Yazeed ko Yaseer
Ayshart Farouq
NWA
3
Da sauri Afnan ta is a gida gabanta sai
faɗuwa ya ke yi ganin motar mahaifinta da ta yi. Salah Maiaikinsu
taci kari da ita a falo.
Cikin faɗuwar gaba ta ce.
"Momy fa?"
Salah ta ce," tana sama gurin Alhaji"Ɗakinta ta wuce jikinta duk ya mutu ta yi zaune tare da rafka uban tagumi. Allah Allah kawai take tana
addu'a Allah yasa baima momynta
faɗa ba.
Tana nan zaune cikin zullumi
Ta ji wayar Momynta ta sake shigowa.
Da Sauri ta ɗauka ta ce. "Mommy na dawo tun dazu Ina ɗaki"Can bangaren Mommy ta amsa da cewa "Afnan kizo DaddynKu na neman ki"
Abunda take ma gudu ya auku yau sai tasha faɗa.
Ba tare da ɓata lokaci ba ta nufi part ɗin mahaifin nata cikin faɗuwar gaba, saboda har ga Allah
ta tsane kiran mahaifin nata duk da ta san baima fiye ɗaure mata ba akan sauran yayunta. Ita laifinta yafi shafuwar Momynta.Da sallama ta shiga ɗakin tare da gaida iyayenta.
cikin fari'a Abba ya ce, "Zo nan uwata" murmushi
Afnan ta saki ganin ba wata matsala a fuskarsa hasali ma murmushi ta gani kwance kan leɓensa.Can ta matsa kusa da shi "Abba sannu da dawowa"
"Yawa uwata ana nan ana ta hutu ko?"
"Eh ai hutun ma ya kusa k'arewa"
"Masha Allahu bani wayar ki nan" ya ce yana kallonta
Kafin ta ce wani abu wayar da ke hannunta tayi ƙara.
Kallon wayar ta yi kafin ta kalle Abba, gabanta na wani irin bugawa.
Ganin yanda ta kallesa ne yasa ya mik'a hannu ya karb'i wayar don yaga abunda ya tsoratata.
ganin sunan mai kiran wato Maryam2 yasa ya mik'a mata wayar "ɗauki mana ba ƙawarki ba ce¡"
Amsa ta yi, sai dai kafin ta yi wani abu har Call din ya tsinke.
Ajiyar zuciya ta sauke har saida Abban ya kalleta.Kafin su ce komai wayar ta sake daukan ruri a karo na biyu.
A hanakali ta kara wayar a kunnenta"assalamu alaikum" ta ce tana mai sake rage volume ɗin wayar.
can ɓangaren aka amsa da "My princess da fatar kin isa gida lfy?"
marar gaskiya Ko a ruwa sai ya yi jiɓi. Duk sanyin a.c ɗin dake ɗakin bai hana Afnan yin zufa ba. Saboda ganin ta ke yi tamkar ana jin abunda Yazid ɗin ke faɗi.
A sanyaye ta dake tare da cewa, "Maryam ki daina yi min maganar nan bana so dan Allah. Ok to sai mun hadu a islamiyan gobe"
ta yi saurin datse wayar tare da mikawa Abbanta wayar.Cikin murmushi ya karɓa, sai da ya duba contacts dinta kaf duk tana zaune tana kallon
shi. Wata kwalla Ce ta zubo Mata wadda ba ta san
lokacin da ta zubo ba.Momy dai zaune kawai take tana ganin ikon Allah. Duk da cewa ba wannan ne farau ba.
Sosai Afnan ta bata tausayi ganin yanda take ƙwalla.Cikin ranta kuwa haushi ta ke ji da takaicin hali irin na mijinta da ya kasa gane halin da rayuwa take ciki
a wannan zamani.Kasa hakura ta yi sai da ta yi magana. "Amma dai fisailillahi Alhaji abunda kakewa Afnan sam bai dace ba. kaine fa ka haifeta amma ace sam ka kasa yadda da ita wannan wace irin rayuwa ce?"
Ɗagowa ya yi ya kalleta fuskarshi tamke. "Bana son irin abunda kike mun zainab. Ni Ina hango abunda baki hango ba. Kun matsa abata
waya na bata waya. Don haka dole ne a gareni a matsayina na mahaifinta in lura da abunda take yi da wayar, saboda bana son Allah ya kamani da wani laifi akan tarbiyar Afnan gobe kiyama, don haka idan kinji kina iya taimaka min mu tarbiyantar da
ita walillahil hamdu idan kuma kinji baki iyawa kar ki sake min magana akan abunda nake ganin shine dai dai"Cikin ɓacin rai momy ta ce, "Ai wannan abun da kake ba shine tarbiya ba. Duk wata tarbiya da zaka ba ta bai wuce ka aurar da ita ba"
Ɗaga Mata hannu yayi "kinfi kowa sanin cewa ni mutum ne wanda yake so yaga Dan Adam ya dogara da kansa don haka maganar aure ba matsala ba ce. Idan lokaci yayi ni da kaina Zan
zaɓo Mata mijin da ya dace da rayuwarta"Afnan na jin wannan maganar ba ta San lokacin da ta fashe da kuka ba. Wanda saida ya baiwa iyayen
nata mamaki dukan su.
Da sauri Abba ya dubeta "Me ye haka Afnan? Me ki ke yi wa kuka ne?"Cikin bacin rai momy ta ce. "Ai dole ta yi kuka tunda ta ji kana nema ka tauye Mata hakkinta, wallahi Alhaji kaji tsoron Allah. ka sani fa yanda mu ke da hakki a kan yaranmu haka suma suke da hakki a kan mu"
Jikin Abba yayi matukar sanyi baice komai ba ya miƙawa Afnan wayarta tare da cewa. "Tashi ki je ɗaki Afnan, yi haƙuri ki share hawayen ki zan sake nemanki"
Jikin Afnan sanyi kalau ta tashi ta je ɗaki da tunani da yawa a cikin zuciyarta.
Number maryam2 ta lalubo wato Yazeed ɗinta. Fira suka shiga yi sosai tamkar za su cinye junansu
saboda so da ƙauna.Ba su sukayi sallama ba
saida aka fara kiran sallahr magriba..
