Wayar da ke ruri Afnan ta tsurawa ido.
'To me ke shirin faruwa ne? Dole ne ma nasan maganar Yazid abba zai yi min toh me zance ma sa?' ta faɗa a azuciyarta.
Ganin ba ta da wata mafita ne ya sanya ta mike ta je ta wanke fuskarta, sannan ta nufe gurin kiran da Abban nata ke yi ma ta.
Da sallama ta shiga ɗakin mahaifin nata, bayan ta gaidashi ya karɓa kaman yanda ya saba.
cikin fari'arsa ya yi ma ta izini da ta zauna. Bayan ta zauna ne ya dubeta da kyau yana karantar yanayinta. "Me yake damun ki ne, naga idanuwanki sunyi ja haka Mamana?"
Murmushin yaƙe ta kakalo da iyakarsa saman leɓenta.
"Ba komai Abba daga bacci na tashi ne."
"Oh bacci kike yi ashe? ai kuwa da nasan bacci kike da ban takura maki ba sai in barwa mahaifiyarki saƙon ta gaya maki."
"Lah ba komai wallahi Abba, dama lokacin tashina ya yi. Zan kamawa Mommy aiki."
Ya ce, "yana da kyau hakan. Dama na kira ki ne kan maganar yaron da kika ce kina so."
Ras! Gabanta ya faɗi.
Ya ci gaba da magana, "Na ji daɗi sosai kan abunda yaron ya yi, saboda abunda ya yi shi ya nuna min cewa yaron kirki ne, kuma da gaske yake neman ki. kusan kwana biyu ko da yaushe sai ya kirani ya gaida ni. Yanzu haka ma bamu daɗe da ƙare waya da shi ba, kuma har mahaifinsa ya ba wayar muka yi magana da shi.
Mahaifinsa ya bani haƙuri kan cewa ba za su samu zuwa wannan satin ba, sai bayan sati biyu, saboda ankwantar da Yazid ɗin ne a assibiti ba shida lafiya. Kuma shi mahaifin zai yi tafiya a wannan satin sai idan ya dawo"
Gaban Afnan ya faɗi. Hankalinta ya yi matukar tashi, duk da cewa sosai ta ji daɗin maganar da mahaifin nata ya yi. Amma jin rashin lafiyar Yazid sai ta ji duk ta ƙara rikicewa.
Sam mahaifinta bai lura da halin da ta shiga ba ya ci gaba da magana.
"Yanzu dai na ce masu su yi haƙuri nan da sati biyu masu zuwa sai ayi maganar saboda nima tafiya zanyi a yau. Kuma ina tunanin zan yi kamar kwana goma ban dawo ba. Shi yasa na kira ki in gaya ma ki don infitar miki da hakkinki, duk da nasan cewa wannan maganar ba dole ne sai kin jita ba. Amma abun ne ya yi matukar birgeni, na ganin mutanen sun mutuncin kansu ba su barmu muka yi ta zuba idanuwa ba."
Afnan ta yi murmushin jin daɗi. Ba komai Abba. Adawo lafiya Allah ya tsare, ya kai lafiya."
"Ameen uwata" ya faɗa tare da cewa.
"Amma fa uwata baki kyauta ba da baki gayamin surukin nawa ba lafiya ba abun har da kwanciya a assibiti"
Rufe idanuwanta ta yi "Ai Abba ya ji sauƙi"
Murmushi ya yi. "Toh Allah ya bada lafiya"
ya faɗa tare da mikewa.
Ki kira min Mamanki lokacin tafiyata na matsowa"
"Toh abba" ta faɗa tare da mikewa ta bar falon tana hamdallah.
Karo ta ci da momyn zata shiga falon. Shi yasa bata ma tsaya gaya mata saƙon ba ta wuce abinta kawai.
Tana shiga ɗakinta ta faɗa kan gado tare da sake dialling number Yazid.
Abun ya ɗaure mata kai sosai na ganin still number bata zuwa. Tsaki ta yi tare da wulgar da wayar can ƙarshen gado tana jin wata damuwa na sake rufeta.
Haƙiƙanin gaskiya ta san tana muradin jin muryarsa tare da marmarin ganin kyakkyawar fuskarsa. To me hakan ke nufi na kasa samunsa da ta ke yi bayan kuma yana waya da mahaifinta? Kasa samawa kanta amsa da ta yi ne yasa ta bar abun cikin ranta. Tare da ɗaurawa kanta damuwa mai girman gaske.
Safiyar yau ma haka ta tashi da mafalkan Yazid iri iri, ji take yi yau sam bata iya rayuwa idan bata gansa ba ko ta ji muryarsa ba. Haka ta shirya ta je makaranta jikinta duk ba daɗi.
Bayan sun kammala lectures ne sun fito.
Tana zaune kan wata kujera tana Danna wayarta ta ji anmata sallama.
Amsawa ta yi ba tare da ta ɗago fuskarta ba. Jin mutumen ya kira sunanata ne ya yasanya ta yi saurin ɗago fuskarta ta saka cikin idanuwansa.....................!!!!!!!
