Babi na arba'in

608 51 7
                                    


Suna cikin tafiya sun kusa kai part ɗin Mamie kenan suka ci karo da Yaseer.

kallo ɗaya ya yi musu ya kauda idanuwanshi sakamakon zuciyarshi da take wani irin tiriri. kasa tafiya ya yi inda zaina, sai ya yi tsaye tamkar wanda aka dasa.

Yazeed na ganin hakanan ya sake  kamo Afnan ya karata da jikinsa ya sanya hannunshi ɗaya ya riƙo ƙugunta. Wani irin murmushi mai ƙayatarwa ya sakar ma Yaseer tare da cewa "morning bros. Har za a fita aikin ne"

Tsaki  Yaseer Ya yi kaɗan, sai ya yi banza da Yazeed ɗin kamar bai ji sa ba. Can kuma  ya ji sam ba zai iya kyale Yazeed bai soka mishi magana ba.  murmushi ya aro ya azawa fuskarsa.

"Ango kasha mai"  ya faɗa tare da rufe bakinsa da hannunsa kafin ya ce.
"Sorry bross na manta da ba mai a garar ta ango. Haka aka kawota ba tare da ta cika complete ba"

Maganar tashi ta soke Afnan ba ko kaɗan ba. Sai dai jin yanda Yazeed ya kara matseta jikinshi alamar kar ta damu yasa ta ɗan ji wani sassaucu a ƙasan zuciyarta.

Shima cikin murmushi Yazeed ya ce.
"Idan dai har haka irin wannan incomplete gara take toh nikam sai dai godiyar Allah. Saboda ta yi min ɗari bisa ɗari. Gashi kuma naga duk da  kasancewar ta ba cikakka ba haka naga da yawa sun bar complete ɗin suna neman su yi wawusu kan incomplete.  Ni kam sai godiyar Allah  tunda dai ni na zama champion" ya ƙarashe tare da ƙara rungumeta sosai jikinsa yana ƙara gyara mata mayafin jikinta.
Bai sake bi ta kan Yaseer ba ya jata suka wuce inda za su.

Da sallama suka shiga falon Mamie. Nabeela ce kaɗai zaune tana kallo sanye da wata arniyar rigar bacci da kusan duk  surar jikinta ana ganinta. Kuma wai a haka ta fito falo ta zaun tana kallo ko a jikinta ga gidan da alama kowa ba iya shigowa ba tare da ya jira iso ba.

kallo ɗaya Yazeed ya yi mata ya kauda idanuwanshi saboda ta san sam ba ya son wannan ɗabi'a tata ta sakin jiki.

Afnan kam kallonta take yi tana mamakin ta, ace ƙarfe kusan goma sha ɗaya mutum na sanye da kayan bacci. Kuma kayan ma ba kayan albarka ba. Haushinta ne ta ji ya kamata dan ta riga ta san da maganar aurenta da Yazeed. Kallonsa ta yi taga sam hankalinsa bai kan Nabeelar sai ta samu kanta da jin sanyi cikin ranta.

Nabeela kuwa tunda ta karɓa musu sallamar ta fara yatsinar fuska tamkar wadda taga kashi.

Daƙayr ma ta samu ta gaida Yazeed.

"Mamie fah?" Ya tambayeta ba tare da ya kalleta ba.

"Tana ciki" ta faɗa tare da miƙewa. Da alama kiranta za ta yi. Tana tafiya tana wani jujjuya jiki. Sai abun  yaso ya bama Afnan dariya saboda ko alama Nabeela ba tabda kirar kwarai. Tana da kyaun fuska Amma jikinta haka yake tamkar an girke baho.

Murmushi ta yi lokacin da suka haɗa idanuwa da Yazeed.
Shima murmushin ya sakar mata tare da kara matse mata hannu cikin nasa.

Suna cikin haka ne Mamie ta shigo da fari'arta irin ta ƴan duniya.

Har ƙasa Afnan ta duƙa ta gaidata.

Tana murmushi ta ce "amarya ya baƙunci?"

Murmushi Afnan ta yi kanta na ƙasa ta Amsa da "Alhamdulillah"

Mamie ta ci gaba da magana tana yi ma Afnan wani shu'umin kallo.
"Dan Allah amarya a kula mun da ɗana kin san sabon shiga ne bai saba ba. Dan Allah a lallab'a kar a zure har  a kai ga shanye mishi ruwan kai kin ji?"

Afnan tune ta gano inda maganar Mamie ta dosa. Wani irin abu ta riƙa ji yana taso mata har ya toshe mata zuciya. Nunfashinta ta ji ya fara yin sama alamar ranta ya yi ƙololuwar ɓaci.

Ba tare da Mamie ta lura da yanayin Afnan ɗin ba ta ci gaba da magana. "kinga ke kin riga da kin san abunda an nan, don haka dan Allah a kula a ɗan riƙa daga mishi ƙafa don ya samu damar sauke wani nauyi dake bisa kanshi".

Yazeed ko YaseerWhere stories live. Discover now