Tun lokacin da Yazeed ya bar gurin Afnan bai sake komawa ba kuma bai nemeta ko a waya ba. Ya so ya yi mata maganar Yaseer sai kuma yaga rashin kyautuwar yin hakan. Saboda ya yi tunanin lokacin da abun ya faru Yaseer ma baya ƙasar bai yi sati ɗayama da dawowa ba shi yasa hankalinsa ya kwanta ya kauda wannan tunanin.Misalin karfe 5 na yamma Afnan na zaune ita da Mommy suna fira. Message ta ji ya shigo wayarta. Kamar kar ta duba sai kuma ta kasa sharewa duk da tana tunanin cewa ƙila mtn ne saboda yanzu ko charting ta daina yi kuma ba ta da number kowa sai ta 'yan gidansu, da su Ammie.
Koda ta duba sai taga Yazeed ne. Murmushi ta yi da ta buɗe saƙon.
"Hi!
Ki shirya nan da minti ashirin za mu je wani wuri"Yazeed.
Wani murmushi ta wa yi mai haɗe da jan sirarin tsaki.
Kallonta Mommy ta yi.
"Lafiyarki kuwa kike tsaki?""Lafiya lau Mommy"
Taɓe baki Mommy ta yi tana cewa. "Wannan ɗabi'a taki ta tsaki ki dainta don ba ɗabi'ar kwarai ba ce."
Daga haka kuma sai suka cigaba da firarasu.
Ibrahim ne ya shigo gidan da sallama yana cewa.
"Mommy ga surukinki can waje ya zo ya ce ba zai shigo ba"Gaban Afnan ne ya yi ras ya faɗi ta zubawa ƙofa ido kamar zata gansa a wurin.
"Haba dai shi kuma Yazeed don me ba zai shigo ba? Ai yanzu ya wuce ya ce sai an yi masa iso ni ba surukarsa ba ce mahaifiyarsa ce. ka je ka shigo da shi mana ai duk laifinka ne...."
Bata ida rufe bakinta ba ya yi sallma ya shigo, fuskarsa ɗauke da murmushi. Suit ne jikinsa dark blue, da baƙaƙen takalma. Sumar kansa ta kwanta luf sai sheƙi take yi. Daga gani daga assibiti yake daga shi har Ibrahim ɗin saboda kusan yanayin shigarsu iri ɗaya ce.
Sai da ta ji yana gaida Mommy sannan ta dawo daga duniyar mamakin da ta tafi.
"Lalala, shine zaka shigo ba za ka jira a yi maka iso ba?" Ibrahim ya faɗa yana kallonsa.
Mommy ta ce. "Oh dama kai ne ka dakatar da shi a waje kuma ka zo kana cewa yace ba zai shigo ba?"
Murmushi Yazeed ya yi. "Wai har ya kai ga kulla min sharrin alhali Ni na taimaka masa na ba shi lift"
"Lift ɗin dole ne ka bani ai tunda ba yanda za ka yi na riga da na shiga gabanka na zama yayanka"
"Baka shiga gabansa ba kam tunda shi yana da mata kai kuma ka tsaya ruwan ido" cewar Mommy tana murmushi.
Dariya suka yi dukan su.
Afnan kam sunkuyar da kanta kawai ta yi ƙasa tana wasa da yatsunta. Mommy sai jefa mata harara take yi ganin taƙi gaishe da Yazeed.
Sunfi minti goma suna fira sannan Yazeed yace. "Dama Mommy Ammie ce ta ce. In zo in ɗauki Afnan in kaita gidan wata aminyarta da take saro kaya daga dubai don ta zaɓi wanda take so. Yau aka buɗe kayan kar a zaɓe. Shine nake so in ba damuwa ki bamu izini in je in kaita."
Murmushi Mommy ta yi. "Haba Yazeed kai da matarka har sai na yi ma izinin ɗaukarta? Allah ya tsare a dawo lafiya. Bari in shiga ciki. Ke kuma ki tashi ki je ki shirya ka da ki ɓata masa lokaci"
Tana kaiwa nan ta yi masa sallma ta haye sama.Dakyar Afnan ta samu ta miƙe ta shiga ɗaki saboda yanda ƙafafuwanta suka yi mata nauyi.
Bata wani ɓata masa lokaci ba. Ta shirya cikin baƙar jallabiya, ta yane kanta da mayafinta. ba kara min kyau ta yi ba cikin ba ta yi makeup ba powder kawai ta shafa sai kwalli. sai ta fito tamkar wata balarabiya.
![](https://img.wattpad.com/cover/95453973-288-k589738.jpg)