Babi na hamsin

707 78 14
                                        

Kasancewar kan titin da officien yan sandar ke kai ne abun ya faru nan take su Yazeed suka gano cewa Yaseer ne tsautsayi ya faɗawa.

Tun a nan wurin Yazeed ya fara ba shi taimakon gaggawa har suka isa assibiti, in da anan ma sai da aka nemi jina. Ba ɓata lokaci Yazeed ya bada jininsa saboda ganin yanda Yaseer ɗin ya zubar jini da yawa a jikinsa.

Sosai Mamie ke kuka tana nadamar abunda ta aikata ga rayuwa ƙwaya ɗaya da ke ƙoƙarin taimakonsu a lokacin da duniyar nan ta juya masu baya.

Yazeed bai bar assibitin ba sai da ya ga komai ya kammala, sannan ya yi masu sallama tare da basu tabbacin zai dawo dan sake duba jikinsa. Daddy ma ba a barsa baya ba ya yi iya ƙoƙarinsa kan yaron sai dai ko wurin da Mammie take bai kalla ba haƙurin da take basa ma cewa ya yi idan ta ƙara yi masa magana bakin sauran igiyarta ɗaya, ba shiri ta kama bakinta tana ji tana gani har ya bar gurin sai dai kallo.

Misalin ƙarfe takwas na dare Yazeed na zaune gaban Ammie yana mata magiya kan tabarsu su koma gidansu tunda komai ya riga da ya wuce, ganin kamar bata da niyar cewa ya ɗauki matarsa su tafi.

Ganin yanda yake so ya sanya mata kuka dan tace ba yanzu Afnan ɗun zata koma ba ya sa ta ce.
"Ni ba wai naƙi barinka ka ɗauke matarka ku koma ba  ne ni babban abunda nake jiwa tsoro bai wuce kar wani abu ya same ɗiyar mutane ba. Ka dai san halin Zuwaira sam ba ta da imani za ta iya biyar bayan fage don ganin ta ɗauke fansar abunda ya faru"

"Ba wani abu da zata iya yi Ammie saboda an riga da an yi yarjejeniya da su a court.  kuma wlh Ammie idan kika ganta za ki tabbatar da ba ƙaramar nadama ta yi ba saboda she is  helpless, ganin halin da Yaseer yake ciki.  Ni wallahi har tausayi take bani yanda ta zama lokaci ɗaya.

Taɓe baki Ammie ta yi tana jinjinawa halacci irin na Yazeed cikin mutuwar jiki ta ce.
"To Allah ya sa dai har cikin zuciyarsu sun yi nadamar. Dan ai dama haka muke fata. Addu'a ta dai ɗaya ce Allah ya ganar dasu idan suna da rabon ganewa"

Ci gaba ta yi da magana.
"Dama ni ba riƙe maka mata zan yi ba tun da ita da ka yiwa laifin ma ta yafe ni meye nawa. Zaka iya ɗaukar matarka ku tafi gida duk randa kake buƙata fatana dai Allah ya kauda fitina tsakaninku. Sannan a riƙa nesa nesa da zuciya, a riƙa bincike kafin yanke hukunci. Allah ya yi maku albarka dukan ku"

"Ameen Ammie." Ya faɗa tare da
rungume ta yana jin tamkar ya fi kowa sa'ar uwa ta gari a duniya.

Ɗakinshi ya nufa dan ya huta saboda yanda yake jin yanayin jikinsa. Tabbas tana buƙatar hutu sosai duba da irin stress ɗin dake tare da shi tun jiya.

Ko da ya shiga Afnan har ta yi bacci saboda magungunnan da ya rubuta mata harda na bacci. Saboda ita ma tana buƙatar hakan dan lafiyarta.

Saida ya rusuna ya mata kiss a goshi, sannan ya shiga bayi ya yi wanka ya fito, sai da ya shirya cikin kayan baccinsa yasha maganin ciyon kai, sannan shima ya bi lafiyar gado ya kwanta tare da janyota jikinsa ya ƙanƙameta sosai yana ajiyar zuciya.

Cikin ƙanƙanen lokaci bacci mai tattare da nutsuwa ya kwashe sa.

Wansahake ma da wuri ya fita saboda wayar da ya yi ta samu daga wani likita kan falkawar Yaseer da kuma rigimar da yasa kan sai sun sallamesa ba zai iya zama assibitin ba.

Sanar da Afnan kawai ya yi cewa ta shirya dan da ya dawo zasu wuce gidansu.

Ko da ya tafi assibitin kasa haɗa ido da shi Yaseer ya yi saboda kunyar abunda ya aikata agaresa.

Sai lokacin da Mamie ke basa labarin abunda ya faru yake jin nadama na shigosa sosai na abunda ya aikata a ga Yazeed, shi ya sa ma ya dage da sai an sallamesa  dan ya tafi wani guri ya yi jinyarsa saboda sam ba zai iya ci gaba da haɗa idanuwa da Yazeed ba.

Yazeed ko YaseerTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang