Babi na arba'in da takwas

592 48 5
                                    


A hankali ya buɗa ƙofar ɗakin ya shiga. Can ya hango ta kan gado naɗe cikin bargo, da ganin yanda take kwance ka san akwai abunda yake  damunta ganin yanda duk ta takure kanta guri ɗaya.

Cikin sauri ya isa inda take, ya gurfana saitin fuskarta tare da yaye bargon da take ciki yana kiran sunanta a hankali.

Ɗaga idanuwanta da suke mata nauyi da zafi ta yi, ta buɗe su tar kan kyakkyawar fuskarsa.

Kasa janye idanuwanta ta yi daga gare sa, saboda ba ta son ta falka daga  mafalkin da take, da zata dawwama a haka har abada tana kallon fuskarshi ada ba za ta damu ba saboda ba ta hange kallon tsanar da yake yi mata a idanuwanshi ba sai tsantsar kaunarta da ta gani kwance a ƙwayar idanuwansa.
Waɗannan idanuwan sune nata, sune na Yazeed ɗinta ba waɗan can da ta gani ɗazu ba.

"Wannan shine Yazeed ɗina."Ta faɗa a hankali tare da runtse idanuwanta tana mai fatar idan ta buɗesu ta sake yi tozali da shi a gabanta.

"Ni ne Yazeed ɗinki Afnan ni ne." ya faɗa yana mai haɗe hannayinshi duka biyu a guri ɗaya alamar roƙo.
"Ban san ta inda zan fara ba. Afnan ban san ta inda zan fara neman gafarar ki ba"

Sai dai ya ja iska ya fesar sannan ya ci gaba da magana.

"It was really hurt, really really hurt for hurting you Afnan. But ki sani, son ki bai taɓa raguwa a zuciyata ba ko da na misƙala zarratin ne.

Ki hukunta ni Afnan. Ki hukunta ni ta ko wace hanya da kika ganin ta dace da ni, amma pls ka da ki hukuntani ta hanyar da na hukuntar dake da ita. Wallahi idan kika yi min irin hukuncin da na yi maki na nisanta kanki daga gare ni mutuwa zan yi Afnan"

Wani abu take jin yana mata yawa a jiki sai lokacin ta tabbatar da ba mafalki take yi ba shi ɗin dai ne Mutumin da zuciyart ke ɗawainiya da son sa, da zullumin mafi munin laifin da ta aikata a garesa.

Magangannunsa ko ɗaya ba ta gane ba, ita abunda ta gane ta kuma fahimta kawai yau shine a gabanta,  shine wanda zuciyarta ke bugawa da sonsa da ƙaunarsa a ko wace daƙiƙa ta rayuwarta.

Bata san ya aka yi ba, sai ganinta ƙasa kawai ta yi  itama saman ƙafafuwanta ta harɗe hannayenta kamar yanda ya yi, sai dai kasa furta komai ta yi sai jikinta da ke rawa idanuwanta na fitar da hawaye.

Ganin haka yasa ya yi saurin  janyota zuwa jikinsa ya ƙanƙameta sosai tare da ɗora kansa a wuyanta yana faɗin. "I am sorry Afnan am really sorry"

Wasu sanyayyun hawaye ne suka zuba daga idanuwanta. Ta saka dukkan hannyenta ta zagayesu garesa tana mai jin tamkar su dawwama a haka har abada.

"Don't leave me again Yaa Yazeed dont leave me. I can't do with out u Ya Yazzed I promise i will never hurt your feelings again please  Yaa Yazeed don't......."

Yanda take magana da yanda kuma ya ke jin zafin jikinta na shiga jikinsa, da kuma ɗumin hawayenta da ke zuba a bayansa ne yasa, ya yi saurin ɗagata tare da sanya yatsarshi a bakinta yana girgiza mata kanshi.

"You are sick Afnan. Jikinki ya yi zafi sosai."

Lumshe idanuwanta ta yi tare da jinginar da kanta a gado dan ba ta da kuzarin da zata zauna ba tare da ta jingina ba.

Sake taɓa jikinta ya yi tare da miƙewa  ya tallabeta dukanta ya ɗorata kan gado.

Bathroom ya nufa da sauri sai gashi ɗauke da towel ƙarami da ruwa a ciki. Zama ya yi kusa da ita, ya riƙo hannayenta.
"Pleasels let me help you Afnan. Dan Allah kar ki ce a'a  jikinki ya yi zafi sosai komai zai iya faruwa gashi kuma ba magani a kusa. This is the only thing that can help u now pls"

Sunkuyar da kanta ta yi ƙasa ba tare da ta iya cewa komai ba saboda a halin da take ciki ita kanta tana buƙatar ko wane irin taimako ne.

Tana jin lokacin da ya ɗorata kan cinyarshi ya zuge zip ɗin rigarta. r
Runtse idanuwanta ta yi gam saboda tsananin kunyar da take ji.
Shi kuma ido kawai  ya tsura mata  yana mai yiwa Allah tasbihi da ya mallaka mishi wannan halittar a matsayin tashi.
Towel ɗin ya rik'a tsomawa cikin ruwa yana  shafe mata dukkanin ilahirin jiknta dashi.

cikin ƙanƙanen lokaci ya kammala  tare da kwashe kayan da ya yi amfani da su ya maidasu muhallinsu.

Afnan kam sake tattakewa ta yi cikin bargo sai ta fara kakkarwar sanyi.

Ganin haka yasa Yazeed ya miƙe tare da cire riga jikinsa.  sai da ya rage daga shi sai boxer sannan ya kashe wutar ɗakin ya shiga cikin bargon da Afnan ke ciki ya janyota jikinshi.

Matseta ya yi sosai a jikinshi yanda zai bata damar ta samu ɗimin jikinshi yanda ya kamata. Cikin ƙanƙanen lokaci zufa ya karye mata wani bacci ya kwasheta mai cike da nutsuwa.

Yazeed kam bai runtsa ba har asuba. Sai da ya ji kiran sallah sannan ya iya miƙewa ya shiga bathroom tare da watsa ruwa ya ɗoro alwala. Bai je masallaci ba nan ya yi sallar shi. Yana cikin yin lazima Afnan ta falka, jikinta ya yi sauƙi sosai dan ba zafi sai dai ciyon kan da take ji.

Kallonta ya yi tare ya sakar mata murmushi mai kyau. Ita ma murmushin ta maida mishi tare da miƙewa a hankali ta shiga bathroom.

Koda ta fito har Yazeed ya fara angaje kan sallaya, kasancewar bai samu yin bacci jiya ba.

Tausayinshi ta ji ya kama ta, ta san jiya bai yi bacci ba ganin ɗan motsi kaɗan idan ta yi sai ya yi mata sannu.
Gefenshi ta tsaya tare da  tata sallar.

Bayan ta kammala azkar ɗinta ne ta maida dubanta gurin Yazeed da ya fara bacci tana nazarin fuskarshi.

Idonshi ya buɗe tar cikin nata. Miƙewa ta yi da sauri tana mishi ina kwana, kunya duk ta rufeta ganin yanda ya kamata tana kallonshi.
murmushi ya yi tare da janyota ta faɗo jikinshi.

"Me kike kallo a fuskana?"

Sunne kanta ta yi a kirjinshi. Cikin kunya ta ce. "Ni ba kallonka nake yi ba. Kawai ina mamaki ne"

Ya gane in da ta nufa sai kawai ya ce.
"To ko kallona kike sai me? Ba mijinki kika kalla ba?" ya faɗa yana mai ƙara gyara mata zama cikin riƙonsa.

"Ya jikin? Hope dai ya yi sauƙi?"

Gyaɗa mishi kai kawai ta yi saboda yanda yake wasa da hannunshi a jikinta ba ƙaramin kashe mata jiki ya yi ba.

"Yaa Yazeed!" Ta kirashi cikin wata murya.

Jin yanda ta kira sunanshin ne yasa ya kasa Amsawa, sai kawai ya lumshe idanuwanshi tare da ɗan bubbuga bayanta alamar yana jinta.

Zamewa ta yi daga jikinshi tare da  gurfanawa gefensa kanta na kallon ƙasa ta ce.
"Yaa Yazeed me yasa kake zargin na cu amanarka" ta faɗa muryarta na rawa.

Bai yi zaton jin wannan tambayar ba, duk da yasan dole sai ta tambayeshi, amma sam bai yi tsammanin zata yi mishi ita a wannan lokaci ba.

Miƙewa ya yi zaune yana fuskantar ta da idanuwanshi da suka fara chanja launi, saboda tunowa da abunda ya faru.
"Me yasa kika ɓoyemin gaskiyar lamarinki Afnan? Me yasa baki sanar da ni abunda ke tsakaninki da Yaseer ba?"

'Ta faru ta ƙare' . Ta faɗa cikin ranta. dama tasan wannan ne dalilin da yasa Yazeed ya juya mata baya.
Ko ba shine ba,  tana da niyar ta gaya masa saboda ta gaji da binne abunda ke tsoratar da tunaninta ko da yaushe. "Ya illahi" ta faɗa hawaye na zubo mata tare da jin komai na dawo mata sabo fal cikin kwanyarta.

Ganin yanda duk ta ɗaga hankalinta ne yasa ya kamo hannuwanta duka biyu ya riƙe yana murza yasunta.

"Ɓoye min da kika yi ne yasa Yaseer ya yi Amfani da wannan damar ya so ya rusa zamantakewarmu."

Ganin kallon da take masa ne yasa
ya miƙe ya dauko wayarta ya miƙa  mata.

Afnan jikinta rawa ya shiga yi, a tunaninta ko video aka yi mata na ɓatanci aka nuna masa.

Hankalinta sosai ya yi matuƙar tashi. Wayar da Yazeed ke miƙa mata ta sanya hannu ta karɓa ta soma ƙaranta saƙwannin ciki......

Yazeed ko YaseerWo Geschichten leben. Entdecke jetzt