Yazeed ɗa ne tal gun Alhaji Ahmad Abdulrahman.
Mahaifinsa Alhaji Ahmad ya rabu da mahaifiyarsa Hajiya Ameena tun Yazeed ɗin yana ɗan shekara biyar kasancewar dama ba auren soyayya suka yi ba. Auren dangi ne suka yi, kuma da basu samu jituwa ba suka rabu duk da cewa lokacin mahaifiyarsa ta fara developing feeling kan mahaifin nasa. Amma da yake shi sam hankalinsa na gun wata yasa zaman yaƙi daɗi sai da aka rabu.Bayan sun rabu ne cikin ikon Allah ta sake aure, ta haifi yara biyu Hafsa da Usman.
Bata daɗe da haihuwar Usman ba Allah ya yi ma mijinta rasuwa. Kasancewar sa mai hali sosai ya sanya ta gaji dukiya mai yawa.
Ganin tana da dukiya bai sa ta zauna haka nan ba sai ta faɗa harakar business dan ganin ta sake gina kanta da yaranta.
Bayan rasuwar mijinta da 'yan shekaru sai kuma Allah ya yi wa Usman rasuwa shima kasancewar dama tun da aka haifesa ba lafiyayye ne ba.
yanzu Hajiya Amina (Ammie) tana nan gidanta daga ita sai ɗiyata Hafsa sai kuma yazeed da ke kai mata ziyara lokaci lokaci kasancewar ana gari ɗaya.Mahaifinsa kuma tunda suka rabu da mahaifiyarsa sai ya aure Hajiya Zuwaira da ta kasance tsohuwar budurwarsa wadda ta yi aure wani guri ta fito da diya biyu, wato Yaseer da Nabeela.
Ganin mijinta mai shahararrun kuɗi ya sanya ta kwaso yaranta ta maidosu hannunta sai abunda sukaga dama suke aikatawa cikin gidan.Sai dai ganin har ta shekara biyar ba ta samu haihuwa da Alhaji Ahmad ba ya sanya ta ɗoki karan tsana ta dorawa ɗansa Yazeed ganin shi kaɗai ne Alhaji Ahmad ya mallaka wanda ko mutuwa ya yi shi kaɗai zai gade sa.
Ganin yanda Alhaji ke son janyosa ga lamurransa ne suka sake tunzurata saboda komai sai yace Yazeed. Hakan da yake ne yasa ta fara lurar da Yaseer kan ya shiga cikin al'amuran Mahaifin. Tun yaron bai fahimta har ya fara fahimta. Nan take sai hasada da ƙyanhi suka shiga zuciyarsa na ganin duk abunda Yazeed ya mallaka shima yana son ya mallake irinsa.
Tun Yazeed na ƙarami burinsa da na mahaifiyarsa ya yi karatu ya zama cikakken likita, inda mahaifinsa kuma shi so yake ya zama kwararren dan business kamarsa dan ya riƙa lura da al'amuransa ko bayan ransa.
Kasancewar sa yaro mai taurin kai yasa ya bi ra'ayin kansa ya karanci abunda yake so inda shi kuma Yaseer ya karanci fannin business ɗin duk da ba shine ra'ayinsa ba shima ra'ayinsa ya zama likita irin Yazeed. Amma ganin yanda mahaifiyarsa ta dage yasa ya zubar ya yi wanda take so.
Tun da Yazeed da Yaseer suka girma suka mallaki hankullan kansu, sai Yaseer ya kasance mutum mai neman matan tsiya, da kuma ƙarya da nuna ɗan wani ne. duk maccen da Yaseer zai nema ba zai je mata da ainihin sunan shi ba sai dai ya ce sunasa Yazeed ko Ahmad.
Sai tafiya ta yi tafiya ne ya tabbatar da yar hannu ce ke sannan zai gaya maki gaskiyar sunansa.
idan aka masa complain sai ya ce yafi jin daɗin Yazeed kan Yaseer kuma sunan dan uwansa ne da haka yake kulle bakin mutane.Kuma babban abinda yasa ba a cika ganesa ba saboda duk friends dinsa da Abdulrahman Y Ahmad suke kiran sa.
ma'ana, Yaseer Ahmad Abdulrahman, da wannan ne ya samu yake yaudarar 'yan mata son ransa.
sai dai kuma duk meman matan sa bai taɓ yi ma wata fyade ba, da yawa ma matan su suke kawo kansu gare shi, Afnan ce macce ta farko da ya nema ta karfi ganin sha'awarta na nema ta illata sa.Yazeed kuwa ganin irin abubuwan da Hajiya zuwaira ke yi masa ne ya sanya ya yi kudurin ganin bai dogara da mahaifinsa ba.
Saboda ko bayan dawowarsa daga karatu saida sunka kai ruwa rana da mahaifin nasa kan cewa dole ne ya yi masa aiki kamfunnansa shi kuma ya dage ba zai yi ba. Wannan na ɗai daga cikin abunda yasa mahaifinsa bai damu dashi ba yafi nuna damuwarsa kan Yaseer saboda shi yana yi masa duk abunda yake so.Sosai Hajiya Zuwaira ta ɓatawa Yazeed suna gurin mahaifinsa sam baya ganin farinsa don sau da yawa idan tana son kudade masu tsoka zata shirya da wata aje gurin Alhaji ace Yazeed ne ya mata ciki idan yana so a zubar a rufe maganar sai ya bada kudi kaza.
Shi kuma matsayinsa na dan siyasa babban mutum da ya tsani ɓacin suna zai bada ko nawa ne. Sai dai kawai yakira Yazeed ya riƙa zaginsa yana alawaddai da halinsa. Tun abun na damun Yazeed har ya daina damunsa da zaran ya kirasa ya ce kai ka yiwa wance ko wannan ciki sai kwai ya ce eh shi ya yi dan ya ƙarawa mahaifinsa haushi tunda sam bai yarda dashi ba.Ganin abun na so ya wuce wuri yasa Nabeela ɗiyar Hajiya Zuwaira da ke bala'in son Yazeed kamar ta fadowa Allah ta yiwa uwarta jan ido kan zata sanarda mahaifinta gaskiya, sannan Hajiya Zuwairat ta daina ɓatawa Yazeed suna ta wannan hanyar.
Sai kawai ta neme wata hanya wai Alhaji ya haɗa Nabeela da Yazeed aure ko Yazeed ɗin zai nutsu. Sosai Alhaji ya ji daɗi dan ganin Hajiya Zuwaira bata guje gudan jininsa ba duk da tasan halayensa ba masu kyau ne ba, dan shi har ganin yake ma kamar yaron nashan wani abu.Yanzu dai cikin ikon Allah al'amuransa da mahaifinsa sun ɗan fara dai daita saboda irin fadan da Ammie ke yi masa.
Abun na ƙonawa Hajiya Zuwaira rai sai dai sanin abinda zata shirya gaba yasa ta ɗan rage hasa wutar zuwa wannan lokaci.
An dawo labari.
Bayan wucewar yazeed da yaseer ne Ammie ta tsurawa Afnan ido tana nazarin wani Abu da game da yarinyar.
A hankali Afnan ta buɗe idanuwanta tana kallon Ammie. Ganin haka ya sanya Ammi matsawa kusa da ita tana yi mata sannu.
Tunawa ta yi da abunda ya faru, nan ta ke ta miƙe zaune tana kiran sunan Momminta.
Kuka ta ke yi sosai tana cewa. "Shi kenan ta mutu ko? Na kashe mahaifiyata. Wayyo ni Allah na shiga uku na kashe mahaifiyata."Yanda take Kuka tana sabbatu ne yasa
Ammi ta rungumeta tana bubbuga bayanta.
"Yi shiru 'Yata mahaifiyarki tana raye bata mutu ba, yi shiru daina kuka kinji."Cikin rashin yarda Afnan ta tambaye ta ko waye ita.
Murmushi Ammi ta yi tare da faɗa mata ko ita wace ce saboda ganin yanda ta ɗaga hankalinta.
Cikin sauri Afnan ta zame jikinta daga gareta ta kwanta wasu hawaye masu zafi da ƙunar zuciya suna fita daga idanuwanta.
Sai yanzu komai ke sake dawo mata cikin kwanyar kanta. Mamaki ta ke yi sosai na yanda aka yi tsawon shekara ɗaya tana tare da mutum amma sam ta rasa gane takamammen sunansa. Wasu abubuwa take tunawa da su can baya lokacin da suna soyayya. Lallai namiji a barshi kawai saboda ita bata ma san ya za ta kira kanta ba, marar HANKALI KO DABBA?.
Lol Pls masu karatu ku gaya mata sunanta.
![](https://img.wattpad.com/cover/95453973-288-k589738.jpg)