A Bangaren Yaseer kuwa. Soyayya ta maida shi wani iri. Sai yanzu yake regrating abunda ya yi wa Afnan saboda bai san yana son ta har haka ba saida Yazeed ya aureta.
Tabbas da ace wani ne ya aure ta da zai iya hakura da ita. Amma sam ba zai taɓa iya lumuntar ganinta tare da Yazeed ba a matsayin ma'aurata.
A yanda yake jin tsanar Yazeed halin yanzu ji yake zai iya kashesa. Ganin yake tamkar ko yaushe ya gansa kallon loser marasa hankali yake yi masa. Me yasa Afnan zata yi masa haka? Me yasa sai a kanta ne komai ke so ya taɓarɓare a rayuwarsa?.
Ko yaushe ya ƙilla ido yaga Yaseer yana so ya gaya masa cewa shi Afnan ta baiwa jikinta ya yi yanda yaga dama da kyawawan halitunta. Amma sai ya ji bakinshi ya yi masa nauyi, ya kasa iya faɗa masa hakan.
Babban abunda ya kwantar masa hanakali bai wuce, jin maganin da Mamiensa ta karɓo a gurin bokanta ba. Da wannan ya ɗauke ɗamarar tarwatsa auren Yazeed da Afnan ɗin ko ta halin yaya.
A ɓangaren su Yazeed kuwa sannu sannu soyayya da shaƙuwa mai tsanani suka shiga tsakaninsa da Afnan duk da cewa basa yawan haɗuwa saboda matsalolin da yake fuskanta duk lokacin da zai keɓe da ita. Sai dai ko da yaushe suna maƙale a waya.
Cikn haka aka sanya ranar tarewarsu sati biy, kasancewar mahaifinsa da ya yi tafiya ya dawo har an kammala gyaran part ɗin da Afnan zata zauna.
Sosai Yazeed ya so a bari ya tare a gidansa tunda ya riga ya kammala sashe ɗaya, amma Daddy ya ce sam ba zai tare ba sai lokacin da zai aure Nabeela sai su tare baki ɗaya.
Har ga Allah ya san yana yawan tauyewa Yazeed incinshi har dai kan lamarin Yaseer da Nabeela. Abun na matuƙar damunshi sai dai ba yanda zai yi dan shi sam ba zai iya ja da maganar Mamie ba, duk yanda take so haka yake yi duk da wani lokaci abun na ci mishi tuwo a ƙwarya.
Bangaren Mamie ko wata Yayarta ce ta ƙara bata ƙarfin guiwar Amfani da maganin da aka bata. A kan haka ma ne ta sanya Nabeela dawowa daga egyp dan ta yi hutu gida wannan karon sabida komai ya tafi masu kan yanda suka tsara.
Afnan na zaune falo domin karɓa kiran Abbanta.
Zaune suke dukansu Abba, mommy, Ibrahim da sagir. kasancewar ranar ta zamo ta weekend.
Abba ya kalle Afnan ya soma magana.
"Tabbas da na kasance mutum mai tsananin son kanshi. Wanda hakan ne ya jawo min na tafka babban kuskuren da ya tashi jefa ni cikin makunyaciya rayuwa"
Sai da ya ɗan ja iska sannan ya ci gaba da magana.
"Ba komai yasa nake irin wannan maganar ba, face duba da irin rayuwar da na tashi jefa Afnan a cikin ta saboda ɓacin rai.
Da ba don Allah ya kawo muna waɗannan mutane masu tsananin adalci da halacci ba da ba mu san yanda rayuwa zata kasance ba nan gaba. Da ba mu san wane irin hannu Afnan zata faɗa ba. Amma da Allah yake karimun Rahimun ne sai ya sanya lamarin ya zo cikin sauƙi dan ya nuna mana ba mu isa yin komai ba ba tare da yardarsa ba.
Wannan magana ina yinta ne ba don komai ba sai don jan kunne da gargaɗi gare ki da ki bi mijinki sau da ƙafa, saboda Yazeed ya gama yi miki komai a rayuwa.
Ki sani idan na ji ko na gani kin mishi wani Abu wanda bai dace ba sai na yi tsananin saɓa miki fiye da yanda ba kya zato.
Na zaɓi in yi miki wannan maganar ne yau don nasan da ga gobe gidan zai fara kachamewa da hayaniyar 'yan uwan da za su fara zuwa daga nesa.
Sannan abu na gaba shine, ban yarda ki kawomin ko mahaifiyarki ƙarar mijinki ba. Ban yarda da ki yi fushi ki yi ya ji ki zo gidana ba koda kuwa ke kike da gaskiya.
idan kuma har ɗaya daga cikin wannan ta faru, ni kaina ban san irin hukuncin da zan yanke miki ba.
Afnan kam tuni hawaye sun gama wanke mata fuska saboda yanda take jin maganganun mahaifin nata na tasiri a zuciyarta.
