Yazeed na fita daga gidansu Afnan motar Yaseer na kunno kai. ganin haka ya sanya Yaseer ɗin yin Rivas ya bi bayan Yazeed da gudu don dama neman shi yake yi tun jiya ya kasa ganinsa.Yazeed bai nufe ko ina ba sai gida. yana yin parking motar Yaseer na shigowa. Tamkar ya tashi sama haka ya shigo da motar.
Fitowa ya yi ba tare da ya rufe motar ba. Idanuwansa sun yi jajir tamakar wanda ya sha ƙwaya.Bai yi wata wata ba kawai ya kaima Yazeed da ke ƙoƙarin fitowa daga motarsa naushi a fuska.
Cikin zafin nama Yazeed ya fito tare da naɗe hannun rigarsa Ya naushi Yaseer dai dai shima inda ya naushe sa. Kafin kace me faɗa ya kacame tsakaninsu. Daƙyar maigadi da abokinsa suka shiga tsakaninsu.
Wani kallon tsana Yaseer yake yi wa Yazeed tare da nunasa da yatsa ya ce.
"Ka yi gangancin shiga gonata. Yazeed ka yi gangancin shiga rayuwata. Wallahi tallahi wannan karon ba zan taɓa ƙayle ka ba. Sai ka yi danasanin mallakar abunda ya zamo nawa a rayuwarka"Cikin rashin gane inda maganar Yaseer ɗin ta dosa ya sanya Yazeed yin murmushi ya ce.
"Ga dukkan alamu ka fara shaye shayen ƙwayoyi. Ka je idan ƙwayar da ka sha ta sake ka sai ka zo ka gaya min duk abunda kake so ka gaya min dan ni yanzu bana da lokacin magana da wanda baya cikin hayyacinsa. Sannan kuma magana ta ƙarshe da zan gayama. Wallahi duk lokacin da ka sake shan ƙwaya ka yi gigin taɓa ni sai ka kwamacema kiɗa da karatu. Wawan banza marasa hankali" ya faɗa tare da sakin tsaki ya juya ya wuce.Da sauri Yaseer ya sake shan gabansa.
"Tun muna yara kake samun duk wani abu da nake so a rayuwata. Wannan karon kam tun muna mu biyu ka sakarmin matata don Afnan tawa ce ni kaɗai. ni Afnan take so tun inda aka fito ba kai ba. Afnan ba za ta taɓa sonka ba. Ta aureka ne kawai don ta huce takaici amma zuciyarta ba kowa a ciki sai ni."
Yana kaiwa nan ya yi fu ya wuce ya bar Yazeed nan cikin wani irin ruɗaɗɗen al'amari.'shin me Yaseer ke nufi da cewa na shiga gonatai? Me yake nufi da cewa Afnan ta aureni ne don huce takaici? Wane takaici Afnan take son hucewa ne. Shin dama akwai wani Abu tsakanin Yaseer da Afnan ne ko me?'
Haka Yazeed ya riƙa jerawa kansa tambayoyin da ko alama ba shida amsar su.
Kasa shiga gida ya yi sai kawai ya koma cikin motarsa ya tada ya yi gurin Ammie.Ammie na zaune falo ita da Hafsa suna fira. Ganinsa kawai su ka yi tamkar wanda aka harbo.
Kallo ɗaya Ammi ta yi mishi ta gane cewa ba lafiya ba."Lafiya kake kuwa?" Cewar Ammie tana mai bashi dukkanin kulawarta garesa.
"Ammie me kike sani tsakanin Yaseer da Afnan?"
Nan take hankalin Ammie ya tashi. Shikenan abunda take gudu ya afku Yazeed ya gane gaskiya. Amma sai ta aro dakiya ta ce.
"Bangane abunda kake nufi ba yi min bayanin da zangane""Shin kina da masaniyar Yaseer da Afnan suna soyayya kika sani na aureta ko kuwa baki sani ba?"
Ajiyar zuciya Ammie ta yi.
"Eh to Afnan ta taɓa gayamin cewa Yaseer yace yana sonta ban cin kaima ka gayamata kana son zaka aureta"Ajiyar zuciya ya ɗan sauke ba tare da ya gamsu da bayanin Ammie ba.
"Toh Ammie me yasa kika sanya ta aure ni bancin kin san Yaseer ɗin take so?"
Murmushi Ammie ta yi. Cikin ranta tana cewa. 'He will never change wato har yanzu shi bai yin considering kansa sai Yaseer. Wannan karon kam ba za ta yarda ba, dole ne Yaseer ya ɗan ɗana abunda Yazeed ke ɗan ɗanawa idan aka hanashi abunda yake so aka bama Yaseer ɗin.
Basar da tunani ta yi tare da cewa. "Wannan yin kanta ne. Ni shawara kawai na bata cewa ta zaɓi wanda zuciyarta ta aminta da shi tsakaninku."
Haƙiƙa ya ji sanyi a zuciyarsa jin kalaman Ammie, duk da akwai tambayoyi da yawa da yake so ya yi game da lamarin amma ba zai yi ba tun da ta riga ta zama mallakinsa ba zai so ya dawo da hannun agogo baya ba.
"Alhamdulillah" kawai ya ce ya nufi ɗakinsa da ke cikin gidan dan sam ba zai iya komawa gida ba.
Kallonsa Ammie ta yi. "Yanayinka ya nuna min kamar dama kana son Afnan ɗin meye sirrin?" Ta faɗa cikin tsokana.
Shi sai lokacin ma shi ya fahimce kalar ruɗewar da ya yi.
"No Ammie, ni kin san bana son abunda zai ɗaga min hankali ne. Nafi so idan zan yi faɗa in yi sa da hujja"Dariya su Ammie suka yi. Hafsah na cewa.
"Ni Wallahi Ammie da naga shigowar sa har na ɗauka gobara ce, Ashe kishin ɗiyarki ne ya kaɓosa. kai gaskiya ni Ammie wannan salon soyayyar ta birgeni"Hararanta ya yi yana daure fuska
"Yaushe raini ya fara shiga tsakanina da ke? Allah zan ɓaɓɓala ki idan ba ki yi hankali ba""Dan ta fad'i gaskiyar ne zaka ɓallata to bisimlah" Ammi ta ce tana yi masa dariya.
Bai sake cewa komai ba ya wucewarsa ya barsu suna yi masa dariya.
Ɓangaren Yaseer kuma bai je gida ba shima ya juya ya ya ta fi gidansu Afnan. Ita ma sosai ya ɗaga mata hankali tare da gaya mata magangannu masu k'ona zuciya yana iƙirarin cewa sai ta yi nadamar auren Yazeed da ta yi ta barsa. Sosai taci kuka tana mai tausaya masa ganin yanda abun ya yi affecting ɗinsa sosai. Sai dai ko alama ba ta yi nadamar abunda ta aikata a garesa ba saboda shima haka nan ya yi mata wasa da tata zuciyar.
Mamie kuwa hankalinta ne ya yi ƙololuwar tashi ganin yananyin da Yaseer ya shiga.
Ba shida wani aiki sai kuka duk ya bi ya lalace saboda bala'in da ya jefa kansa ciki.
Ganin kuma yanda yake yi mata barazanar cewa zai ji ya faɗiwa Daddy shi ya yi wa Afnan fyaɗe da sunan Yazeed ya sanya dole ta je gurin boka aka daure bakinsa. Saboda boka ya ce, duk lokacin da Daddy ya ji cewa shi ya yiwa yarinyar fyade da sunan gudan jininsa to asiri ba zai sake tasiri kansa ba. Kuma ba zai sake yadda da shi ba har abada.
Ita kuwa ta san duk randa asiri ya bar tasiri kan Alhaji kuma ya daina yarda da ɗanta, ta san ƙaryarta ta riga ta ƙare.