Ɓangaren su Yazeed kuwa. Tun lokacin da suka bar gurin Daddy ya fara jin mood dinshi na canzawa. Ba kamar yanzu ma da suke zaune dab da juna.
Ɗan janyota ya yi jikinsa cikin dabara ya fara shafar jikinta yana faɗa mata kalamai masu daɗi nutsar da zuciya cikin kogon ƙauna.
A hankali ta ji ya fara wuce gona da iri. Nan take irin makamcin abunda ta riƙa ji a daren jiya ya sake taso mata.
Lokaci ɗaya jikinta ya fara rawa. Cikin tashin hankali ta samu ta kwace jikinta daga garesa ta faɗa dakinta da sauri ta sanya key.
Da mugun mamaki Yazeed ya bita da kallo. Bai yi yunƙurin bin bayanta ba, zaune kawai ya yi yana ambaton sunan Allah.
Saida ya fara jin nutsuwa na safkar mishi sannan ya tashi ya ɗauke makullansa ya yi gidan Ammie.
Ya daɗe sosai gidan Ammie sannan ya dawo gida. zuwa lokacin kuma har ya dawo normal.
Ganin har karfe huɗu ba alamar Afnan ta fito ta ci Abinci ya sanya shi ya je ya buga mata kofa. Tana jinshi ta ƙara makurewa kan gado.
Saida ya yi ta haɗata da Allah tare da alƙawarin ko hannunta ba zai taɓa ba sannan ta fito.
Tana fitowa ko kallonta bai yi ba ya isa dining ya zuba mata abinci. Kasa cin abincin ta yi sai sharɓar kuka take yi. Har ga Allah ta san ba ta kyautama mijinta mai ƙaunarta ba. Sai dai ba yanda ta iya da wannan sabon al'amari da ya sameta.
Ganin taƙi cin abincin ne yasa ya shiga lallashinta da kwantar mata da hankali dakyar dai ya samu ta ci kaɗan.
Nan suka zauna suka ɗan taɓa fira duk da ba wata maganar kirki ce suka yi ba. Yana ganin yanayinshi ya fara sauyawa Ya bar mata falon ya yi tafiyarsa dakinshi.
Ganin ya daɗe bai fito ba yasa itama ta koma ɗakinta ta kwanta jiki ba ƙwari.
A haka dai har suka yi sati ɗaya. Cikin satin nan kuma kullun za su je gaida Mamie a tare da safe. Amma da sun dawo kuma sai kowa ya kama gabanshi.
Bayan wata ɗaya. Sosai Afnan ke ƙoƙarin ganin ta sauke duk wani haƙƙi nasa da ya shafe dafa abinci da kuma tsabtar muhallinshi.
Ita kanta yanzu tsoron da take ji duk lokacin da zata keɓe da shi ba ƙarami damunta ya fara yi ba. Ba ma kamar da taga Yazeed ɗin ya fara nuna mata halin ko in kula.
Saboda yanzu duk ma wata hanya da za ta sadata da shi ya toshe ta. Tun da sassafe idan ya fita gidan baya dawowa sai cikin dare.
Sosai abun ke damunta. Ta yi kuka har ta gaji ba tare da ta san wanda za ta iya kaiwa matsalarta ba, saboda cikin kashi ɗari ta san chas'in da tara duk laifinta ne.
Ta rasa abunda ke damunta na rashin bashi haɗin kan da take yi don sauke hakkinsa da ya rataya a kanta. Kwanan baya har ciyo ta ji mishi a kai da ya neme kusantar ta. To tun daga lokacin sai ya fita hanyarta baki ɗaya.
Misalin ƙarfe goma sha biyu na dare ne ya shigo cikin gidan. Yana shigowa direct ɗakinshi ya shiga ya yi wanka ya sanya kayan baccinsa sannan ya nufe dining ya ɗan tsakule abinci ya ci saboda yunwar da ya kwaso gashi shi sam baya son cin abincin waje tun inda aka fito.
Sai da ya kammala cin abincinsa ne har zai koma dakinshi sai kuma ya kai dubanshi ɗakin Afnan.
Wani abu ya ne ji ya ɗarsu a zuciyarsa. Nan take wata zuciya ta tunasar da shi hakkinta dake kanshi. Idan bai manta ba yau kusan sati biyu bai sanyata a idonshi ba saboda irin sammakon da yake yi da kuma daren da yake yi kafin ya dawo.
Wani abu ya riƙa jin yana taso mai mai kama da shakku da tsoro.
A hankali ya isa bakin ƙofar ɗakin murɗa handle ɗin ƙofar ya yi duk da bai yi tunani zai ji kofar buɗe ba. Ga mamakinshi sai ya ji yana mirɗawa kofar ta buɗe.
Cikin sanɗa ya shiga ɗakin, ko ina tsab tsab sai ƙamshi ke tashi.
