Yazeed koYaseer
Ayshart Farouq
Nagarta writers association
4
Bayan sati biyu da faruwar haka su Afnan suka koma makaranta. Wannan karon komawa hutun ya yi
Mata daɗi sosai saboda kusan koda yaushe tana tare da Yazeed ɗinta suna soyewa.Karatun da take yi ma yanzu ta fara ja baya da shi sosai kasancewar wani lokaci ko attending lectures ba ta yi yanda ya kamata. Saboda ko tana aji Yazeed ya kirata fitarta take yi ta je wurinsa su sha soyayyarsu son ransu. Haka kuma idan
ta dawo gida matukar tana cikin ɗakinta ita kaɗai to kuwa suna nanne ne da juna a waya."Afnan! Afnan!" Ta jiyo muryar yayanta Sagir yana kwala mata kira daga waje.
Harararsa ta yi lokacin da ya ƙaraso cikin ɗakin nata.
"Mi ye ne wai kake ta ƙwalan kira haka" ta ce ba tare da ta tashi daga kwancen da take ba. Haka kuma bata katse wayar da take yi da Yazeed ba. Saboda ba kowa ne zai iya fahimtar cewa tana waya ba saboda headphone ɗin da ke maƙale a kunnenta.
Ganin hararar da take ta zuba mishi ne ya sanya Sagir ɗin ƙarasa karasowa kusa da ita. "Ni kike harara?"
Ya faɗa yana nuna kansa da yatsa.Turo baki ta yi. "To miye na kwala min kira haka tun daga waje kaman kana biyata bashi?"
Tsaki ya ja "Wallahi kin rainani da yawa Afnan. Ammah zan yi maganinki"
"Oho dai" ta faɗa ciki ciki.
Kwafa ya yi kafin ya ce.
"Abba ya ce in kira ki, idan
kuma baza ki je ba sai in je in faɗa masa kina waya da saurayanki ba ki da lokacin amsa kiransa" ya faɗa idanuwansa a kanta.Zaro idanuwa ta yi "Allah Ya Sagir ba waya nake yi ba. Ni ina naga saurayin da zanyi waya dashi saboda Allah?. Waƙa ce fah kawai nake sha ni kada kamin sharri" ta faɗa cikin ruɗani. Kalli ɗaya zaka mata ka gano batada gaskiya.
Murmushi ya yi ganin yanda ta ruɗe "Marsa kunyar banza da dai ki bari in je inje in gaya masa haka"
"Tab rufan asiri dan Allah gani nan zuwa yanzun nan Sweet Yaya"
Harararta ya yi kafin ya ce. "Daga baya kenan. Ki dai gode Allah na ƙwaran ba kaina da kinga sharri yau" ya faɗa yana barin ɗaki.
Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta waiwaye wayarta da bata san lokacin da ta daƙaleta ba.
Kiran da ya shigo ne yasa ta sake ɗaukan wayar still earpiece ɗin na kunnenta.
Tsokanarta ya fara saboda kusan duk ya ji maganarta da Sagir.
"Kin cika tsoro Baby. kamata ma ya yi idan kika je yanzu ki cewa Abba kina biyayya ga mijilnki ne, kina faranta masa rai, kina masa fira mai dadi yana jin muryar nan ta ki mai daɗi tana ratsa jikinsa kina samun
lada"Dariya Afnan ta yi tare da cewa,
"Yazeed kenan!, kwarai kuwa Zan gaya mishi haka. Idan kuma ya zo min faɗa har Kai sai ya tattara ya haɗa"Shima dariya ya yi "ba komai, ai kin San dama daɗi da wuya munyi alkawarin rabashi ni da ke"
Murmushi ta yi tamkar yana ganinta. "Zan ɗauki wuyar ka dauki daɗin"
"A'a ni zan ɗauki wuya ke ki ɗauki dadin"
"Ni dai a'a mana" ta faɗa cikin muryar shagwaba.
A kasalance ya ce, "kin ganki ko? kin Fara kashe min jiki da shagwabar nan taki. Yanzun sai kisa tunanin ya fitine ni ya hanani sakat"
Dariya ta yi. "Ai haka nake so tunanina kaɗai ya fitine zuciyarka"
"Afnan!" ta sake jin muryar mahaifiyarta, na kiranta. Da sauri
ta katse wayar ta fita da gudu, tana cewa.
"Gani nan zuwa momy ina banɗaki ne""Toh ai tunda kin fito sai kiyi maza kiyi sauri Abbanku na son magana
dake tun ɗazu"Ta karɓa da "Toh Mommy"
Falonsa ta nufa cikin sauri zuciyarta cike da tunanin dalilin kiran da yake yi mata.
Da sallama ta shiga falon nasa, sai dai
ganin Ibrahim da Sagir a zaune gaban
mahaifan nata ne ya sanya gabanta ya ɗan faɗi saboda ko ba a faɗa ba tasan dole ne akwai maganar da Abbnta zai yi masu. Ita dai fatanta kawai Allah yasa ba faɗa ne zaiwa ɗayansu ba. Saboda wani lokaci idan wani ya yi laifi duka yake taraku ya yi masa faɗa. Sannan ya gameku yayi maku ku duka.