Babi na araba'in da biyar

577 50 5
                                        

Bai damu da ganin ɗakin  tsaf tsaf ba kasancewar  yasan ko da yaushe Ammie na ƙoƙarin ganin a gyara shi ko ba kowa a ciki.

Direct bedroom ɗin shi ya nufa ba tare da ya kawo komai a ransa ba.

Afnan na zaune ta yi nisa cikin tunanin da take yi ta ji motsin an shigo ɗakin.

Magana ta fara yi saboda a ɗaukarta Hafsa ce  ta shigo saboda ita ce ta fita bada daɗewa ba dan ta kawo musu abinci, kasancewar koda yaushe suna tare a ɗakin. Bacci kaɗai ke rabasu saboda ita  Hafsar ɗakinta take kwanciya a cewarta ba za ta iya kwana ɗakin na Yazeed ba saboda Air condition ɗin ɗakin ya mata sanyi sosai.

Abubuwan dake cikin ranta da yanda shauƙin ƙaunarsa ke bijirowa zuciyarta ta ke so ta samu ta gayawa wani ko wane ne. A hankali take maganarta muryarta ɗauke da wani sauti maigirma.

"Hafsat wallahi ina tsananin son  Ya Yazeed  kasancewar shi inuwa mai sanyi a gareni a dukkan lokacin da nake muradi.

Ya kasance wani babban jarumi a duniyata da ba zan taɓa iya mantawa da shi a duniyata ba. Ya kasance mai sanyani farin ciki da nishaɗi a ko wane sa'i.

Sautin muryarsa na kawar da dukkanin damuwar da ta addabi zuciyata"

Murmushi ta yi ba tare da ta damu da shirun da ta ji ba ta cigaba da maganarta.

Tun ban san ina ƙaunarsa ba murmushinsa ke matuƙar sanyaya duniyata.

Kyawawan halayensa su ne kan gaba wurin janyo dukkanin soyayyata a garesa, ba tare da tunanin komai ba na miƙa masa ragamar rayuwata da duniyata baki ɗaya.

A ko wace safiya idan na buɗe idanuwana da kyawawan sakunansa,  su kan zauna a cikin tunanin har yammaci.
A gareni ya kasance wata babbar tsoka a cikin jikina da ke sarrafa jini da tunani zuwa ga ƙwaƙwalwa.

Idan zuciyata ta buga ki gaya masa ba kowa a cikinta face shi dan Allah." Ta ƙarashe Maganarta tare da ɗora hannunta kan zuciyarta da take jin bugunta na tsananta mata.

Ƙamshin turarensa da ya game ɗakin bai sa ta yi tunanin komai ba saboda ko da yaushe yana nan tare da jikinta.

"Tabbas mu kan samu saɓani a tsakaninmu  saboda harshe da haƙora ma wani lokaci su kan saɓa a tsakaninsu. Sai dai hakan bai taɓa kawo nakasu a cikin soyayyarmu, ba. Muna fahimtar juna ga dukkanin matsalolinmu, muna kuma bawa juna uzuri a laifukkanmu.
Amma Hafsa me yasa wannan karon Ya Yazeed ya k........."

Maganar da ta ji ce ta katse duk wata kalma dake ƙoƙarin fitowa ga bakinta.  Idanuwanta ta buɗe ta waresu kan fuskarsa tare da ware kunnuwanta sosai tana sauraren kalamansa.

"Bravo alaiki." Ya faɗa yana mai jifarta da wani kallo mai tsorata duniyarta da dagula lissafin rayuwarta.
"Tabbas kin cika babbar marasa kunya da har za ki iya dubin  kanwata ki riƙa gayamata waɗan nan kalamai naki na yaudara, wɗanda aka shiryasu domin wanin ɗan uwanata"

Wani maiƙo take hangowa a gefen idanuwansa da ya ƙara firgita tunaninta.

"Ban taɓa tsanar sunana ba saida kika shigo cikin duniyata. Babbar nadamar da na taɓa yi a rayuwata da kika zamo a bar yarda a gareni.

A duk lokacin da na tuna Amincin da zuciyata  ta baki ba tare da amincewar wasu sasa na jikina ba nakan ji  baƙin ciki ya na mamaye zuciyata.

Da lokacin baya na same waɗan nan kalamai daga gare ki da bansan babban matsayin da zuciyata zata ɗora ki a kai ba. Amma yanzu da na san ko nawaye sai na ji na ƙara tsanarki fiye da yanda na tsaneki a baya."

Yana kaiwa nan ya yi saurin nufar wardrobe ya buɗe tare da ɗuakar  wata briefcase ya juya ya bar ɗakin da sauri yana jin wani irin abu na game dukkanin zuciyarsa da kuzarinsa.

Afnan kuwa haka ta yi zaune ba tare da ta iya yin wani  ƙwaƙƙwaran motsi ba. Kalamansa take ta ɗorawa a ma'auni amma ta kasa gane ta inda suka dosa.  Sosai tunaninta ya yiwa duniyarta girma zubewa kawai ta yi kan gado tana fidda ƙwalla mai matuƙar bata wahala a ƙasan zuciyarta.

Shi kuwa ikon Allah ne kawai ya kai shi gida. Yana isa ɗaki kawai ya faɗa ya ɗauko wayar Afnan da ke hannunasa.
Chargy ya jona wayar saboda tun ranar da abun ya faru yake tunanin wayar ta dauke.
Ba komai yasa ya sanya wayar chargy ba sai dan ya kaima Ammie ta ga abunda Afnan ta aikata a gareshi ko zata  ba shi damar ya sauwaƙe mata ya huta da wahalar da zuciyarsa take ciki.
Wai me ma yasa zuciyarshi take tausayinta ne maimakon ta tsaneta kawai? Me yasa ya kasa sanarda wani abunda ta yi masa?
Sosai yake yaƙi da abunda zuciyarshi take yi mishi a kanta. ya fi so zuciyarsa ta tsaneta tsana mafi munin da zata ji shakkar ko kusantar in da yake da tsawon kilometer dubu. Sai dai kash ba zai iya ba.
Yana yi mata wani irin so ne wanda shi ke sanya  duk lokacin da ya yi yunƙurin nunawa Ammie wayar sai ya fasa. Baya so kowa ya tsaneta sai shi.

kwanakkin da ya yi ba tare da ita ba suna cikin kwanakki mafi wahala a duniyarsa. Saboda shi kaɗai yabsan irin azabar da ya ɗan ɗana.

Yanzu kam ya ɗau alwashin nunawa Ammie saƙwannin da ke wayarta ko zai samu sassaucin zogin da zuciyarshi take yi mishi idan ya tuna da har lokacin tana cikin ikonsa.

haka dai  ya yi ta saƙe saƙe har bacci ya yi awon gaba da shi.

Ba shi ya tashi ba sai ƙarfe shiddan safe. ba ƙaramin mamaki ya yi ba da ya samu wannan baccin haka mai yawa. Cikin gaggawa ya tashi yabyi wanka ya yi arwala ya yi sallah.

Bai wani ɓata lokaci ba ya shirya saboda  jirginsu ƙarfe takwas ne na sage. wayar da yasa chargy ya cire sai dai maimakon ya sanya ta a jaka sai ya ajiyeta ya saka charger gurin sauri.

Gidan Ammie ya nufa dan ya yi mata sallama, ya kuma nuna mata wayar dan ya ji hukuncin da zata yanke.

Idan ta bashi damar ya sake Afnan sai ya saketa kafin ya wuce.

Falke ya samu Ammie bayan sun gaisa ne ya bude jakar don ya nuna mata sakkonnin  wayar  ya ga charger ce ya saka ba wayar ba.
Tsaki kawai ya yi tare da yima Ammie bankwana yana mai sake jaddada mata cewa da ya dawo zai rabu da Afnan.
Bata ce masa komai ba sai fatar dawowa lafiya da ta yi mishi tare da raka shi har gurin mota ta koma cikin gida.

Afnan kam tun lokacin da Yazeed ya bar gurinta ta shiga wani mawuyacin hali.
Duk ta yi baƙi ta rame ko yaushe cikin damuwa take.  Ammie kuwa ko yaushe cikin ƙoƙarin bata  bata ruwan zam zam da aka tofe da adduo'i na karya sihiri take yi.

Su Mamie kuwa  shirye shiryen biki kawai suke da neman hanyar da Yazeed ɗin zai rabu da Afnan dan yanzu sun riga sun san cewa bai saketa ba.

Wata ƙanwaarta ta kira Aina'u kasancewarta shahararriya gurin shiga bokaye da malamman tsibbo. Anty aina'u ta tabbatar ma mamie za ta iya  ganinta ko wane lokaci don suje Ilorin gurin wani bokanta.
(Ta Allah ba taku ba ehe)

Vote
Comment
Share and follow me on this @ayshartfarouq

Yazeed ko YaseerStories to obsess over. Discover now