Bayan sun wuce ɗaki Afnan ta shiga ta faɗa kan gado tana rusar kuka. Baki ɗaya notukkan kanta sun kwance. tambayar kanta take yi. Shin me Abbanta ke nufi da ita ne? Me yasa ya yi mata haka? Shin bai san ba ta da wanda take so ba idan ba Yaseer ba? Wata zuciya ta ce 'yana nufin ki tsaida Yaseer ɗin'
"No bazan taba auren Yaseer ba koda kuwa son shi zai illata ni I hate him and can't never forgive him for wat he did to me"
Can wata zuciya ta ce 'ki bari kawai Abba ya zaɓar miki wanda za ki aura dama can wannan shi ne ra'ayinsa"
Dafe kanta ta yi saboda ba shawarar da zata iya ɗauka daga zuciyarta a halin da take ciki. "oh Allah ka kawo min mafita ta alkhairi" ta faɗa tana mai jin raɗaɗi da zafi mai ciyo a ƙasan zuciyarta.
Haka ta yi ta saƙe saƙe har aka kira sallar magrib.
Misalin ƙarfe tara Ammi taga Afnan bata shiga wurinta ba kamar yanda ta saba yi. Ganin haka yasa ta shigo dakin Afnan ɗin da ganin halin da take ciki.
Zama ta yi kan gado ta dafa kafa kafaɗun Afnan.
"san kina cikin ruɗani sosai na jin hukuncin da mahaifinki ya yanke a gare ki. Afnan ina so ki kwantar da hankalinki ki cire duk wata damuwa a zuciyarki ki barmin wuƙa da nama. Insha Allahu zan cika miki alkawarin da na daukar miki a assibiti"
Murmushin yaƙe Afnan ta yi. "Ba komai Ammie ko yanzun ma haka nagode ƙwarai da abinda ki ka yi min. Sadani da iyayena kaɗai da kika yi tamkar kin cika alƙawarin da kika dauka ne kuma Nagode maki Allah ya saka miki da alkhairi"
Murmuahi Ammi ta yi"kada ki damu duka yiwa kai ne. Ke dai kawai ki yi abunda nace maki. Ki cire damuwa a zuciyarki insha Allahu Allah zai saka maki da kwatankwacin haƙurin da kika yi. yanzu ki kwanta kawai ki samu ki yi bacci kar kanki ya kama yi maki ciyo" cewar Ammie muryarta cike da nutsuwa da kwantar da hankalin mai sauraro
Sosai magangannuta suka sanyawa Afnan nutsuwa mai ban mamaki har bata san lokacin da bacci ya kwasheta ba.
Bayan kwana biyu sosai Afnan ke ta dubin ta ji me Ammi za ta ce game da maganar amma ta ji shiru. Kallo ɗaya zaka yi mata ka gane tana cikin ruɗani. Duk ta jeme ta yi wani irin sanyi tamkar ba ita ba.
Sosai Ammi ke lura da yanayin da take ciki. Tausayinta take ji sosai, jin matsalarta take yi tamkar ta Hafsa. fatanta kawai Allah ya cika mata burinta ta taimaka mata kamar yanda take so.
Yau ya rage saura kwana biyu cikin kwanakinta da mahaifinta ya ɗibar mata. Ganin har zuwa lokacin Ammie bata ce komai ba yasa ta yanke shawarar ta je ta sameta da maganar dan jin shawararta saboda yanda Yaseer ke mata naci cikin kwanan nan gashi har zuciyarta naso ta aminta dashi a karo na biyu.
Kama hanyar ɗakin Ammi ta yi ba tare da tunanin komai ba. Maganar da ta ji na fita ne daga ɗakin ya sanya ta yi tsaye ta kasa buɗe kofar tana sauraren abun da ake cewa.
"Haba Ammi ya zaki ce in aure yarinyar da ta je ta zubar da mutuncinta a waje?" Ta jiyo muryar Yazeed yana faɗa.
"Ƙaddara ce ta faɗa kanta wadda bata wuce ta faɗa kan ƙanwarka ba. Ko kai baka san ƙaddara ba ne?"
"Gaskiya Ammie ban yarda da gaskiyar yarinyar ba. Ni kwata kwata ma ban yarda da fyade aka yi mata ba saboda alamu sun nuna cewa sam yarinyar ba ta da gaskiya akwai abunda take ɓoyo"
Ganin ya ta kasa shawo kansa kamar yanda take zato yasa ta ce cikin bacin rai.
Wai Yazeed yaushe ka zamo haka ne? Yaushe ka zamo mai taurin kai har irin haka? Ace yau kusan kwana biyu muna abu ɗaya haba. To wallahi tsaya ka ji, idan dai har ni na haifeka kuma na isa da kai, to ka je ka same Afnan yanzu ka gaya mata kana so ka aureta. Kuma idan ka nuna mata wani abu da zai nuna tursasa ka na yi har ta ki aminta da kai to ka je ka nemi wata uwar ba ni ba"
"Subhanallahi me ya yi zafi haka Ammi?"
Ya faɗa yana mai riƙe dukkanin hannayenta.
Muryarsa karye ya ce. "Duk yanda kike so haka za a yi. Amma dai kin san akwai maganar Nabeela kaina ko? Ba na son kan maganar nan Daddy ya sake nisan ta ni daga gare ki"
Murmushi Ammi ta yi. "Ba ma zai saki yunƙurin aikata irin wancan gangancin ba. Maganar Nabeela kuma ni ban ce kada ka aure ta ba, duk da bana son ta saboda nasan ba dan Allah mahaifiyarta ke son haɗa ka aure da ita ba duk da irin abubuwan da ta aikata a gareka.
Shiru ya yi yana jin wani irin ɗaci a cikin zuciyarsa kafin ya ce.
"Toh yanzu kina ganin idan na je masa da maganar yarinyar din zai Amince?"
"Idan ka ce kai ke so ba zai ce a'a ba tunda ya san dama ba son Nabeelar kake yi ba. Kuma ba shi yace ko bayan ka aure Nabeela zaka iya auren duk wadda kake so ba?"
Bai ce komai ba sai lumshe manyan idanuwansa da ya yi, yana jin duk ilahirin kansa ya dau chargy.
Shin me iyayen nasa ke so su mayar da shi ne? Shin shi ba za a bari ya zaɓi abunda yake so ba ne?"
"Ka tashi ka je ka same ta ku yi magana ko hankalinta zai kwanta" ya jiyo muryar Ammie na faɗa.
Jin haka yasa Afnan ta yi saurin barin wurin tana hawaye. Kan gado kawai ta faɗa tana rusa kuka mai bata wahala a ƙasan ƙirjinta.
Da sallama ya shiga ɗakinta. Ganin kamar bata san da shigowarsa ba yasa ya ƙarasa kusa da inda take ya zauna.
"Wan nan kukan da ki ke yi na meye? Na jin daɗi ko na rainin wayo?
Da sauri ta ɗago ta kallesa da rinannun idanuwanta saboda harga Allah bata ji shigowarsa ba.
Taɓe baki ya yi. "Koma mi ye nasan ba zai wuce samarin da kika baiwa kanki ba yanzu suka juya miki baya, right?"
"Pls ka fita daga nan idan magana ka zo ka gayamin"
"Ba magana na zo in gaya miki ba taimakon ki nazo in yi"
"Ka barshi kawai bana buk'atar wani taimako daga gareka. Wanda ka yi min ma ya isa nagode. Yanzu taimakon Allah kawai nake nema"
"Ki ka sani ko nine Allah yasa zan taimake ki, ko ba kya son in samu lada ne?"
Kallonshi kawai ta yi. Idan ance yana magana haka ba zata yarda ba saboda bata taɓa jin maganarsa mai tsawo irin yau ba. Ita zamanta gidan gaisuwa kawai ke haɗata da shi.
"Na san dai yanzu ba ki da wani tsayayye da zaki kaiwa mahaifinki shiyasa naga ya dace in taimaka miki ki gabatar da ni gurin mahaifin naki dan kar a sake aikata yar gidan jiya"
Wasu sirarran hawaye ne suka ziro mata waɗanda bata ma san da zuwa su ba. lallai Yazeed ɗin nan ji yanda ya soka mata magana hankalinsa kwance zuciyarsa zaune. Cikin muryar kuka ta ce.
"Dan Allah Yaya Yazeed ka fita ka tafiyarka. Ina ganin girmanka ka barni kada in gaya maagana. Taimako daga wurinka bana so ka wani iri ne pls"
Murmushi ya yi. "Ki dai ƙara nazari. Ni bana son ki koma ruwa ne"
Wani abu ta ji ya soke ta ta ce cikin ɓacin rai.
"Bari ka ji in gayama abunda baka sani ba Ya Yazeed. mai hali ba zai taɓa barin halinsa ba dan haka ko ka taimake ni ka aure ni ba zan fasa aikata abunda nake aikatawa ba"
"Ki san irin maganar da za ki riƙa gaya min. Ba dan ina son ki na zo nan ba sai don in taimaka miki in fitar dake daga ƙangin da kike ciki kamar yanda na gaya miki. Koma dai miye jibi idan abbanki ya zo sai ki gaya masa ni ki ke so kaman yanda ya buƙata. Amm fa ki sani ni bana son ki kuma ba zan taɓa sonki ba, ko aurenki da zan yi na wani ƙaramin lokaci ne, da zaran kin daidaita da mahaifinki zan sakeki ki je can ki ƙarasa rayuwar da kika daukarwa kanki"
