Babi na ashirin da uku

548 43 1
                                        


Yau ta kasance assabar da misalin karfe uku na yamma.
Afnan na zaune falo tana kallo sai dai a zahiri ne zaka ga tamkar kallon take yi amma cikin zuciyarta abubuwan duniya ne suka taru suka yi mata yawa, dan ko kallon yi ne kawai take ba tare da tana fahimtar abunda ake yi ba.

Sallama ya yi ya shigo falon, tunda ya ganta ita kaɗai ya ji wani irin sanyi ya mamaye mishi zuciya da gangar jiki.  Dama yau ya zo ne ayita ta ƙare saboda sam ya kasa sukuni da sabuwar ƙauanarta da ta addabi ruhinsa.

Sai da ya tsaya ya ƙare mata kallo tsaf, sannan ya ƙarasa gurinta. Durƙusawa ya yi gabanta, tare da hura mata iskan bakinsa a idanuwanta. Sai da ta ɗan firgita lokacin da ta dawo cikin  hayyacinta.

"Me ye haka" Ta fada cikin tsiwa tana zuba masa manyan idanuwanta da suka zame masa ababen soyuwa a mafalkinsa.

Bai razana da kallon da take masa ba ya yi murmushi tare da furta.
"Ya kamat ki maida wukar Afnan I mean no harm. Na zo ne kawai in ƙara neman gafararki kan abubuwan da suka faru.  kuma ina so in ƙara jadda da godiyata a gare ki  kan rufa min asirin da ki ka yi a assibiti alhalin kina da damar da zaki tona min asiri. Afnan ki sani duk abubuwan da suka faru ƙaddarori ne waɗanda shaiɗan ya ba da gudunmuwa sosai a cikin faruwar su. Yanzu ina mai tabbatar maki cewa a shirye nake da in aure ki idan har kin Amince. Sa........!"

Uwar tsawar da ta daka mishi ne ya sanya maganar tashi ta katse ba tare da ya san da hakan ba.
Wata irin dariya ta yi mai cike da duhun baƙin ciki da ɓacin rai masu matuƙar girma a gareta.
"lallai Yaseer sai yau na tabbatar da kai ɗan akuya ne marar kunya. Kai banda ma jakkanci da rashin sanin ciyon kai har kana da bakin da zaka zo min da wannan magana?
Toh bari ka ji in gaya maka abunda baka sani ba. Wallahi tallahi na tsaneka Yaseer,  na yi baƙin ciki da nadamar sanin ka a rayuwata. Duk lokacin da na gan ka ina ji ne tamkar naga baƙin maciji. Da in aure ka wallahi ƙara in aure kare" ta faɗa tana mai tuna lokacin da take masa magiya tana haɗa sa da Allah dan kar ya keta mata haddi.

Wani irin ɓacin rai da zafin kalamanta na ƙarshe suka taso masa. Idanuwansa nan take suka chanja kala suka koma jajur. Zai iya jure komai amma ba zai iya jure jin komai amma ba zai iya jurar jin kalamanta na ƙarshe a garesa ba.
Cikin izza ya ce.
"Ƙarya ki ke yi wallahi Afnan na san har yanzu kina sona. Idan kuma ba kya sona me yasa kika rufa min asiri a assibiti bayan kina da damar faɗin abinda ya faru? Afnan ki yi haƙuri mu rufawa kanmu asiri na san kina so na ɓacin rai ne yasa kika gaya min abun da kika gaya min a yanzu. Ki yi tunani   Afnan kin san duk duniyar nan ni ne  kaɗai zan iya rufa miki asiri. Dan Allah ki yi haƙuri kada ki ce ba zaki aure ni ba" ya ƙarasa  maganarsa cikin rauni tare da haɗa hannayensa biyu a guri ɗaya alamar roƙo.

Wani mugun murmushi ne ya kafcewa Afnan wanda sam bai yi kama da na farin ciki ba ko na jin daɗi.
"Da wannan ka dogara Yaseer?" Ta faɗa tana mai lashe leɓenta na ƙasa da ya bushe kafin ta ci gaba da magana.
"Ya kamata  in gaya maka abunda ba ka sani ba Yaseer. Rufama  asirin da na yi a assibiti ba komai ba ne face tonuwar asirinka.  Wallahi wallahi Yaseer yadda ka tozartani ka keta min mutuncina ta ƙarfin tsiya to ka sani nima sai na yi ma abunda ya fi haka. sai na dasa maka ciyon da har ka mutu ba zaka taɓa mantawa  da shi ba" Ta faɗa tana mai sake nuna kanta ta ce.
  "Ni Afnan sai na FANSHE BUDURCINA da ka yaga ta ƙarfin tsiya ko da kuwa hakan ne zai zame min silar baƙin cikina "

Sosai kalamanta suka kashe masa jiki suka sanya sa ya yi mutuwar zaunen da ba amsar ransa aka yi ba.
Gangar jikinsa ta amshe kalamanta yayin da zuciyarsa ta kasa gasganta kalma ko ɗaya da ta furta da bakinta. Ji yake tamkar ta faɗa ne kawai dan ɓacin rai amma  ba zata iya aiwatar da komai ba, duba da irin son da take yi masa wanda a nashi ƙaramin tunanin yake ganin tamkar yana iya ganinsa a ƙwayar idaniyarta.
Wani malalacin  murmushi ya saki tare da jiƙa leɓensa da harshensa.
Babban yatsansa ya ɗaga mata alamar jinjinawa a gareta  kafin ya koma kan kujera ya zauna ya fuskance ta.

Sallamar Yazeed ce ta sa ya fasa fadar maganar da zai faɗa sai kawai ya karkata hankalinsa ga tv yana kallo.

Gudun kar Yazeed ya fahimce wani Abu yasa Afnan ta karƙaro murmushi ta ɗorawa fuskarta tare da furta "ina wuni Ya Yazeed"

Ko a ina ya zama yayanta?  ya faɗa cikin zuciya yana taɓa baki tare da amsa mata gaisuwarta da "lfy"
Bai wani  kallesu ba saboda ya gano take taken Yaseer tun a assibiti kamar yana son yarinyar.

"Ammie fah?" Ya tambaya.

"Tana sama"  Amfan ta bashi amsa tana satar kallon Yaseer da zaka iya rantsewa bai ma san da zamanta a  gurin ba saboda yanda ya baiwa tv dukkanin attention ɗinsa.

'munafuki, zaka gane kurenka' a fada cikin ranta. Lokacin da Yazeed ya wuce sashen Ammie.

Cikin mintunan da basu wuce biyu ba sai ga Yazeed da Ammi suna saukowa daga sama. Ammie na cewa,
"Ayi haka kai ko? Me yasa baka shigo da su ba? ai yanzu sun zama ƴan gida kuma"

Kira ta kwalawa Afnan da ta kusa shigewa kitchen.

"Dakata Afnan. Zo ki zauna ga baƙi nan munyi bari ku gaisa barwa Salame aikin kawai"

Haka kawai Afnan sai ta tsinci gabanta da faɗuwa.  Da sauri ta juwo tana murmushin yaƙe. Tace "dama ai mun kammala tun ɗazu salamen ma ta wuce kina bacci"

"Kun yi ƙoƙarin kam" ta faɗa tana mai juya gurin Yaseer da ke gaidata.

"Dama tare kake da su Yazeed ɗin shi ne bai gaya min ba?" Ta faɗa tana kallon Afnan da ta yi wuƙi wuƙi alamar rashin gaskiya.

Yaseer Ya ce. "A'a Ammie ba tare muke ba, nima dai yanzu nan na shigo aka ce kina sama"

"Allah sarki, ai da sai ka wuce saman" ta faɗa tana gyara mayafin kanta da ya zame.

Kafin ya sake magana  aka yi sallama aka shigo.

Abba ne da Mommy da kuma Ibrahim sai Yazeed da ke gaba ya  musu jagora.

Maraba maraba Ammi keta faɗi tana nuna musu gurin zama. Afnan kan  tsaye ta yi kamar an shukata don jikinta baki ɗaya daukar mazari ya yi. Shin mafalki ta ke yi ko da gaske ne Abbanta take gani da Momminta.?

Yazeed ko YaseerStories to obsess over. Discover now