Babi na sha uku

580 41 0
                                        


         
             
Kasancewar yau asabar dukan su suna falo.
Afnan da ba wani karfi ne a jikinta ba tana kwance ta dora kanta kan cinyar mahaifiyarta, kallo ɗaya zaka yi mata ka gane cewa tana cikin matsala saboda yanda ta  ƙara haske ta rame tayi fau da ita, zaman da ta yi ma aman tagama.
Ciyon kai kam ba a cewa komai dan ya zame mata tamkar kadangaren bakin tulu, idanuwanta ma bata iya bude su sosai saboda azabar da takeji.

Da sallamar shi ya shigo falon wadda ba ma kowa ya jita ba sai mai kaifin ji irin Abba. Kallo ɗaya zaka yiwa Ibrahim ka gane baya cikin hankalinsa sam. Wuri ya samu ya zauna jikinsa ba ƙwari sai gumie ke keto masa.
"Lafiya ka shigo haka kamar wanda aka yiwa mutuwa" cewar Mommy tana kallonsa.

Bai ce komai ba ya saka hannu cikin aljihunsa ya zago takardar da ya amso gurin test ɗin da aka yiwa Afnan jiya.
Abba ya miƙawa ba tare da ya ce komai ba.

"Meye wannan kuma" Abba ya faɗa ba tare da ya warware takardar ba.

"Gwaje gwajen da aka yiwa yarinyar nan ne" ya faɗa ba tare da ya kalle kowa ba.

Nan take ƙirjin mutanen falon ya buga saboda jin yanda ya yi maganar.

Cikin azama Abba ya soma warwarewa yana karantawa.

"Wannan ai ba na Afnan ba ne naga kaman na maijuna biyu ne" cewar Abbab idanuwansa kan Ibrahim.

"Abba nata ne Ina office doctor harun ya kai min yace in kawo maka"

"He will be mistaken am very sure ya faɗa jikinsa na ɗan kakkarwa"

"Wallahi Abba nata ne AFNAN NA DAUKI DA CIKI NA WATA BIYU"

" innalillahi wa'inna ilaihirraji'un" ce kawai kalmar da ke tashi cikin ɗakin yayin da zuciyoyi da yawa suka raunata.

"Kin cuce ni Afnan kin cuce tarbiyyar da na baki"
Abinda Abba ya iya faɗa kenan yana dafe da zuciyarsa saboda wani irin zafi da take mishi.

Tsaye  Mommy ta miƙe  batare da ta san lokacin da ta mike tsayen ba, tana nanata taslima.
Ganin haka yasa itama Afnan ɗin da ta yi mutuwar zaune  miƙewa  tana wani irin kuka mai ban tausayi. Sagir  da ke kokarin shigowa dakin  tsaye ya yi chak tamkar Wanda ruwa suka cinye yana biyar ahalinsa da kallo.

Cikin tsananin tashin hankali Abba yayo kan Afnan ɗin yana fadin.
"kin cuce ni Afnan kin wargaza min tsari, kin tuddamin mutuncina kin............"
Bai ida fadi ba ya faɗi ƙasa warwas saboda bugawar da zuciyarshi ta yi lokaci ɗaya.

Mommy dake tsaye sai lokacin hawaye suka zubo a idanuwanta. Da gudu ta yi kan Abba tana kiran sunansa.
Kan shi su ibrahim suka yi da Sagir da ke tsaye bakin ƙofa. "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un" dukan su ke faɗa.

Afnan ma cikin tashin hankali ta matsa kusa da shi tana fadin,   "wlh Abba  ba laifina ba ne fyade ya yi min wlh fyaɗe........"

Marin da Ibrahim ya ɗauketa da shi  ne ya sanya ta katse maganar da ta ke shirin yi.
"Kika kashe mana uba wlh kema sai na kashe ki" ya fada cikin goshewar hankali da tunani.

Daƙyar suka samu suka kamashi shida Sagir suka saka shi mota.

Emergency aka nufa dashi ba ɓata lokaci aka bashi taimakon gaggawa. Cikin ikon Allah aka samu kanshi.

Zuwa lokacin duka suna Assibitin har Afnan da driver ya kawo.

Lokacin da Abba ya falka ba abinda ya furta face "na yafeki Afnan har abada kin fita daga cikin zuri'ata" waɗan nan kalaman ba ƙaramin tayarwa Mommy da hankali suka yi ba.

Afnan kuwa tun da ta ji kalaman Mahaifinta take rusar kuka tana fadin ba laifinta ba ne fyaɗe ya yi mata. Ganin tana so ta ƙara rikita al'amarin yasa aka izo ƙeyarta waje. Nan bakin kofar ɗakin ta yi zaune tana kuka.

Sai da aka sake yiwa Abba allurar bacci sannan suka fito daga ɗakin.

Ajiyar zuciya Ibrahim ya yi yana kallon Mommy da ta bala'in fita hayyacinta.  Tausayinta yake ji har cikin ransa kasancewarta uwa mai rauni amma duk da haka tana ƙoƙarin jurewa.

"Miye mafita kan Afnan Mommy? Nasan  yana da wuya Abba ya bari ta zauna masa gida"

Momy ta dube shi cikin damuwa ta ce.
"Naga kamar tace  fyade ya yi mata, inaga kaman abun zai zo da sauƙi idan haka ne. Yanzu abinda ya dace kawai  aje a same yaron a gaya mishi idan ma ta kama a shiga kotu sai a  shiga, ni zan tsaya mata ko da mahaifinku ya ƙi dan ganin  an fitar mata da hakkinta"

Shawarar ta yi wa Ibrahim daɗi  shima.
waje ya sameta zaune rakube tana kuka
"Ke!"
Ya Kira sunanta fuskar shi tamke, 
Kallonsa kawai ta yi ba tare da ta ce komai ba.

"Uban wa ye ya miki ciki? Kuma ki ka min karya wlh yanka ki zan yi, kina ji na ko?" Ya fada tamkar zai daketa.

Saida ta fyace majina sannan ta yi magana.
"Yazid ne kuma wlh fyade ya yi min"

"Da ya miki fyade me yasa ba ki fada ba?"
Ya sake fada a hasale.
Shiru ta yi ta kasa cewa komai sai uwayen hawaye da ke fita a idonta.

"Kin san gidan su Yazid ɗin?" Ya faɗa yana ɗan rage sautin muryarsa.

Gyada mishi Kai ta yi,
"Eh na sani"

"Ok tashi mu je ki kaini ingan shi" ya faɗa yana mai juyawa

Ita ma ba ta yi gardama ba ta miƙe ta mara masa baya.

Mommy tace lallai itama sai ta bisu.
don tafi son ayi komai gaban idonta. ba yanda Ibrahim bai yi ba don ta tsaya  gurin Abba ta ce ita alan balan sai taje sai dai Sagir ya tsaya tare da shi.
Ba yanda ya iya dole suka tasa Afnan gaba har gidan su Yazid din.

Yazeed ko YaseerDonde viven las historias. Descúbrelo ahora