Yau Assabar kuma yau ne su Abba za su zo. Kallo ɗaya zaka yi wa Afnan ka gane cewa bata cikin nutsuwarta. Duk ta bi ta dabirce motsi kaɗan zata ji sai gabanta ya faɗi.
Ammi na lura da ita, ta kawo ido ta zuba mata. Ta barta da dabararta, saboda ita harga Allah ba ta son ta takurawa Afnan kan zaɓin zuciyarta. Faranta kawai Allah ya saɓa mata miji na gari wanda zai so ta ya kuma kare mutuncinta. Amma har ga Allah ta yi wa Yazeed sha'awarta sai dai ba yanda ta iya.
Su Abba ba su iso gidan Ammie ba sai bayan la'asar. koda suka zo tuni Yazeed da Yaseer sun garzayo suma saboda dama Abba yasa a ayi kiransu matsayin su na shaidu.
Zaune suke babban falon Ammi dukan su.
Bayan anƙare gaishe gaishe Abba ya kalle Ammi ya ce.
"Yau dai na zo karɓar alƙawarina gurin ƴarki da fatar baku manta ba?"
Murmushi Ammi ta yi. "Ba mu manta ba saboda ƴata ƴar halar ce ba zata baka kunya ba".
Ammi ta faɗa tana kallon Afnan da gabanta ke dukan uku uku.
Kallonta Abba ya yi "ina jin ki wa kika tsaida matsayin wanda kike so Kuma a ina yake, waye mahaifansa?
Ba Afnan ba, duk da da Yazeed da Yaseer saida suka same kansu da Faɗuwar gaba duk da cewa cikin su kowa ya san makomarsa a wurinta.
Ruɗewa Afnan ta yi bakinta sai kakkarwa yake yi ta kasa furta komai.
"Da ke nake magana" Abba ya daka mata tsawa yana zare mata idanuwa."
Maida dubanta ta yi gun Yaseer da Yazeed da suke zaune guri ɗaya duk sun zuba mata idanuwa. sake maida kanta ta yi ƙasa tare da furata.
"Ya Yazeed na tsaida matsayin wanda zan aura"
TASHIN HANKALI GOBARAR GEMU.
Wani irin zufa ne ya ketowa Yaseer tun daga kansa har zuwa yatsun kafafuwansa na k'afa. Idanuwansa take suka ƙanƙance har wasu ruwa ruwa kake gani na tashin hankali a ciki.
Shi kansa Abba bai gasganta abunda ta ce ba sai da ya sake tambayarta.
"Shin wane Yazeed kike nufi, shi wancan ɗin da ya ce ya fasa auren ki ko kuma wani daban?" Ya tambaya fuskarsa ɗauke da mamaki.
Nuni ta yi da Yazeed ɗin da ya shiga shock saboda ko alama bai yi tunanin jin abunda ya ji a gareta ba.
Ammi kam bakinta ƙin rufuwa ya yi saboda tsantsar farin ciki.
Cikin wani yanayi Abba ya dubi Yazeed "kana da masaniya game da abunda Afnan ta faɗa ko kuma ƙaryarta ce da ta saba yi wa mutane?."
Murmushi ya yi tare da sosa ƙeyar kansa. "Eh Abba ina da masaniya" ya faɗa kansa a ƙasa.
Ganin Abba ya kalle Ammie da alamar tuhuma yasa ta yi saurin cewa.
"Ai tun kafin ka yi mata magana suka daidaita kansu. Haɗi ne kawai na Ubangiji. Dama shi ya san abinda yasa Afnan ta shigo rayuwarmu"
Ba Yazeed ba dudda da Afnan saida ta kalli Ammie saboda jin abunda ta ce, wanda ko ba a faɗa ba ya yi wa su Abba daɗi kuma sun gamsu ɗari bisa ɗari, ganin yanda fuskokinsu duk suka washe da fari'a lokaci ɗaya.
"Masha Allahu amma na ji daɗin wannan abun sosai wallahi. Ai kowa na son ya haɗa iri da mutanen kirki da suka san darajar ɗan adam irin ku." Abba ya faɗa kafin ya juya gurin Yazeed ya ce.
"Gobe ka turo mahaifinka idan dai ba takura. Kuma ya zo da shirin karɓa maka auren Afnan dan insha Allahu cikin satin nan nake so na ɗaura mata aure ga duk wanda ta kawo min koda kuwa bashi da zarafi ne, ni zan tallafa masa"
"Aure fah ka ce Abba?" Afnan ta tambaya cikin tsananin mamaki.
"Tabbas abunda kika jiwa kunnenki haka ne. Dan da baki fito min ma da mijin ba da yau yau zan ɗaura miki aure ga duk wanda zuciyata ta aminta da shi"
Yaseer ta kalla. Sai dai da sauri ta janye idanuwanta saboda ba za ta iya kallon yanayin da yake ciki ba. Tausayinsa da soyayyarsa ta ji na neman su bijiro mata lokaci ɗaya.
Wani irin kukan da bata san dalilin yinsa ba ne ya kubce mata.
Yazeed kam lumshe idanuwansa kawai ya yi. Fuskarsa sam ba za ka iya cewa ga yanayin da take ciki ba.
Cikin dakiya ya ce. "Amma Abba da an ɗan ƙaramin lokaci daidai na shirya ko zuwa nan da wata ɗaya ne."
Murmushi Abba ya yi. "Kar ka damu auren kawai za'a daura idan yaso daga baya ko yaushe ka tashi sai ta tare."
Mommy dai bata ce komai ba. Amma da ganin yanayinta ka san tana cikin farin ciki marar misaltuwa. Haka Ibrahim da Sagir sosai zaka karance murna ƙarara a fuskokinsu. Ba kamar Ibrahim ma da ya san ko waye Yazeed.
Abba ya kalle Afnan. "Sai ki tashi ki kwaso kayanki mu wuce gida ko." ya faɗa tare da miƙewa yana ƙara yi wa Ammie godiya.
"Alhaji da zaka yi mana alfarma da ka bar min ita zuwa anjima sai in mayar ma da ita dai dai mun ida shirya wa"
Momy ta ce.
"Ayi haka kuwa Hajiya? Hidimar ai ta yi yawa ko wannan halaccin da kika nuna mana kaɗai ya isa a jin jina maki"
Murmushi Abba ya yi "Ba komai ga Afnan ɗin nan ko yaushe kike yi ra'ayi sai ki kaimuna ita, ai yanzu kuma an riga da an zama abu ɗaya"
"Naji daɗi sosai Alhaji Insha Allahu zuwa anjima zan kaita da kaina. Dama Hafsa nake jira ta dawo anjima sai in kaita kar ta tafi ta barni cikin kaɗaici. Gashi itama Hafsar tana ta yi min naci kar in bari Afnan ta je ba tare da ta ganta ba"
"Allah sarki Allah ya dawo da ita lafiya" suka faɗa.
Baki ɗayan su miƙewa suka yi suka fita bancin Yaseer da ya kasa gane ko a wace duniya yake ciki. Saboda jikinsa har wani cira yake yi saboda tsananin tashin hankalin da yake ciki.
Ba wanda ya kula da halin da Yaseer ɗin yake ciki sai Afnan da take satar kallonsa akai akai?
Bayan sun fita ne Yaseer ya samu damar janwo Afnan da ke baya.
Kofar da zata sadaka da guarding ɗin gidan ya turata da karfi.
Wata irin shaƙa ya yi mata, idanuwan nan nasa sun yi jajur tamkar garwashin wuta.
Wata irin kakkarwa Afnan ta riƙa yi tamkar zata shuɗe.
"You are hurting me Yaseer" ta faɗa tana ƙoƙarin ƙwatar kanta.
Bai saketa ba sai da yaga ya kusan illatata sannan ya wulgar da ita gefe saida kanta ya bugu da bango.
Nuna ta ya yi da yatsa.
"Wallahi baki isa ki wulaƙanta ni ba Afnan. Me na yi miki haka da zaki yi min irin wannan hukuncin? Kin fi kowa sanin yanda nake son ki Afnan me yasa zaki yi min haka?"
Duƙawa ya yi kusa da inda ya wullata tare da riƙa hannayenta.
"Dan Allah na roƙe ki da ki je ki warware wannan abun da kika ƙulla. Ki je ki gaya ma su ni kike so ba Yazeed ba"
Duk azabar da take ciki bai hanata ta ƙwace hannayenta da ƙarfi ba.
"Ba zan taɓa gaya masu ba mudddun ba ka je ka gayawa iyayenmu cewa, kai ne ka yi min FYADE ba.
Sannan kuma ka yi min ƙaryar suna dan ka yaudare ni, ka kuma ɓatawa ɗan uwanka suna. Idan ka yi haka na yi maka alƙawarin ba ni da wani namiji da zan aura sai kai, idan kuma baka iyawa am sorry to say kana gani zan zama matar waninka. Dan haka kana da daga yanzu zuwa gobe da safe".
Tana kaiwa nan ta miƙe ta zagaye sa za ta wuce.
Wata irin fisga ya yi mata.
"Baki isa ba wallahi. Kuma baki isa ki aure wanina ba. Ni kike so kuma ni zaki aura. ke me yasa ba ki da imani ne ba ki da yafiya Afnan?"
Wani irin murmushin rainin wayo ta yi.
"Rashin imani fa ka ce? Ai Ina ganin duk wani marasa imani yana bayanka Yaseer. kuma da kake cewa yafiya, ni ban san kalmar ba. kuma kamar yanda ka ce kai kaɗai nake so. Tabbas haka ne kai kaɗai nake so, amma ka sani ko da sonka zai kashe Ni ba zan taɓa aurenka ba muddun baka je ka faɗama Iyayenmu kai ka yi min Fyaɗe ba. Saboda wannan hanyar ce kaɗai hanyar da zan fanshe BUDURCINA a gareka. Sannan ita ce kaɗai hanyar da zata nuna min kana yi min sonbda kake iƙirari.
Tana kaiwa nan ta raɓa ta gefensa ta wuce tana sharar ƙwalla.
