"Yusuf" ta furta fuskarta ɗauke da wani farin ciki mai yawa.Murmushi ya yi tere da cewa,
"Manyan gari kwana biyu kin ɓata ɓat""Hmm! Ya Abokinka da jiki?" Ta faɗa tana maida dukkan hankalinta zuwa garesa.
Murmushin yaƙe ya yi. "Alhamdulillahi he's getting better, amma fah fushi ya ke yi da ke."
Fuskarta ɗauke da mamaki ta kallesa "fushi fah kace? Da na yi masa me?"
"Ni ba za a ji mutuwar sarki a bakina ba. Amm dai gaskiya ni Afnan kin ban mamaki sosai.
Yanzu a ce duk rashin lafiyar da Yazeed ya yi ki kasa zuwa ki dube sa ko sau ɗaya duk irin soyayyar da kuke nunawa junanku?. Ko yaushe cikin maganarki yake. Mamie ma ta yi mamakin da ba wani naki da ya je dubawa duk maganar auren da ke nema ta shiga tsakaninku."Jin maganar da ya yi ne yasa hankalinta ya sake tashi. "Kar dai ka ce min har yanzu yana assibitin?" ta faɗa hawaye na zubowa a idanuwanta.
"Eh yana can har yanzu Amma dai yau ko gobe ake sa ran za su sallamesa"
Idanuwanta ta goge tare da cewa. "Allah ni ban san ma bashida lafiya ba sai jiya da Abbana ya gaya min. Saboda ko na kira wayarsa ba ta zuwa ban san dalili ba"
"Gaskiya ne. Ko an kirasa ba a samunsa. Ko Abbanki ma ai da wayar mahaifinsa ya kirasa dan kar ya ɗauka ba da gaske yake yi ba"
Ɗan murmushi ta yi tare da cewa.
"To me yasa wayarsa bata shiga? Kuma me yasa bai gaya min bashida lafiya ba" Ta sake jefa masa tambayoyin nan."Wannan kuma shi kaɗai zai iya baki Amsa. Ni dai kawai shawarar da zan baki ki je ki dubasa kafin a sallamesa ko keda ƙawarki ne sai in ajiye ku ko ina gaya maku sunan assibitin sai ku je. Na tabbatar da ba ƙaramin daɗi zai ji ba idan kika yi masa tafiyar ba zata"
Tunawa da ta yi, ya taɓa gaya mata yana son a yi supriase ɗin da ne yasa ta ji ya kamata ma ta yi masa ko dan irin kewarsa da zuciyarta ke yi.
"Wane asibiti ne aka kwantar da shi?" Ta ce tana kallonsa.
"Ecowa"
"Gaskiya ban san inda assibitin take ba kuma gashi Safiyya ta wuce gida" cewa da ƙwarya course mate ɗinta.
Idan ba damuwa ki zo kawai sai in ajiye ki, dama can zan je daga nan.
Ganin wannan ce kaɗai damar da gareta da za ta iya zuwa duba sa ya sanya bata kawowa ranta komai ba ta amince. Dama shigarta ba laifi zata iya shiga da ita ko ina duk da cewa hijab ne a jikinta.
Ba su wani ɓata lokaci ba suka isa assibitin. Saidai suna isa tun nan reception aka shaida ma su an sallamesa tun ɗazu.
Haka suka fito jikin Afnan duk ya yi sanyi gskiya tana son ganin Yazeed a yau ko ta ƙaƙa dan ganin take ma kaman idan bata gansa ba zata iya zaucewa. Saboda zuciyarta ta cike take da kewarsa.
Kallonta Yusuf ya yi kaman ya karance abunda ke cikin ranta yakamata gaskiya ki je gidansu ki dubasa tunda kin yi niya"
Duk da cewa wata zuciya na so ta je sosai bai hanata cewa "A'a gaskiya ba zan je gidansu ba, idan na je ma me zance? Dama Safiya tana nan da abun zai fi sauƙi"
Murmushi ya yi. "Na san damuwarki duk ba zai wuce Mamie ba ko? To ki kwantar da hankalinki dan ba za ki isketa ba. Sai dai ƙannesa kaɗai zaki taras. Su Nusaiba ai nasan kin sansu ko?"
"Eh" kawai ta ce saboda sosai yake bata waya su gaisa da Nusaibar. Haka kuma tana ganin pictures ɗinta tare da shi ko ita kaɗai a wayarsa.
Ba dan ta amince ɗari bisa ɗari zata je ba. Sai dai yanda Yusuf ya riƙa azata yana fasa mata kai da bata labarin irin son da Yazeed ke mata yasa ta ji dole ma ne sai ta je ta dubosa ko don kar Yusuf ya yi masa dariya, dan ta lura da take takensa.
![](https://img.wattpad.com/cover/95453973-288-k589738.jpg)