Babi na ashirin da biyu

568 46 2
                                        


Kwanan Afnan biyu  a assibiti aka sallameta. Cikin kwana biyun nan kuma ko da yaushe sai Yaseer ya je dubata a cewar sa amana ce garesu da Yayanta ya ba su.
Sosai yake so ya keɓe da ita dan su yi magana sai dai sam ya kasa samun damar yin hakan  saboda ko da yaushe suna tare da Ammie.

Shi kuwa Yazeed tun ranar da suka je da mahaifinsa bai sake  komawa gurinta ba, sai dai ya kira Ammi a waya.

Da aka sallameta Direct gidan Ammie   suka wuce kamar yanda Ibrahim ya roƙi alfarma a wurin Ammie.

Gidan Ammie gida ne babba don idan ba sani ka yi ba, ba zaka taɓa cewa gidan mace ɗaya ne ba.

Ɗakin Hafsat Ammi ta kaita kafin a gyara inda zata zauna, kasancewar Hafsat ɗin ma bata nan tana gidan kakaninta na gurin Babanta.

Zuwanta gidan ba zata ce ya mata daɗi ba ko akasin wannan. Saboda ko ba komai tana kewar iyayenta sosai.

Yau ma kwance kawai take duk abun duniya ya yi mata yawa. Kasancewar ko jiya ta kira number Momminta a wayar Ammi amma ba a ɗauka ba.

'Ko a wane irin hali take ciki yanzu?' wata zuciya ta tambaye ta. Miƙewa ta yi da suri ta nufe gurin Ammie.

" Ammi bani aron wayar ki Dan Allah"

Murmushi kawai Ammi ta yi tare da miƙa mata wayar.

Number mommy  ta saka ta sake kira, ringing ɗaya ba a ɗauka ba sai a na biyu ne a ka ɗaga da sallama.

Jin muryar mahaifiyarta ba ƙaramin daɗi ta ji cikin zuciyarta ba. Kasa magana ta yi sai ajiyar zuciya da take saukewa.

Sai da mommy ta yi magana kusan sau biyu sannan ta yi magana.
"Mommina"  kalmar da ta iya faɗa ke nan sai ta  fashe da kuka.

Hankalin mommy ba ƙaramin tashi ya yi ba jin yanda Afnan ke kuka, duk da har zuwa lokacin tana cikin tsananin bakin cikin abunda Afnan ɗin ta aikata na zubar masu da mutunci da ta yi.

Tsaki taja tare da cewa. "Zan kashe wayata idan kuka kika kirani ki yi min"

"No mommy plz kada ki kashe min waya Dan Allah, na tuba NAYI NADAMA kan abunda na aikata Dan Allah mommy Ku gafarta min, ku dawo dani a gabanku dan Allah.

Kasa haƙuri Mommy ta yi kawai ita ma sai ta sanya kuka.

"Ƙarasa mana ita ki ke so ki yi ko?
ta jiyo muryar  Sagir  yana faɗa a cikin tsawa.

D'if!, ta ji an kashe wayar.

Kuka ta fashe da shi tana faɗin.
"Nashiga ukuna ni Afnan"

"Ba ki shiga uku ba Afnan" in ji Ammi da ta ji duk abunda ya faru.

"Ki kwantar da hankalinki Afnan, na riga na ɗaukar miki alƙawarin sada ki da iyayenki ko ta halin ƙaƙa, don haka ki bani daga yau zuwa wani sati insha Allahu everting will be alright"

"Allah ya sa Ammi nagide sosai" ta fad'a tare da ƙanƙame Ammin tana kuka.

  Mommy zaune duk abun duniya ya yi mata yawa. Ta yi kuka har ta godewa ubangiji. Kewar ɗiyata take yi sosai duk da cewa Ibrahim ya gaya mata inda ta ke amma sam hankalinta bai kwanta ba ganin tana kusa da su ma tsautsayi ya gitta ina da bata tare da su?.

Sallama Abba ya yi amma ba ta ma san yana yi ba sai da ya yi kusan sau biyu sannan ta ji. firgit ta amsa masa tana maida kwalar da ta zubo mata.

"Kuka ki ke har yanzu ko Zaiba" ya faɗa yana mai tsura mata idanuwansa.

Wannan karon kam ba ta jin zata iya ɓoye damuwarta. Ta fi so ayi duk wacce za ayi dan ba zata yarda abinda ke faruwa da wasu matan kan ƙaddara kwaya ɗaya ya faru da tata ɗiyar.
Cikin  Muryar kuka ta ce.
"Saboda me ba zan yi kuka ba? Dan Allah yanzu abunda ka yi har a cikin zuciyarka kana tunanin ka kyauta? Shin ko kana ganin korar da ka yi ma Afnan Allah ba zai tambaye ka ba ne? Yanzu idan ta shiga duniya kana ganin zaka iya goge abun kunyar da kake tunanin ta janyo maka? Me yesa ba zaka yi ma Ƙaddararta adalci ba ne? Kuskure ne  kai ma fa ka yi shi a matsayinka na uba. Tun farko  kai ka tauye mata hakkinta ka fifita boko kan aure. Ka takura mata ka sanya mata takunkumi da yawa.
Dan Allah Alhaji ina rokon ka da ka yi gaggawar maido min da yarinyata hannuna tun kafin ABUNDA AKE GUDU ya faru. Saboda yanzu ba abinda ya faru dan har yanzu ba kowa ya san da abunda ya faru da ita ba. Dan ta ciki ne Allah ya dube mu da idon rahama ya ɓarar da cikin. Me kake gudu yanzu kuma?" Ta tambaya tana kafesa da idanuwanta da ke zubar da hawaye.

Duk dauriya irin ta ɗa namiji sai da Abba ya yi kwalla jin kalaman Mommy tabbas ya san gaskiya ta gaya masa sai dai aikin gama ya riga ya gama. Ba garin  Allah da zai waye ba tare da ya tuna baƙin cikin da Afnan ta cusa mishi a zuciya ba.
Ya yi danasanin tsaurin da ya yi mata babu iyaka. Duk lokacin da ya tuna ranar da aka ce tana ɗauke da juna biyu sai ya ji tamkar a ce mafalki yake yi. Farin cikin shi ɗaya cikin da ke jikinta da ya zube.
wannan ka ɗai yake tunawa ya ɗan ji sanyi cikin ransa. Mutunci kuma  ta riga ta sayar a titi. Sai dai fatan Allah ya ƙara rufa masu asiri.

Rungume mommy ya yi tare da cewa. "Ya isa hakanan daina kukan, na san ni kaina ina da laifi kan abunda ya same Afnan sai dai fushin zuciya ne yasa na yi mata hakanan da ta faɗi gaskiyar lamarinta.
kar ki damu mun yi magana da mariƙiyarta Maman Yazeed ɗin.

Ta kirani Ya fi a kira tana min wa'azi da nasifa kan rayuwar Afnan, kuma tabbas abunda ta faɗa gaskiya ne, insha Allahu zamu je zuwa jibi gurinta. Afnan za ta dawo gida muddun ta cika SHARADINA ɗaya tak da zan ginɗaya mata"

Da sauri Mommy ta ɗago ta kalle shi. "Wane sharaɗi kuma Alhaji?"

Murmushi ya yi iya leɓe. "Calm down I won't repeat that mistake again, na san shi kike tunani. Za ki ji ko ma miye idan mun je.

Daɗi sosai Mommy ta jiya,  at list dai ta samu peace of mind kuma ta san duk wani sharaɗi da zai ginɗaya ma ta mai amfaninta ne don ta san ba zai kuskura a sake maimaita ƴar gidan jiya ba.

Yazeed ko YaseerStories to obsess over. Discover now