" ya faɗa yana ƙara mirɗe kunne.
Idanuwanta sun yi hajur harda kwallar wahala saboda azaba.
"Dan Allah ka yi haƙuri ba zan sake ba"Ganin yanda hawaye ke ta zuba a idanuwanta ya sanya ya saki kunnen tare da kafeta da manyan idanuwansa.
"Ina fatar kin gayama Ammi abunda kika ce zaki gaya mata saboda ni ban shiryama auren karuwa ba"
Cikin rawar baki Afnan ta yi magana. "Duk abunda za ka yi min ka yi min amma dan Allah ka daina kira na da karuwa, saboda ni ba karuwa ba ce. Magana kuma na riga na gayawa Ammi cewa ba zan aure ka ba. Saboda ni a wurina da auren irinka da bai san me ake nufi da kalmar kaddara ba ƙara in aure ko wane irin mutum mahaifina zai zaɓar min koda kuwa maigadin gidanmu ne.
kuma nagode ƙwarai da halaccin da ka yi min kai da mahaifiyarka Allah ya saka maku da alkhairi. Insha Allahu daga gobe ba za ka sake ganina gidanku. Wata ƙil ma ba zamu sake haɗuwa ba har abada". Tana kaiwa nan ta raɓa ta gefensa ta wuce tana goge hawayen idanuwanta.Yazeed kam tsaye ya yi tamkar an shuka dusa. Kalaman Afnan ba ƙaramin tasiri suka yi mai cikin zuciya ba. Wani Abu ya riƙa jin yana ratsa dukkanin jini da gangar jikinsa zuciyarsa har wani tururi take yi masa.
Kalamanta sun tsaya masa a zuciya.
Zaune ya yi kan gado tare da dafe kansa. Abunda yake ji bai taɓa jin makamancin sa ba. Ga magangannun da suka yi da Ammie na dawo masa ɗaya bayan ɗaya.
Shi yanda ma ta samu ƙarfin guiwar gayawa Ammie ba zata auresa ba yake son ya sani saboda sosai abun ya kwance masa kai.Ni dai na ce anya Malam YAZEED ba a faɗa TARKO ba?
Muje dai zuwa Mahaukaci ya hau kura.