Babi na talatin da takwas

577 58 4
                                    


  Sannu sannu bata hana zuwa sai dai a daɗe ba a akia ba. Yau har an fara bikin Yazeed da Afnan.

Sosai Biki ya kan kama. An yi shagulgulla masu ƙayatarwa.

kasancewar yau juma'a kuma yau ne ranar da ake mothers night  wanda Ammie ce da kanta ta shiryashi.

Amarya ta haɗu iya haɗuwa. Wani danqareren less ta sanya milk mai ratsen light blue acikinsa. Head ɗin da aka  ɗaura mata  ma light blue ne. Idan ka kalleta dole ne sai ka sake kallawa saboda irin haɗuwar da ta yi.

Shima ango irin shigarta ya yi. Ya sanya shadda light blue dinkin babbar riga kayan sun yi masa kyau sosai har sun gaji.

Bayan mota suka harɗe da shi da ita wani amininsa na jan motar.

Hannunta ya kama da yasha kunshi, ya sumbata.

Ƙasaƙasa ya yi magana yanda ita kaɗai zata ji.
"Amaryata kin yi kyau sosai har sai sai na ji kamar kar mu je mothers night ɗin nan"

Murmushi ta yi mai ƙawatarwa.
"Akan me za mu fasa zuwa bancin don mu kawai aka shirya sa?"

"Ina kishin wasu maza su gane min  wannan kwalliyar taki shi yasa na ce event ko daya maza ba za su je ba. Ni na fi so ingan ki ni kaɗai ni da na mallake ki. Kin san ina da kishi sosai kan abunda ya zama nawa ni kaɗai musanma ma kanki Afnan"

Hancinshi ta ja.
"Am all yours Ya Yazeed, so karka kawo komai a ranka.

Ya ji daɗin kalamanta sosai. Ja mata hanci ya yi shima yana maƙale kafaɗa.
"Uhmuhm! Ni dai ba zan yarda ba mu koma gida kawai"

Dariya ta yi saida fararen haƙoranta suka bayyana
Kafin ta yi magana ta ji mota ta tsaya alamar sun iso gurin.

Ba ƙaramin haɗuwa gurin ya yi ba. Wasu ƙananan yara ne da suka sha gyara suka zo suka take masu baya suka shiga ciki.

Ba a wani ɓata lokaci ba aka fara ƙaddamar da program ɗin.

Nan aka buƙace ango da amaryarsa da su fito su yi rawa. Ba wata rawa suka yi ba dan sam Yazeed ya hanata shaƙat.
Sunsha ɓarin nera gurin yan uwa da abokan arziki. Ranar idan ka ga Ammie ba za ka  taɓa cewa ta haifi kamar Yazeed ba saboda kwalliyar da tasha.

Zuwan su Mamie ne ya ɗan tada hankalin Afanan. Saboda kallo ɗaya da ta yi wa matar ta gane ko waye ita saboda tsantsar kamarsu da Yaseer.

Mamie da kanta ta neme m.c da ya kira mata amarya da ango su sake fitowa. Ai kuwa da suka fito nan ta ɓare bakin jaka tana ta ruwan kuɗi.

Mawaƙa sai ƙara wasata suke yi. Suna yi mata kirari na uwar ango.

Yaseer kam Afnan ya shiga yiwa liƙi tamkar ba gobe. Abinda ya yi matuƙar ƙona zuciyar Yazeed.

Nabeela ma  ta shiga liƙawa Yazeed. Amma hankalinshi sam ba ya kanta. Idanuwanshi sun rufe sosai  da tsananin kishin Yaseer.

Ita kanta Afnan ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba. Saboda ganinshi a yau ba ƙaramin haifar mata da wasu abubuwa ya yi ba a zuciya.
Ba ma kaman yanda ta ga yana nema ya shiga cikin jikinta.

Wani kallo yake yi mata mai tattare da wasu manufofi da shi kaɗai ya barwa kansa sanin su. Wani mayaudarin murmushi ne ɗauke a bakinshi lokacin da ya ɗan rankwaɓo gurin kunnenta ya na yi mata magana.

"Kar ki ɗauka na haƙura da ke dan ganin na wofantar da lamurranki tsawon wani lokac ba tare da na neme ki ba. Ki sani ina nan tare da ke ina ganin duk wani motsi na ki a zuciyata.

Ina so ki riƙe wannan a ranki cewa. Ba wanda ya isa ya mallakeki matuƙar ina raye idan ba ni ba.

Na san ni kike so kuma nine zaɓin zuciyarki, dan haka ki sa ranki cewa  the game is just the beginning. Na barki lafiya sai mun haɗu a gida gobe" ya ƙarashe maganarsa tare da sakar mata wani  shu'umammen murmushin da shi kaɗai ya san ko na miye.

Yazeed ko YaseerDonde viven las historias. Descúbrelo ahora