Ganin yanda take Kuka ne yasa Ammi ta dafa kafadarta.
"Ki yi shiru 'yata ki daina kukan hakanan kada ki sake sanyawa kanki wani ciwo"
Ɗago idanuwanta ta yi da suka rine sukayi jajur ta dube Ammi tare da dafe zuciyarta,
"Ciwo duk ya fi wannan da nike ji a zuciyata? Wallahi mama bana tunanin akwai ciwon da ya fi wanda nakeji a halin yanzu""Uhum! Nasan yanda kike ji amma ki sani duk abunda ya yi tsanani maganinsa Allah, duk abunda haƙuri bai yi ba rashin sa ba zai yi ba"
Wani kallo Afnan ta yi mata na baki san yanda nake ji ba.
"Shekara ɗaya ban San true identity dinsa ba. Ya shigo rayuwata ne kawai saboda ya yaudare ni ya rabani da mutunci na. Mama ya rabani da iyayena da 'yan uwana ta yaya ba zany i kuka ba? Ki gaya min mama ta yaya dan Allah" ta faɗa murayarta na nuna tsantsar gajiya da yanayin da take cikinsa.Sosai Ammi ta tausaya mata matukar tausayawa. Kallonta ta yi ta ce.
"Zan taimaka miki in dawo miki da duk abunda ya rabaki dasu matukar kika gaya min gaskiyar lamarin ki""Harda mutuncina zaki dawo min dashi?" Afnan ta tambaya da sauri.
"harda mutuncinki, idan baki yi min ƙarya ba"
Ammi ta bata amsa kai tsaye.Murmushi Afnan ta yi a karo na farko da ta samu kanta cikin wannan matsalar.
Bayan hannuwanta ta sanya ya shafe hawayen da ke zuba a idanuwanta kafin ta soma ba Ammi labarin duk abunda ya faru da ita tun farkon haɗuwarsu da yaseer har zuwa wannan lokacin.
Kuka sosai Ammi ta yi, ita da Afnan ba mai lallasar wani. Sai da suka yi mai isarsu suka gama sannan Ammi ta soma magana.
"Amma gaskiya yaseer ya yaudare ki Afnan, ni tunda ma nake duniya ban taɓa jin yaudara irin wannan ba" Ammie ta faɗa tana mai jin ɗacin abun da ko ba komai ta fara hango abunda take so ta gani na lalata mata sunan yaro da ake yi.Haka suka raba dare suna fira Ammi na ƙara bata hakuri tare da shawarwarin da take ganin za su amfaneta.
Tunda suka koma gida ya kasa zaune ya kasa tsaye, bacci baki ɗaya kasa yin shi ya yi, sosai ya rasa takamammen abunda ke damun sa. Haƙiƙa da ba don gudun fushin Daddy ba da ba yanda za ayi ya karyata abunda Afnan ta ce tunda ya san shi ya aikata. Sai dai yanzu is to late ba zai yarda ya yi losing trust ɗin Daddy akansa ba.
tabbas sai yanzu ya yarda da ba sha'awar Afnan kawai yake yi ba harda kaunarta yana yi kuma kauna mai tsanani. Toh yanzu ya zai yi?
Wata zuciya ta ce, 'kawai ka sameta ku yi magana zata rufa ma asiri ta aure ka tunda tana son ka'.
haka dai ya yi ta saƙawa da warwarewa har garin Allah ya waye.Yazeed kuwa ya rasa dalilin da yasa take yawan fado masa a rai. Sosai yake jin tsanarta saboda irin ƙaryar da ta yi masa gaban idanuwansa. Sosai yake so ya ɗauki mataki saboda tura ta riga ta kai bango ba zai sake lamuntar wata ta sake lalata masa suna ba.
Tunda ya tashi guraren ƙarfe takwas ya shirya zuwa aiki saboda yanada appointment din safe a Assibitin.Yana saukowa ƙasa ya ci karo da Daddy da Yaseer. Cikin ladabi ya gaida Mahaifin nasa.
Bai ko kalle inda Yaseer yake ba ya sa kai zai wuce Daddy ya yi saurin cewa.
"Dama kai nake jira baka ga kirana a wayarka ba ne?"
"Lafiya dai ko?"
Yazeed ɗin ya tambaya ba tare da ya amsa ma Daddy tambayarsa ba.Daddy bai damu da yanda ya yi masa ba ya ce
"Lafiya lau. Yarinyar jiya dai nake so ku kaini gurinta, saboda in kara tambayarta don ban san abunda zai je ya dawo kar a ɓata min siyasata." Ya faɗa kansa tsaye."Kuma ina so in San dalilinta na zuwa gidana kaɗai duk faɗin unguwar nan ta ce an mata fyade. Idan ma turota aka yi zata yi bayani ku kira yayan nata dan ayi komai a gabansa" ya faɗa yana gyara babbar rigarsa tare da wucewa gaba ya barsu cirko cirko.
Baki ɗayan su hankalinsu tashi ya yi kowa da a binda yake tunani, bama kaman Yazeed da yake ganin tamar shi zata sake lakawa tunda at the first place shi tafara cewa. Kuma shi aka yiwa shaidar ɓata yaran mutane amma ba a taɓa kawo case ɗin fyade ba saboda girmansa da muninsa.
Yaseer kuwa har wani gumi ke taso masa ganin yake daga asibitin ma Daddy zai kore sa daga gidansa idan dai har yarinyar can ta faɗi gaskiya.
Kiran Ibrahim Yazeed Ya yi ya gaya masa abunda Daddy ya ce. Ibrahim bai ji daɗi ba saboda ya so a kashe case ɗin tunda an gano cewa ƙarya ce kai ta yi masu. Sam baya son abun nan yafita waje har yakai ga police. Sai dai ba yanda ya iya dole ya ce su haɗu a assibitin.
Da isar su assibitin, direct ɗakin da Afnan take suka nufa. Daa sallama suka shiga, kallo ɗaya Afnan ta musu ta dauke kai saboda wata irin faduwar gaba da ta ji ganin yanda suka shigo ɗakin.
Gabanta ya shiga dukan uku uku ganin fuskar mahaifin na su. Wani Abu ta ke jin yana ta so mata yana tokare mata zuciya. 'anya zan iya abunda Ammi ta ce kuwa?' ta faɗa cikin zuciyarta.
Sallamar Ibrahim ce ta dawo da ita daga tunanin da take yi.
Hankalinta ba ƙaramin tashi ya yi ba ganin yanda fuskarsa take tamkar ba yayanta da tasani ba mai kaunarta ba.Har ƙasa ya rusuna ya gaida Daddy da Ammi, sannan ya bawa Yazeed da Yaseer hannu suka gaisa.
Ko kallon gefen Afnan bai yi ba saboda yanda yake jin haushinta cikin ransa."Ya jikinki, da fatar kin samu sauƙi?" cewar Daddy yana jin ɓacin ran da ya fito da shi daga gida yana narkewa ganin innocent face ɗinta.
"Naji sauki Alhamdulillah" ta faɗa tana kallon Yazeed da gefen idanuwanta.
"Masha allahu haka muke so. Dama ba komai ya kawo ni ba face ina so ki sake dubin girman Allah ki gaya min gaskiya waye ya miki fyaɗe a cikin yarana"
Kamar ta tambayesa idan ta faɗa zai bi mata hakkinta ne sai kuma ta yi shiru tana kallon Ammie da tun shigowar su kanta ke duƙe ƙasa tana jan charbi.
Kamar Ammie ta san ita take kallo ta ɗago kannta suka hada ido. A hankali ta girgiza mata kanta alamar kar ta ce komai.Wasu sirarran hawaye ne suka fito a idanuwanta. 'Me ammi ke nufi da ta ce kada ta faɗi alhali ga dama ta samu da zata wanke kanta'
Wata zuciya ta ce 'ki yi mata biyayya tunda ta haife ki Abunda babba ya hango yaro ko ya hau tsani ba zai hango ba, tun da ta san ba ɗanta ya yi ba kuma tace ki rufawa wanda ya yi asiri ƙila akwai abinda baki sani ba a kasa'"Ina jinki, kar kiji tsoron komai ki gaya min gsky kin ji?" Daddy ya faɗa yana kafeta da idanuwa.