Babi na ashirin da shidda

580 42 3
                                        

          
Wani irin ƙululun baƙin ciki ne ya tokare zuciyar Afnan har wani ɗaci bakinta ke yi mata. Bata san lokacin da ta fashe da kuka ba tana cewa.

"Wallahi ni ba karuwa ba ce. kuma ka je ka cewa Ammi da ta turoka ni  bana sonka. Na haƙura da taimakonta"

Murmushi ya yi.  "Thank god da kika gane turo ni aka yi. Sai dai ni mai biyayya ne ga iyayena, da dai zaki taimaka min ki je ki gaya mata haka da ba ƙaramin  taimako na kika yi ba."  Yana kaiwa nan ya yi waje abinda, ya barta tana rusar kuka.
cikin ranshi addu'a yake Allah yasa ta je ta gaya ma Ammi bata son sa dan shi yanzu  tama ƙara fice masa a rai saboda yaga bata da kunya.

Bai dai yi ƙasa a guiwa ba saboda yana bala'in girmama umurnin mahaifiyarsa. Yana fita daga gidan Ammie direct gida ya zarce gurin mahaifinsa.
cikin sa'a kuwa ya same sa.  Bayan sun gaisa ne yake sanar da shi maganar son auren Afnan ɗin.

Kallon shi Daddy ya yi cikin tuhuma. "Kana nufin ba wanda zai taimakama ta  ya aureta sai kai alhali kuma kai ka san akwai maganar Nabeela kanka"

Dum! Gabansa ya faɗi dama ya san Sai Daddy ya yi wannan maganar.

Sosa ƙeya ya yi. "Ba haka ba ne Daddy, yarinyar ce tana buƙatar taimako ne saboda takunkumin da mahaifinta ya sanya ma ta"

Ganin har zuwa lokacin kamar Daddy bai Aminta ba yasa ya ce.
"Gaskiya kuma yarinyar ta kwanta min ina sonta saboda ɗan zaman da ta yi gidan Ammie na fahimce tanada kirki"

Murmushi Daddy ya yi.  "Na ji daɗin jin haka a bakinka. Tun farko da ka tsaida hankalinka ka kawo min wadda kake so ai da ban takuraka kan auren wata ba. Amma duk da haka ka sani maganar Nabeela tana nan."

Kwanakkin nan bai san abunda yasa mahaifin nasa ke sake masa ba. Ko ba komai abun na masa daɗi ko bai so ya faɗa. Ganin yanda yake masa yasa ya ce bari ya gwada damarsa ko Allah nasa ya ragewa kansa jangwangwama. Cikin ladabi ya ce.
"Amma Daddy ka san fa ba wata soyayya tsakanina da Nabeela ni a matsayin ƙauna na ɗauke ta"

"Kar ka soma wannan zancen yanzu. Idan baka sonta ai ita tana sonka. Kuma kaima Zuwaira ta ce min kana sonta. Dan haka ka shirya ko su duka biyun  hali ya yi sai a wanke ma su lokaci ɗaya a kaima.

Murmushi kawai Yazeed ya yi tare da yi wa mahaifinsa godiya sannan ya wuce.

Tun bayan da ya bar gurinta take ta rusar kuka har wani jiri take jin yana ɗibarta  saboda tsantsar damuwa. Haka Ammi ta zo ta risketa cikin wannan halin.

"Lafiya kike kuwa Afanan?" Ammie ta faɗa da sauri tana mai isa kusa gareta.

Cikin dauriyabta ce.
"Lafiya kalau nake Ammi, kaina ne kawai ke min ciwo."

"Eyya in jin kin sha magani?"

Gyaɗa kai ta yi. "Eh na sha bada daɗewa ba"

"Toh Allah ya sauwaƙa"

Afnan ta karɓa da  "Ameen".

Ammi ta ce,
"Dazu Yazeed  ya zo min da wata magana. Wai yana so ya aure ki. shine na ce to  ya zo ya ji ta bakinki idan kina sonsa. Ina fatar dai kun daidaita kanku ko"

Wani murmushi Afnan ta yi mai ciyo. "Amma Ammi kina ganin abun bai yi yawa ba?  Gaskiya Ammi ni ba zan iya auren Yaya Yazeed ba ko dan halaccin da kuka yi min. Ni na ma yanke shawara kawai Abba zan barwa zaɓi. Duk wanda ya zaɓar min zan aure sa amma gaskiya ba zan iya rushe future ɗin' Ya Yazeed ba. Dan na san ya yi ne kawai saboda tausayina.

Fuskar Ammi tuni ta koma ta damuwa. "Haba Afnan ya za ki ce haka? Shi fah ya ganki ya ce yana so. Shi ya ji zai iya dan kansa. Shin kin san wanda mahaifinki zai haɗa ki da shi ne?.  Idan mahaifinki bai gaya masa ƙaddarar da ta auku kanki ba ya zaki kallesa, ko me zaki ce masa lokacin da zai tuhume ki kan mutuncinki?. Yazeed fa shi ya san komai naki dole zai hakura a duk yanda ya same ki. ki yi tunani a kai  Afnan kar wankin hula ya kai ki ruwa".

"Ammie na riga na yi tunani dan Allah  ki yi haƙuri amma gaskiya ba zan iya Auren Ya Yazeed ba"

Ran Ammi ba ƙaramin ɓaci ya yi ba. Hankalinta ya yi bala'in tashi. Sam bata so Afnan ta yi mata nisa. Tana kaunar yarinyar sosai saboda ita kaɗai take ganin ta dace da Yazeed ɗinta.

Cikin mutuwar jiki ta ce. "Anya Afnan! Ko dai wani Abu Yazeed ɗin ya gaya miki na ɓacin rai?"
(Ammie na so ta tonawa kanta asiri)

"A'a wallahi Ammi ba abunda ya gaya min, kawai dai bana so na cutar da wanda ya taimake ni  ne shi yasa na ba sa haƙuri na gaya mishi ba zan aure sa ba."

"Ki dai tsaya ki yi tunani da kyau Afnan ki zabi abunda ya dace da rayuwar ki. Na barki lafiy" ta faɗa tana  barin ɗakin ranta ba daɗi.

Tana fita taci karo da Yaseer.
Gaidata Ya yi sannan ya tambayeta Afnan saboda yanzu ya daina dari dari idan yaga Ammie. Nuna mishi ɗakin da ta ke ciki ta yi  kawai tayi ta haye sama abunta.

Da sallama ya shiga ɗakin. Sai da ya yi kusan sau uku sannan ta ji saboda hankalinta sam baya kant. Ganin mai sallamar ne ya sanya ta kara ɗaure fuska.
"Malam me ya kawo ka cikin ɗakina, ko fyaden ka zo ka sake yi mini?"

Murmushi ya yi tare da takawa kusa da ita ya zauna.
Matsawa ta yi nesa da shi  tana hararasa.

Wani shu'umammen murmushi yake mata mai narkar da zuciya.
"A ina kika taɓa ganin miji ya yi wa matarsa fyaɗe?"

"Ka gyara maganarka, ka san wadda kake magana da ita. Wannan Afnan ce ba matarka ba"

"Toh na ji ba matata kike ba mai shirin zama matata. Ya yi maki haka?" Ya fada yana kashe mata ido ɗaya.

"God forbid ni da mayaudari irinka har abada Wallahi" ta faɗa kanta tsaye.

A hankali ya sauko ya gurfana kasa kusa da ƙafafunta.
"Plz Afnan let begone be bygone. Wallahi Allah ba halina ne ba. Dan Allah ki bani wani chance  in nuna maki irin ɗin bin ƙaunar da baki taɓa mafalki ba. Wallahi Afnan ina yi miki son da ban taɓa yi wa ko wace macce  ba. Afnan ina son ki ba zan iya rayuwa ba sai dake. Dan Allah ka da ki bari Abba ya haɗaki da wani. Idan Abba ya haɗaki da wani mutuwa zan yi.  Afnan ki yi haƙuri ki yafe min mu inganta rayuwarmu. Ke kanki kin san ni kaɗai ne zan iya rufa miki asiri nida na aikata miki ba dai dai ba. Dan Allah Afnan kar ki hukunta ni ta hanyar barina" ya faɗa hawaye na zubowa a idanuwansa.

Tausayinsa ta ji duk ya haɗe ilahirin jikinta. Idan dai abunda take gani a ƙwayar idanuwansa gaskiya ne toh kuwa sonta ne kwance cikin ƙwayar idaniyarsa.
Sai dai abunda ta kasa fahimta idan har yana yi mata irin wannan son to me yasa ya keta mata haddi? Lallai wannan ita ce damar da za ta yi amfani da ita don ta ɗauki fansar abunda ya yi mata.

Ganin ta yi shiru ne ya sanya shi jin wani daɗi a ruhinsa. tabbas haƙonsa na  dab da cimma ruwa.
Cikin rawar murya ya yi magana

"Pls Afnan kice kin yafe min. Ki ce wani abu mana"

"No Yaseer ba zan iya ba. Ba zan iya yafe maka ba. Ba zan iya ba" ta faɗa tana controlling hawayenta dan ta gaji da zubar da su inda ba su da amfani.

Dafe kansa ya yi.  "Is ok Afnan na ji ba za ki yafe mun ba, amma pls kada ki ce ba zaki aure ni ba"

Murmushi ta yi. "Ko na aure ka kada ka yi tunanin jin daɗin zama da ni. Dan haka ka je zuwa jibi ka dawo Dan har yanzu ban gama shawara da zuciyata ba."

Wani irin daɗi ya ji ya a ƙasan zuciyarsa. Ya san ta dai ce ne kawai Amma ba za ta iya yi masa komai ba.  Ta da auresa kawai zai yi maganin ko ma miye.
A hankali ya ce. "Nasan ai ba za ki watsan ƙasa a ido ba. Nagode ƙwarai da halaccinki a gare ni,  zan zo jibin don jin abunda kinka yanke."

Bayan ya  fita  ne Afnan ta dafe kai tana furta. "Inalillahi wa'inna ilaihirrajiun allahumma ajirni fi musibati wa khalifni khairan minha."
Abunda take ta nanatawa kenan.

Zucitarta kuwa  sai saƙe saƙe take yi mata. Tabbas ta san abunda Yaseer ya ce gaskiya ne. Duk duniyar nan kuma shi ne kaɗai zai iya rufa mata asiri shaida ya keta mata haddi. Ko ba komai  za ta iya auren sa  ko don ta FANSHE BUDURCINTA.

Wata zuciya ta ce, 'idan kika aure sa kin yi wa Ammi adalci na barin gidan jikinta?'

"Ina ba zan iya auren Yazeed ba. Saboda idan na aure sa  WULAKANTANI zai yi"

Wata zuciya tace, to  wa zaki zaɓa a ciki
YAZEED  KO  YASEER? Ko kuma ZAƁIN MAHAIFINKI?

Zubewa ta yi kan gado ta fashe da kuka saboda rashin samun takamammiyar Amsar tamabayar da zuciyarta ta yi mata.

Masu karatu Ku bata Amsa wa zata zaba YAZEED KO YASEER?

Yazeed ko YaseerCerita yang bikin terobses. Temukan sekarang