Babi na talatin da shidda

658 124 31
                                    

Ko bata duba ba ta san mai kiranta a wannan lokacin.

Samun kanta ta yi cikin faɗuwar gaba saboda bata ma san me zata ce masa ba.

Kasa ɗaukar wayar ta yi har saida ta tsinke ya sake kira, shima sai da kiran ya kusan tsinkewa sannan ta ɗaga.

Ba wanda ya yi magana cikin su har saida suka yi kusan mintuna uku suna sauraren nunfashin junansu sannan  cikin kasala Yazeed ya ce.

"Kar dai kice min bacci kike yi"

"Uhum" kawai ta iya cewa saboda yanda muryarsa ta bada wata irin gudunmuwa mai ƙarfin wurin nakasa kuzarinta.

"Buɗa baki zaki yi ki yi min magana Afnan"  karo na farko da ta ji ya kira sunanta.

"Ina jinka YaYazeed" ta faɗa cikin wata murtayar da bata santa da ita in fa aka fito ba.

"So ki bani labari" ya yi maganar a kasalance.

Murmushi ta yi.
"Wane labari zan ba ka?"

"Labari mai daɗi wanda zai sa in yi bacci cikin nishaɗi"

"Da baka bacci cikin nishaɗi ne?"

"Ina yi idan  na yi tunaninki. Sai dai na yau na san  zai fi na ko yaushe  daɗi"

"Dare ya yi yanzu Yayazeed, sha dai da rabi fah"

"Ai yau muna tare da ke har safe. Hukuncinki na sanya ni wanka biyu ba tare da na yi ra'ayi ba"

"Wanka kuma Ya Yazeed?"  Ta faɗa saboda bata gane inda ya dosa ba.

"Eh mana. Ɗazu kin sakani a gidan Ammie,  bayan kuma na  kawoki gida kin sake sanya ni wani"

Dif! ta yi saurin kashe wayar saboda ta gane abunda yake nufi. Kanta ta sanya cikin pillow tamkar yana ganinta saboda kunyar da ta jiya.

Tana niyar kashe wayar baki ɗaya dan kar  sake kiranta, ta ji ƙarar shigowar sakonsa.

Buɗewa ta yi tana karantawa.
"Wannan ya zama na ƙarshe da za ki kashe min waya ina magana. Zan sake kiran ki, kuma idan ba ki ɗaga ba gobe zan zo gidanku da kaina kenan in sanya ki abunda kika sanya ni. Try me idan kina ganin ba gaskiya ne ba"

Dafe kanta ta yi, kunya tamkar ta nutse cikin ƙasa.

Ba ɓata lokaci ya sake kira. Ba ta da wani zaɓi da ya wuce ta ɗaga saboda ta san tsab zai iya aikata abunda ya ce.

Tana ɗagawa ya sanya mata dariya.

"Kar dai kin fara shakkata tun kafin aje ko ina?"

Ba ta da amsar ba shi amma tabbas ta fara jin shakkunsa.

"Kin yi shiru"

"Toh me zan ce?" Ta faɗa tamkar za ta yi kuka.

Murmushi ya yi har saida ta ji sautinshi a wayar.

"Yanzu ki gaya min ya aka yi deary na ya shiga hannunki, kafin in yanke miki hukuncin karanta min sirri ba tare da izinina ba"

"Ni Allah tsinta na yi, kuma ni ban karanta komai ba" ta faɗa cikin shagwaɓa kamar zata yi kuka.

Shi kan shagwabarta na matuƙar burge sa. Da ta san yanayin da yake taintar kansa a duk lokacin da ta yi masa da ta tausaya masa ta rage yi masa ita.

Kwaikwayon muryarta ya yi shima yana murmushi. "Ni ba ruwana sai kin karɓi hukunci"

Dariya ta yi jin yanda ya yi maganar. "ka yi haƙuri Allah ba da gangan na karanta ba. Kuma ma pages ɗin ƙarshe  ne kawai na karanta fa"

"Uhum kuma su suka fi komai muhimmanci cikin deary ɗin, don haka punishment ɗinki sai randa kinka tare"

Zaro idanuwa ta yi.
"Haba Yayazeed na fa ce Allah pls"

"Na ji to amma sam ba fashi sai kin karɓe hukunci. Allah dai ya kai damo ga harawa, ko bai ci ba sai ya yi birgima"

Dariya ta sanya jin karin maganarsa.
"Ashe dai ka ji Hausa?"

"Sosai kuwa. Ni yanzu ki gaya min ya aka yi kayana ya kai hannunki coz nata nemansa ban gansa ba harma na fitar da rai da shi."

"Na gayamaka tsinta na yi kan hanya"

Nan dai ta kwashe labarin yanda aka yi ta tsinta da yanda aka yi ta karanta duk ta gaya masa"

Jin jina kai kawai ya yi saboda ya san tabbas wannan abun yin Allah ne kawai.

"Kin san wani abu?" Ya faɗa cikin sanyin murya.

Girgiza kanta ta yi tamkar yana ganinta.

"Ban taɓa shiga tashin hankali ba irin ranar da aka ce ki faɗi wanda kike so. Tabbas ranar da kin faɗi wani ba ni ba, da ban san ya rayuwa zata kasance min ba.
I can't hide it any more. Afnan ban taɓa son wata 'ya mace ba sai ke. Ban taɓa sanin ciyon so ba sai a kan ki. Ban san yanda zan kwatanta miki irin yanda nake ji ba idan har na yi arba dake."

Haka dai Yzeed ya yi ta fayyacewa Afnan sirrin zuciyarsa da tun tana uhum har ta fashe da kuka. Saboda ita mutum ce mai son a so ta. mutum ce mai son a nuna mata kulawa a kuma kaunaceta. Da wannan damar Yaseer ya yi Amfani ya sanya mata soyayyarsa daga baya kuma ya zo ya yaudareta.

Jin yanda take kuka ne ya sanya jikinsa mutuwa cikin galabaitacciyar muryarsa ya ce.
"kukan me kike yi ne Afnan? Ko ba kya so na ne?

Girgiza kanta ta yi.
"Ba haka ba ne Ya Yazeed. Kukan farin ciki nake yi,  da Allah ya bani namiji irinka. Ban taɓa ɗauka zan samu mai sona haka ba. Ban taɓa ɗaukar cewa mace irina zata samu irin wannan soyayyar ba. Na ɗauka ba zan taɓa samun irin wannan soyayya ba har abada. Nagode ƙwarai  Ya Yazeed. Nagode da HALACCINKA a gareni. Ya Yazeed nagode da son da kake min a yanda ka ganni. Haƙiƙa ba ni da abunda zan saka maka. Allah ne ka ɗai zai iya saka maka"

"Kema zaki iya saka min Afnan idan har kika so ni, ki ka bani yardarki da amincewarki. Ki ka toshe duk wata ƙofar da zata kawo rashin yarda a tsakaninsu. Idan kika yi min haka kin gama min komai. Ki yi bacci lafiya zan tada ki asuba insha Allahu"

Jin ta yi tamkar kar ya kashe wayar. Bata jin bacci sam saboda yanda take ji a zuciyarta.

Dafe kanta ta yi. Abinda take ji game da Yazeed ta san ba soyayyace ba. Saboda a zuciyarta Yaseer ne mutum na farko da ta so. Sai dai abunda take ji game da Yazeed ba ta taɓa jin makamancin irinsa  a kan Yaseer ba. Shi yasa take tunanin cewa ba soyayya ce ba.
Ni ko nace (to meye Hajiya Afnan?)

Shi kuwa Yazeed kasa komai ya yi sai juya waya da yake yi. ji yake da yana samu ya yi kuka da ya yi saboda yau ya fidda abunda ya daɗe yana ci mishi zuciya.
Bai ƙara jin yana son Afnan ba sai lokacin da Yaseer yake mishi bori kan cewa shi yake sonta.
Tabbas Allah ne yakawo Afnan cikin rayuwarsa don ya kaunace ta. Allah ne ya kawo Afnan cikin rayuwarshi don ya nunawa Yaseer da Mamie cewa ba ko yaushe mutum ke samun abunda yake so ba.

Idan ba zai manta ba akawi wata yarinya cousin ɗinsa da ya yi dating. Tun farko yarinyar ita ta fara laƙe masa har shima ya ji yana ra'ayinta. Tunda Yaseer ya ƙyalla ido ya gansa da yarinyar nan bai sake kwanciyar hankali ba sai da ya mallake yarinyar. Daga ƙarshe da yaga ya haƙura da ita sai shima ya yi dumping ɗinta tun da dama da biyu ya yi.
Kusan yarinya biyu yana dating cikin danginsu Yaseer na kwace masa. Dama kuma yaran ba su damesa ba sai ma ya daina dating ko wace yarinyar soyayyar ma kwata kwata sai ta fita a ransa.
Sai yanzu Allah ya bashi wadda yake so.
Afnan ce abu ta farko da suka yi tarayyar sonta da Yaseer ya mallaketa ba tare da Yaseer ya mallaketa ba, basu taɓa tarayya son wani abu da shi da Yaseer ba face Yaseer ya mallakesa. Duk abunda yake so Yaseer shi ke mallakarsa ciki kuwa har da uban da ya kawosa duniya.

Masu karatun novel din nan kuna bani mamaki. A page zakaga mutanen da suka karanta sun kai ɗari amma ba zan same vote din da ya wuce goma ba. Comment kuma sai na dauki lokaci ban yi ba zaka ji ana magana. Dan Allah ku riƙa vote da comment suna ƙara ma mutum ƙarfin guiwa.

Novel din nan na yi shi tun wuraren 2016/2017
Editing nake yi. Duk da still akwai kura kurai  da dama  cikinsa.

Yazeed ko YaseerWhere stories live. Discover now