Babi na arba'in da tara

674 58 3
                                        


Tun kafin ta kammala karantawa ta fara zubar da hawaye  masu matuƙar  ɗaci da bada wahala ƙasan zuciya.

Bayanta Yazeed ya dawo ya rungumeta yana bubbuga bayanta alamar lallashi.

"Me yasa Yaseer zai yi min haka? Me yasa zai neme ya zubar min da ɗan sauran mutuncina da ya rage a idon duniya? 
Shin duk abunda ya yi min na keta min haddi bai ganiba sai ya neme ya rabani da wanda ya ƙauna ce ni a yanda nake, ya kuma rufamin asiri,  ya rufe mugun aikin da na aikata a idon duniya? Haƙiƙa da ba don kai da Ammie ba da yanzu ban san yanda rayuwata zata kasance ba, da yanzu shi kansa bai kusanto ni ba. Da guduna zai riƙa yi, ya nunawa duniya  tamkar bai taɓa tozali da irin halittata ba. Ina ji a raina ba zan taɓa yafewa Yaseer ba har abadar abada."   Ta  ƙarashe maganarta tana mai fashewa da wani matsananci kunka mai ban tausayi. Tabbasa kowa aka nunawa abunda ke cikin wayar zai yarda zai amince ganin an yi amfani da numbers har na ƙasashen waje wurin turo saƙon.

Kukanta da take yi yake ji har cikin ranshi. Sosai kukan ke taɓa shi yana kuma ƙara haddasa mishi ƙiyayyar Yaseer mai zafi a cikin zuciya. Sai yanzu da yake jin kukanta abunda Yaseer ya aikata masu ke ƙara ƙona mishi rai. Sai yanzu yake jin haushin kansa na rashin illatashi da bai yi ba ya barshi gurin police.

Wasu sirarran hawaye ne suka zubo daga idanuwanshi.

Ɗumin hawayenshi da ta ji a bayanta ne ya ƙara ɗaga mata hankali tare da dagula mata lissafi. Tsagaita kukanta ta yi tare da juyowa tana fuskantarshi.

Buɗe idanuwanshi ya yi yana kallonta kafin ya jata zuwa gado ya kwantar da ita kan cinyarshi yana shafe mata hawayen fuskarta.

"Ya aka yi ka sani Ya Yazeed" ta faɗa muryarta can ciki.

Duk da yanda yake jin ciyon ka,  bai hana ya kwashe duk wani makircin da suka ji su Yaseer suna Faɗa ba ya gaya mata.

Afnan kasa cewa komai ta yi sai ajiyar zuciya da take saukewa. Cikin ranta kuwa jin jina girman makirci take irin na waɗan nan bil adaman.

Sun ɗauki lokaci tana kwance ta yi matashin kai da cinyarshi yayin da shi kuma ya rankwabo ya ɗora kanshi a kirjinta yana jin bugun zuciyarta.

Sosai suke jin daɗin yanayin nasu sabida ba wanda ya sake magana cikinsu sai sauraren bugun zuciyoyin junansu da saukar nunfashinsu kawai da suke yi.

Boɗe kofa, da sallamar da Ammie ta yi ne, ya dawo da su daga duniyar da suka tafi. Cikin sauri Afnan ta yunƙura zata tashi  Yazeed ya ƙara riƙeta sosai cikin jikin jikinsa.

  Jinta take yi tamkar ta nutse cikin ƙasa don kunyar Ammie.

Shi kuwa Yazeed ko a jikinshi dan dama haka yake so dan kar Ammie ta kawo masa wani kauli da ba'adi game da matarsa dan yaga ba alamar sauƙi a tare da ita.

Murmushi ne ɗauke da fuskarshi yana kallon Ammie da ta yi galala tana kallonsu.

Cikin jin kunya Afnan ta zame jikinta tare da  tsunkulesa a cinya. Yar ƙara ya yi kaɗan tare da sakinta, ta dukar da kanta ƙasa tana gaida Ammie.

Amsawa Ammie ta yi tare da matsowa tana kallon Yazeed. Bakinta ɗauke da mamaki ta ce.
"Kai marasa kunya me kake yi a nan? Bama shi ba wai  ya ma aka yi ka shigo min  gida dan ga dukkan alamu ma nan ka kwana?"

Zaune ya miƙe yana sosa ƙeya
"Ammie ɗakina ne fah, kuma matata tana cik, ita ta buɗe min ƙofa na shigo"
ya bata amsa yana kallon Afnan da har fuskarta ta fara jaa saboda kunya.

Taɓe baki ta yi. "Kar ka ci Amanar Afnan, ka san dai yanda aka yi ka shigo. Da kuma da kake cewa ɗakinka. Yanzu wannan ya tashi daga ɗakinka, ɗakinka yana can gidanku ka baro. Nan dama aro na baka kuma yanzu na karɓe kayana don haka sai a tattara a koma inda aka fito ba mu buƙar ka anan"

Bai sake cewa komai ba sai ƴar dariyar da yake yi ƙasa ƙasa saboda ya gane inda Ammie ta dosa.

Riƙe hannayenta ya yi "Ammie hankuri fa na zo na baku ke da ƴarki"

Dama tun shigowarsa jiya da dare ta gansa. Kuma har biyoshi ta yi ganin yanda ya shigo gidan ɗaukarta ko wani abu zai yiwa Afnan ɗin. Amma ganin ba abunda take tsammani ba ne yasa ta bar jikin ƙofar ta wuce tana mamakin abunda ya chanja ra'ayinsa da tsakar daren.

"Please Ammie hear me out mana" ya faɗa cikin marairaicewa.

"Bana buƙatar jin komai haƙuri kuma ka riƙe kayanka ba ma buƙata. Ka san dama na gaya maka  ba a saurin yanke hukunci kan abunda ba a yi bincike kansa ba, amma sam kai ka ƙi ji har saida ka sanya ɗiyar mutane cikin tashin hankali"

"Na san ban yi dai dai ba Ammie. Amma ki tsaya ki ji dalilin da yasa na yi haka pls" ya sake faɗa cikin magiya.

Hararanshi ta yi tare da zaunawa kan stool. "Ina saurarenka."

Bai rage komai ba ya fayyace mata duk abunda ya faru tare da nuna mata sakwanni wayar Afnan ɗin.

Jikin Ammie ya yi  sanyi sosai. Saboda Ba ta taɓa tunanin abun har ya kai haka ba.
Kasa cewa komai ta yi sai kawai tace su fito su karya.

Fita ta yi tanata jimamen abunda ya faru. Lallai MUTUM MUGUN ICCE ne ta faɗa a ranta tana mai Allah wadai da hali irin na su Yaseer.

Sai da suka sake yin wanka sannan suka shirya suka fito gurin breakfast ɗin.

Suna cikin karyawar Daddy ya kira Yazeed don zuwa police station. Sai da ya kammala sanna ya yi musu sallama ya tafi.

Ko da suka isa idonsu Mamie tune ya raina fata, saboda yanayin cell ɗin.

Daddy bai yi wata wata ba ya fidda takardar saki biyu ya bata yana mai Allah waddai da hakinta.

Kuka Mamie ta riƙa yi harda su majinnu tana roƙon Daddy da ya maidata ɗakinta ta yi masa alƙawarin  ba zata sake zaluntarshi ba, sabida zuwa lokacin ta riga ta fahimce cewa duk maganar da suka yi a kunnesu Daddy suka yi ta.

Daddy bai saurare su ba yasa aka rubuta takarda dan su saka hannu cewa komai ya same ɗaya daga cikin iyalinsa daga yanzu har zuwa wani lokaci su ne.

Sai da suka saka hannu sannan aka sake su. Daddy ya ce kar ya ga ƙafar ko wannensu a gidanshi zai sanya a kwashe musu kayansu a kaimusu.

Mamie har da suma ta yi saboda tsananin tashin hankalin da take ciki na ganin ta rasa tsuntsu ta rasa tarko.

Yaseer kuwa yana saka hannu a takardar ya fita officien yan sandar ba tare da kowa ya kura da shi ba. A wannan lokacin zuciyarsa ɗauke take da wani irin ƙuduri mai girman gaske sabida sam shi bai ga ta yanda za a yi ya iya haƙura da Afnan ba duk da irin wahalar da ya sha kanta.

Yana kaiwa bakin titi zai tsallaka wata mota marasa hankali da birki ya ƙwacewa tana neman tsaya da duk abun da ƙaddara ta saukarwa ta yi sama da shi ta juyashi sararin samaniya kafin ta wulgar da shi wani gefe daban na kan titi in da ita kuma ta samu wani chabe kusa da inda halittarsa ke yashe ya tsayar da ita.

Kokowa yake da dukkan nunfashinsa yana neman iskar da zai shaƙa ya fesar. Wani irin nauyi da raɗaɗi ne suka ziyarcesa lokacin da yake ƙokarin ɗaga hannu da dukkan jikinsa. Wani abu mai nauyi ya hayesa ya kasa ko da ƙwaƙwaran motsi ne.

Idanuwansa a hankali suka fara rufewa kan mutanen da suka fara taruwa kansa dan bashi taimakon da ya dace. Cikin ƙanƙanen lokaci komai nasa ya daina aiki sai kaɗan daga cikin zuciyarsa dake halbawa alamun ya suma amma yana nan da rayuwarsa.

Yazeed ko YaseerStories to obsess over. Discover now