Babi na ashirin da huɗu

661 53 1
                                        


Ganin yanda hankalin Afnan ya tashi ne ya sanya Ammi ta ja hannunta ta zaunar da ita tana raɗa mata
"Ki kwantar da hankalinki Afnan ba abunda zai faru sai alkhairi kin ji?"
Kai kawai Afnan ta iya ɗaga mata saboda bakinta  ya riga ya mutu.

Duk yanda take ɗokin ganin iyayen nata  da son ta kasance tare da su. Yau kasa ɗaga kai ta yi ta kalle su. Mommy ce ma ke ta kallonta tun shigowarsu ganin yanda duk ta rame tamkar ba ita ba.
  Abba kuwa kallo ɗaya ya yi mata bai sake marmarin ƙara kallonta ba don kar zuciyarsa ta karaya kan abunda yake shirin aiwatarwa a gareta.

Bayan an gaggaisa ne Ammi ta soma magana
"Alhamdulillahi, na ji daɗi sosai yau ga Afnan ga iyayenta, muna fatar komai zai zo cikin sauƙi kamar yanda Allah ya kawo sauƙin rashin  shigar ta wata muguwar rayuwa kan kuskure ɗaya tak da tsautsaye da ƙaddara suka wanzar"  ta faɗa tana kallon Daddy da ya sunkuyar da kansa ƙasa.

Murmushi ya yi tare ɗago kansa yana cewa.
"Ban san da wane baki zan yi muku godiya ba kan halaccin da kuka yi min na riƙa min Afnan  hannunku ba tare da duniya sun san halin da nake ciki ba.  Tabbas ba don ku ba da ban san yanda rayuwa zata kasance ba. Da ba don ku ba da ban san inda Afnan za ta tsinci kanta ba saboda kuskuren da na aikata na korarta daga gidana.
Haƙiƙa waɗan nan yaran kun cencenci yabo da godiya mai yawa a gurina" ya faɗa yana nuna Yazeed da Yaseer.

"Duk abinda ta yi muku ku ka iya daurewa har  ku ka taimaketa Allah ya saka maku da mafificin alkhairi"

Su dukan su suka karɓa da Amin.

Cigaba Abba ya yi da magana. "Mutunci ne kam Afnan ta riga ta  zubar mana da shi, don haka bana fatan wani abu makamanci haka ya sake faruwa har a kai ga dauko abun kunyan da Allah ya tsare ba a dauko ba"

Juyawa ya yi. Ya kalle Afnan da tunda aka fara magana take shafar kwalla. Cikin kakkausar murya, ya ce
"Afnan dawo nan" ya nuna mata ƙasa gurin ƙafafuwansa.

Jikin Afnan nan take ya ƙara daukar mazari saboda ganin take yi tamkar dukanta Abba zai yi saboda yanda ya kira ta da yanayin fuskarsa.
Haɗa idanuwa suka yi da Ammi. Ta ɗaga mata kai  alamar ta je.

Miƙewa ta yi tamkar zata faɗi ƙasa saboda tsoron da take ji. Gurinsa ta isa tare da gurfanawa a gabansa kanta a ƙasa ta kasa kallon fuskarsa.

Maida kallonsa Abba ya yi  gurinsu Yaseer  yana cewa. "Ina so dukan ku nan ku zama shaida a gareni na matsayinku na waɗan da suka taimakawa Afnan  yanzu kun zama tamkar yan uwanta ne, dan haka na ce ku zama shaidata"  ya faɗa cikin wani ɗaci da ya taso masa a makogaro

Idanuwansa sun yi ja tare da tara wata ƙwalla mai ciyo a ƙasan zuciya.
"Afnan, Afnan, Afnan "
Ya kirata har sau uku.
Kasa amsawa ta yi ta zubawa sarautar Allah  ido.

"Afnan! Na baki daga yau zuwa wani sati, ki fitar min da mijin da zan ɗaura miki aure da shi.  Kuma wallahi wallahi ba kya bina bashin rantsuwa idan baki kawo ba zan haɗaki da duk wanda raina ke so koda kuwa maigadi ne"

Tashin hankali ne Afnan ra riske kanta a cikinsa mai matuƙar girma da  zafi a ƙahon zuci.
Kuka take yi sosai da dukkanin iyawarta tana rokon Mahaifinta.

"Dan Allah abba ka yi hakuri, ka yafe min. Wallahi Abba na tuba dan Allah kamin duk hukunci da zaka yi min amma banda wannan. Abba ban san ya zan yi da rayuwata dan Allah ka sassauta min"
Ta faɗa tana mai dafe da dukkanin ƙafafunsa ta ɗora goshinta a kai tana kuka.

Tsawa ya daka mata tare da bangazar da ita ta faɗi a gefensa. "Wallahi wannan karon  ba zan taɓa yafe miki ba matukar baki bi umurnina ba" ya faɗa yana mai kauda kansa gefe dan ƙauracewa ƙwayar idanuwanta

Dafe kai Afnan ta yi ta nufe Mommy tana faɗin.
"Nashiga uku, Mommy dan Allah ki ce wani abu ki na jin abunda Abbana yake faɗa Mommy ban shirya ba dan Allah ki ce ya sassauta min"

Mommy kasa cewa komai ta yi sai hawayen da ke fita a idanuwanta. Tausayin Afnan ya kamata ta ko ina a jikinta.  Sai dai ba abunda zata iya yi kan hukuncin da Abba ya zartar mata da shi.

"Kiyi haƙuri Afnan ki bi umurnin mahaifinki. Ba don bai sonki ya yi miki haka sai dai don hakan ne dai dai a gare ki" ta faɗa tana mai jin zafin kalmar daidan da ta fito daga bakinta.

Tsit dakin ya yi. Kowa ya kasa magana ba ka jin sautin komai sai  na kukan Afnan.  Sosai tausayinta  ya kama su na ganin ba ƙoshi ba kwanan yunwa. Ammi kanta hawaye take yi na ganin wannan ɗayen hukunci da kuma gani halin da yarinyar ke ciki.

Yaseer kan shi tausayinta yake ji tare da jin wani irin nauyin laifin da ya aikata a gareta.

Sai dai ƙasan zuciyarsa tunanin yake yi kamar wannan ce damar da zai samu gurin  Afnan ta sauraresa. Ya san yanzu ko ba komai ma dole ne ta saurare shi tunda ba ta da wani saurayi sai shi. Ji yake tamkar ya faɗi cewa yana sonta dan ayita ta ƙare. Sai dai ba zai faɗa ba zai ci gaba da lallabata har ta amince dan karan kanta tun da ya san dole dai shi zata komawan.

Maganar Ammi ce ta dawo dashi daga saƙen da yake yi.

"A gaskiya  Baban Afnan wannan hukunci da ka yankewa  'yata ya muna tsauri.  Amma insha allahu zaka sameta mai cika umurninka. Kamar yanda nake hasashen nagartattun halayenta"

Wani kallo Afnan ta yi wa Ammi don bata san inda zancenta ya dosa ba.

Murmushi Ammi ta yi mata  ta ci gaba da maganarbda take yi.
"Amma Baban Afnan ina neman alfarma ɗaya. Idan dai har ka ɗauke mu  kamar yanda muke tunani to  ka bar min Afnan nan gurina har zuwa lokacin da zaka buƙaci jin wanda ta fidda a matsayin mijin aurenta"

Murmushin jin daɗi Abba ya yi saboda  dama haka nan ya so ya yi dan dai kawai  bai san yanda abun zai kasance ba.
"Ba komai hajiya ai Afnan 'yar ki ce kamar yanda na gaya miki kun riga da kun zamo 'yan uwan mu sai dai in ce Allah ya bar zumunci"

Sosai Ammi ta ji daɗi tana mai hango walwarewar matsalar da ke yawan addabar rayuwarta cikin ƙanƙanen lokaci.

Su Abba basu jima ba suka wuce.

Yaseer ma suna wucewa shima ya wuce dan ya baiwa Afnan damar yin tunanin da ya dace da rayuwarta da tasa.

The game has been just stated.

Ready for the next chappy?

Yazeed ko YaseerHistorias para obsesionarse. Descúbrelo ahora