Babi na sha shida

602 53 2
                                    

Har kusan magrib Afnan bata san inda kanta yake ba.
cikin jikinta ya zube saboda wahala da damuwar da ta shiga. Gashi ta zubar da jini da yawa har saida aka yi mata ƙarin jini.

Har zuwa wannan lokacin kuma Yazeed da Yaseer suna nan a asibitin kaman yanda Mahaifinsu ya buƙata.

Yazeed yana zaune ne kawai saboda amincin da ke tsakanin shi da Ibrahim duk da cewa ba wani daɗewa suka yi da sanin juna ba. Amma kasancewar zamansu guri ɗaya kuma suna kusan sa'annin juna ya sanya suka ƙulla alaƙar amintaka a tsakaninsu.

Yaseer kuwa  Abubuwa da yawa ne suka shi zama a asibitin duk kuwa da irin mamakin kansa da yake na aikata hakan bayan abunda ya aikata ga zuciyar da yake zaune domin ta.

  Ibrahim ne ya fito cikin  ɗakin da Mommy take saboda tun bayan da aka samu kanta aka chanja mata ɗaki aka ɗauke ta daga emergency.

hannu  Ibrahim ɗin ya basu suka yi musabuha tare da ce musu. "Ban san da bakin da zan maku godiya ba da irin dawainiyar da kuka yi duk da an ɓata maku. Nagode kwarai Allah ya saka muku da alkhairi"  ya faɗa muryarsa ɗauke da tsantsar nadama.

"Ameen ba komai ai yiwa kai ne" Yazeed ya faɗa yana ƙoƙarin wucewarsa.

Da sauri Yaseer ya ce. "Bari Mu shiga daga ciki mu ganta sai mu wuce lokacin sallah na gabatowa"

Hararar sa Yazeed ya yi saboda  shi bai so haka ba. Son ya yi su wuce tunda ga Ibrahim ɗin nan yazo. Dama don ganin hankalinsa ya kasu uku ne yasa suka taimake sa.
Ganin za su wuce ne yasa shima dole yabi bayansu suka shiga ɗakin da Afnan ɗin take ciki.

Kwance take har zuwa lokacin. Kallo ɗaya zaka yi mata ka gane cewa tana cikin mawuyacin hali saboda yanda take jan nunfashi da yanda take saukar da shi.

"Har yanzu bata falkla ba?" Cewar  Ibrahim yana duban nurse din da ke daura mata wasu drip a hannunta.

"Eh Gaskiya yanada wuya ta falka yanzu saboda Injections ɗin da aka yi mata masu karfi ne, inaga sai dai zuwa dare ko gobe da safe ko tana falkawa"

Cikin damuwa Ibrahim ya buɗe baki zai yi magana, wayar hannnusa ta yi ƙara.

Cikin ladabi yake karɓa wayar  wadda ko ba a faɗa ba ka san  da mahaifinsa yake maganar duba da yanda yake karɓar umurni a maganar tasa. Yanayinsa sosai ya chanja sai haƙiri yake bawa mahaifin nasa.
Sauke wayar ya yi bayan ya kammala fuskarsa cike da damuwa mai girma.

Yazeed da Yaseer kuwa zuba masa idanuwa suka yi suna kallonsa ganin yanda yaketa haɗa zufa.

"What happen Dr" Yazeed ya tambayesa  yana kallon sa.

Shafe zufan da ke  karyo masa ya yi, "their is problem Dr Yazeed and I really really  needs of  your helps pls" ya faɗa yana mai haɗe hannayensa guri guda alamar roƙo

"Ok inajin ka how can we help u?" Yazeed ya faɗa yana mai sauke hannayen Ibrahim ɗin ƙasa.

Cikin damuwa Ibrahim ya ce, "Abba ne Ya ce yanzu yanzun nan in zo yana nemana kuma baya so ƙafata ta sake takowa wajjen  da Afnan take saboda ya riga ya yafeta bata cikin 'ya'yansa,  idan kuma har na sake na yi bai yafe min ba" ta faɗa idanuwansa cike da ƙwalla.

"Subuhanalla"  Yazeed ya furta, yayin da Yaseer ya faɗi jagwab zaune kan kujerar da ke gefensa  yana dafe kansa da dukkanin  hannayensa.

Ajiyar zuciya Yazeed ya yi yana mai jin haushin iyaye irin nasu Ibrahim da basa daukar ƙaddara.
Cikin jun haushi ya furta. "To mu me za mu yi mata?"

Ibrahim bai damu da yanda Yazeed ɗin ya yi magana ba ya ce.
"Ina so dan Allah ku taimaka min ku ɗan kulamin da ita, har zuwa lokacin da za'a sallameta nasan mahaifinmu ya faɗa ne kawai saboda fushin zuciya,  na tabbatar da insha allahu  kafin lokacin ya sauko daga fushin da yake yi da ita. pls Yazeed don't say no dan Allah ko Ammie ce ka yiwa magana ta zo, na san ba zata ƙi ba.
Duka 'yan uwanmu suna nesa kuma bana ma son abun nan yaje gurin danginmu dan Allah ku taimaka min" ya faɗa muryarsa karye.

Yazeed ko YaseerTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang