Babi na talatin da tara

569 49 3
                                        

 

Ranar Asabar aka yi waleema da Yamma da dare kuma aka kai amarya ɗakin mijinta.

Part ɗinta ya sha gyara sosai. Ɗakunanta an zuba mata kaya na ji da faɗa abun sai wanda ya gani.

Bayan ƴan kai Amarya sun watse akabarta ita kaɗai sai walili take da idanuwa tana jin ta cikin wata sabuwar duniya ta daban.

yanayin da ta samu kanta ciki yanayi ne da ba zata iya taɓa misiltashi ba saboda yanda take jin faɗuwar gabanta na tsananta mata da dukkan motsi na wani abun halitta, a ciki kuwa harda a.c da labulayyan ɗakin.

  Tana nan zaune cikin wannan yanayin ne ta ji an turo ƙofa an shigo haɗe da yin sallama.

Yanda ta ji sautin muryarshi ne ya sake jefa zuciyarta cikin wani ruɗani mai tattare da zuwan wani baƙon lamari a ƙasan zuciyarta.

Dafe kirjinta ta yi dake mata barazanar fitowa. jikinta har wani cira yake yi. Nan take wani irin tsoro ya dabaibaye dukkan sassa na jikinta.

A hankali ya ƙaraso cikin ɗakin fuskarshi cike da haske da wani annuri mai ƙayatarwa.

Gefen gado ya zauna kusa da ita yana mai zuba mata idanuwa tare da yiwa Allah godiya da ya mallaka masa ita ba tare da ƙarfinsa ko dabararsa ba.

Hannunshi ya saka ya yaye lulluɓinta tare da tallabo fuskarta duka da tafin hannayensa.

Runtse idanuwanta ta yi  gam, sai hawayen da ke ta ambaliyar fitowa tamkar saukar ruwan sama.

"Ya rabb." Ya furta tare da sanya manyan yatsunshi guda biyu yana shafe mata hawayenta.

"Kukan ya isa haka Afnan. Yau ba ranar kuka ba ce, yau ranar farin ciki ce, bai dace kina ɓarnata hawayenki inda ba a buƙatarsu ba"

Maganar tashi maimakon ta kwantar mata da hankali sai ta sake ɗaga mata hankali sosai saboda wannan karon jikinta har kyarma yake yi.

Idanuwa Yazeed ya zuba mata ganin yanda jikinta ke yi. ajiyar zuciya ya sauke  cikin sanyin murya ya ce.

"Wannan rawar jikin kuma fah na miye?
Afnan ke fa ba yarinya ba ce ba. Ya kamata ki nutsu ki kwantar da hankalinki, sanin kanki ne ni ba zan taɓa cutar dake ba.

Nasan abunda kike jiwa tsoro. Afnan kada ma ki kawo wannan a rayuwarki saboda ni a wurina na daɗe da binne wannan shafin a ratuwata.

Nasan ƙaddara ce abunda ya faru dake, wadda ni da ke da duk wani mai ƙaunar ki bai isa ya yi komai a kai ba. Dan haka ki kwantar da hankalinki ni ke nake so ba jikinki ba.

So idan ma tunanin da kike kenan na yanda zan sameki to ki ajiye wannan a gefe nasan yanda kike na aureki. Kuma a hakanan nake son ki.

Yanzu ki tashi kije ki watsa ruwa ki doro alwala mu yi sallah dan mu  nuna godiyarmu ga Allah. Nima zan je ɗaki na watsa ruwa sai nayi alwalar kin ji?"

Gyaɗa masa kai kawai ta yi.

Yana fita ta maida wata wawuyar ajiyar zuciya. Magangannun da ya yi mata suka shiga dawo mata a kai. Tausayinshi ta ji ya kamata sosai. Wato shi duk ɗaukarsa tsoro take ji na yanda zai sameta ba budurwa ba.

Ita sam ba wannan ne a gabanta ba, duk da cewa wannan ɗin ma ta daɗe tana tunanishi a ranta, kuma har lokacin da  ta shigo gidansa tana jin ba daɗi a rayuwarta na kasancewarta wadda batada budurci, sai dai, lokaci ɗaya wani baƙon al'amari  wanda bata taɓa kawosa a zuciyarta game da rana irin ta yau ya auku.

Lokaci ɗaya abunda take ji ya zarce duk wata fargaba da ta shigo da ita a gidan. Saboda a halin da take ciki ji take yi idan Yazeed ya kusanceta zata iya rasa rayuwarta  saboda tsabar tsoron abun da take ji a zyciyarta.

Yazeed ko YaseerLa tua prossima ossessione. Scoprilo ora