Babi na talatin da biyar

558 43 2
                                    


   Misalin ƙarfe goma sha ɗaya na dare.  kwance take sai jujjuya dearyn dake hannunta take yi tana murmushi. Tunawa ta yi da randa ta tsince dearyn.

Wata rana Yazeed ya dawo daga asibiti, direct gidan Ammiensa ya wuce kamar yanda ya saba.
Koda ya je bai sameta gidan ba ta fita wurin harakar business ɗinta. Falon ƙasa ya zauna ya fitar da system ɗinsa yana aiki.

Lokacin ita kuma Afnan ta fito da niyar ta yi kallo ko za ta ragewa kanta kaɗaici. Tana fitowa ta samesa zaune nan falon yana ta aikinsa da laptop ɗinsa.

Gaida sa ta yi ya amsa ba yabo ba fallasa. Ganin sam ba za ta iya zama a wurin da yake ba yasa ta zagaya ta bayansa ta wuce saboda har zuwa lokacin tana kunyar abinda ta yi masa.

garden ta shiga. Ta daɗe ciki zaune saboda gurin na ɗebe mata kewa tare da sanyata nishaɗi. Saida ta ƙarshe zamanta sannan ta shiga cikin gida.

Ko da ta shiga falon ba ya nan sai ta zagaya ta inda ya tashi da niyar ta zauna. Ji  ta yi ta taka abu a ƙafarta. Dubawar da za ta yi sai ta ci karo da littafi ɗan k'arami mai shegen kyau.

Daukan littafin ta yi ta wuce daki dashi tana jujjuyawa sai kawai ta samu kanta da buɗawa. A yanda ta lura da pages ɗin littafin ko wane page colour da designing ɗinsa daban ne. Abun da yaja hankalinta kenan har ta cigaba da bubbudawa. Said da ta wuce kusan page biyar  sannan taga an fara rubutu a ciki.

Har ga Allah ta dauka littafin ba shida komai, sai da taga abunda ke cikin fifth page ne sannan ta fahimce ko meye a hannunta.

Ba ta karanta ba ta rufe littafin ta ajiye  tunda ta fahimce deary ne kuma bai kamata ta karanta sirrinsa ba tare da izininsa ba.

Ajewa ta yi da niyar idan ya zo ko Ammie ta dawo ta bata ta ajiye masa  sai Allah ya mantar da ita bata bata ba.

Ana gobe Mahaifinta zai zo don jin wanda ta zaɓa a matsayin mijinta. Lokacin ne ta shiga tashin hankali dan har zuwa lokacin zuciyarta bata yarda da shawarar da ta bata na ta bari Abbanta ya zaɓa mata duk wanda yake so ba. Har zuwa dare bata da wata mafita face ta auren wanda duk mahaifinta ya zab'ar mata saboda ko alama ba zata iya auren Yaseer ba a yanda take ji.

Bayan ta kammala nafila  da addu'ointa na neman zaɓin Allah ne ta ta fi ta ajiye qu'anin da ta yi karatu da shi, can idanuwanta  suka hango mata deary wajen ajiye Qur'anin.

Haka kawai ta ji zuciyarta na ingizata da ta karanta dan taga ko wace yarinya ce Yazeed  ya ke so da har yake jifanta da miyagun kalamai saboda kawai mahaifiyarsa ta ce ya aureta.  Ta san dolema ne ya sanya wadda yake so a dearynsa. Saboda mafi yawan deary na soyayya ne.

Ba ta wani ɓata lokaci ba ta ɗauka ta  fara karantawa. Sai dai har ta yi rabi ba macce a ciki. Amma abubuwan da ke cikin dearyn sosai suka taɓa mata zuciya. Tausayin sa ta tsinci kanta da ji na yanda yake rayuwarsa. Ganin abubuwan ciki na so su ƙara karya mata zuciya yasa ta ji ba zata iya ci gaba da karantawa ba. Har zata ajiye idanuwanta suka hango mata wasu pages masu kyau na kusa da ƙarshe. Bata damu ba kuma sai kawai ta buɗa.

Abunda ta ga an rubuta ne ya yi matuƙar ɗaukan hankalinta.

27 April 2017

LOVE AT FIRST SIGHT.

Dag Kallo ɗaya na tabbatar da rayuwata da duniyata duk zan iya mallakawa ga hallita ƙwaya ɗaya da ƙwayar idanuwana suka ɗora ganinsu a hallittar idaniyarta.

Ta tafi da dukkan tunani da ƙwazo na gangar jiki da zuciyata. Sai dai abun da ta zo da shi a wannan ranar abu ne da ya riƙa warware duk wani ƙuzari da jajarcewar da zuciyata take da shi game da bugun ta zuwa  gareta.

A lokacin itama na ɗauka an yi Amfani da ita ne kamar yanda aka riƙa amfani da irin jinsinta gurin ci min zarafi da ɓatan suna a gurin mahaifina.

Sai dai kalamanta da yanayinta sun nuna min cewa ta yi abunda ta yi ne kawai dan wata manufa tata ta daban.

Lokacin da Yayanta ya bar min ɗawainiyarta a assibiti nashiga ruɗa ni da tashin hankali na ganin yanda zuciyata ta azabtu da ita duk da kuwa akwai haushi da takaicin abinda ta aikata a gareni.

Duk lokacin da na yi arba da ita, zuciyata tana min ƙunci, ina jin kirjina tamkar zai fita saboda tsananin kishin da ke azabatar da ruhina game da ita. Na kasa yardarwa kaina cewa fyaɗe aka yi mata. Zuciyata ta kasa yadda da duk wani kalami da take ajiyewa a zantukkanta.

Zuciyata ko da yaushe tambayarta ita ce. Me yasa za ta baiwa wani namiji jikinta bancin akwai wata zuciya da zata fi son mallakar gangar jiki da ruhinta, ba tare da tozarci a gareta ba?. Me yasa ƙaddara bata fara haɗata da ni ba sai da wanda ya nakkasa mata rayuwa?
A duk lokacin da na tuna da wannan nakan ji tamkar in mutu inbar duniyarnan baki ɗayanta.

Ko da yaushe ina ƙok'arin ganin na yaƙuceta a zuciyata dan ganin na nuna mata tsananin tsanarta a fili. sai dai zuciyata takan ji zafi fiye da tata zuciyar. Zuciyata takan ƙuntata fiye da tata.

Ina jin tsananin soyayyarta da kaunarta mai tsanani duk lokacin da na yi tozali da ita. Tun randa na haɗu da ita ba wani dare da zan kwanta face na yi tunaninta dan samawa zuciya abincinta.

Meye gaskiyar lamarinta? Wannan ita ce kalmar da ko yaushe ke hanani tunkararta da baƙon lamarin da Zuciyata ke kwana ta tashi da shi.

Na barwa Allah komai  ga abunda zuciya, ruhi da gangar jiki suke muradin mallaka. Idan akwai alkhairi a ciki Allah yasa in samesa cikin sauƙin idan kuma ba alkhairi Allah ya nisanta duk wata halitta ta rayuwata a garesa.

Haka dai Afnan tayi ta karatu har takai ƙarshen dearyn kusan duk magangannun a kanta ne.  Ta yi kuka a lokacin har ta godewa Allah.

Tabbas ta san akwai wata fa'ida da ta sanya Yazeed ya yadda deary ɗinsa har ta ji tana kwaɗayin ta karanta.

haƙiƙa ta tabbatar da cewa Allah ne ya sanya zuciyarta jajircewa har sai ta karanta abunda ke ciki, ba don komai ba sai don ya taƙaita mata wahalarta. tabbas tasan Yazeed zaɓin Allah ne a gareta ko don jin da ta yi a lokacin  zuciyarta ta nutsu da shi ɗari bisa ɗari.

Wannan ne dalilin da yasa Afnan ta zaɓi Yazeed lokacin da Mahaifinta ya zo.

An dawo labari.

Wayarta da ta ɗauki ƙara ce ta sanyata dawowa daga duniyar tunanin da ta ta fi.

Yazeed ko YaseerOnde histórias criam vida. Descubra agora