Babi na ashirin da tara

611 53 4
                                        

Baki ɗaya ƙafafuwansa kasa ɗaukar shi suka yi. zubewa nan ya yi yana wani irin nishi mai ƙarfi.
Shi kaɗai ya san abunda yake ji.
Ganin yake yi a duniya bai taɓa shiga tashin hankali irin na yau ba.

Ya san ba ma yanda za ayi ya iya  jewa Iyayensu da wannan maganar. kuma ya tabbatar da idan bai aure Afnan ba zai iya rasa rayuwarsa a yanda yake jin sonta cikin zuciyarsa.

Daƙyar ya samu ya lallaɓa ya tashi yana bin bango ya bi ta ƙofar baya. Allah ne kaɗai ya kai sa gida lafiya a wannan lokacin.

Yana shiga ɗakin mahaifiyarsa ya zube k'asa yana rusar kuka tamkar wata macce.

Ganin halin da yake ciki ne ya sanya Hajiya Zuwaira ta yo kansa da sauri tana tambayarsa.
"Me ya sameka haka Yaseer?" Ta tambaya cikin ruɗani.

"Mamie mutuwa zan yi."

"Me yake faruwa ne wai? Me kake faɗa ne? an bada yarinyar ga wani ne ko me? Ka yi min baya ni mana dan Allah"

"She left me Mamie. She choose some one over me. Mamie she choose him, mutumin da na tsana fiye da kowa Mamie shi ta zaɓa ta bar ni"

"Wace irin magana kake yi haka Yaseer wa ye ta zaɓa ni ban gane ba ka yi min yanda zan fahimta"

"Mamie Afnan choose Yazeed over me."

Wata irin uwar ashar Mamie ta saki. "Yazeed fah ka ce? Chab uban nan ai wallahi ba zai yiyu ba. Nabeelah fah? Ina it can't be ba zan taɓa bari Yazeed ya aure wata ba idan ba Nabeela ba. ta ya zai rushe min plan ɗina ne? Sam ba zai yiyu ba wallahi. Shin dama yana son yarinyar ne ko kuma aikin uwarsa ne?"

"Nima ban sani ba Mamie. Banga wata alama da ta nuna yana son yarinyar ba shiyasa ma ni ban damu da zamanta gidansu ba"

Kwashe yanda suka yi da Afnan ya yi ya faɗawa Mamie, saboda ba abinda bata sani ba har na fyaɗen da ya yi mata.

Sosai hankalinta ya tashi. Saboda tana ganin tonuwar asirinta ƙarara idan har Yasser ya faɗi shi ya yi mata fyaɗe. Cikin tashin hankali ta ce.
""Kan uban nan lallai wannan yarinyar ta zo da abunda ba zai taɓa yiyuwa ba. Ta yaya zaka je ka gayawa Alhaji kai ka yi mata fyaɗe kuma da sunan gudan jininsa? kai gaskiya wanna ba zai taɓa yiyuwa ba"

"Mamie ba zan iya bari ta aure wanina ba must especially ma Yazeed. Gaskiya  zan yi duk abunda take so dan in aureta"

Da tsawa Mamie ta katse sa. "Ka kuwa san abunda kake faɗa?"

"Na San abunda nake faɗa mana. Sannan ko ma miye ke kika ja min da tun farkon da naso na faɗa gaskiya kin bari ni na faɗa da duk haka bata faru dani ba"

Ganin yana so ya ɗahe mata yasa ta ce."Ka yi haƙuri Yaseer.  Duk wannan abun ba zai faru ba. Na yi maka alƙawarin idan dai har sunana Zuwaira to sai ka aure wannan yarinyar.  Sha kuruminka bari kawai Alhaji ya dawo gidan nan."

Wani sanyi ya ji a zuciyarsa jin kalaman mahaifiyarsa. Tabbas ya san dole ta yi wani abu a kai ko dan yanda ta sha burin ganin Yazeed ya aure Nabeelah. Ya tabbatar da zata iya aikata komai don ta hana auren Yazeed da Afnan. A yanda ya san mahaifiyarsa ya san  duk abunda ta gayawa Daddy bai isa ya tsallakesa ba. Da wannan ya ji ya samu nutsuwa mai yawa a zuciyarsa.

Kamar yanda Ammie ta yi alkawari Hafsa na dawowa suka je suka kai Afnan gida. Mommy ta yi murna sosai ta kuma yi ta yiwa Ammie godiya da karamcin da ta yi masu.

Ita kuwa Afnan ganinta  cikin gidansu ba ƙaramin daɗi ta ji ba, nan take ma sai ta ji tana neman ta manta damuwarta.

Daƙyar Hajiya Zuwaira taga safiya ta waye mata saboda jiya kwana ta yi tana kiran wayar bokanta bata samesa ba. Yau tun da sassafe ta bar gidan ta yi ƙauyen da yake.

Yazeed ko YaseerOpowiadania do pokochania. Odkryj je teraz