A yanda Afnan take ji ko daga bacci aka tadata zata iya zuwa gidan su Yazeed saboda bata jin gidan zai taɓa bace mata har abada,
Hon suka yi bakin get ɗin gidan, aka buɗe musu su ka shiga. parking Ibrahim ya yi duk suka fito suna biyar gidan da kallo.
Dai dai kofar da zata sada su da cikin gidan suka bi. Wani dattijon mutum su ka ci karo da shi zai fito daga ƙofar. Kallo ɗaya zaka yi ma shigar da ke jikinsa ta tabbatar ma da shine mamallakin gidan.
Ganin yanayin su ne yasa ya dakatar da su da cewa, "Ina zaku masu gidan fah duk basa nan, hala baku yi waya da hajiyar ba ne?"
Ya faɗa yana biyar su da kallon rashin sani.
Hannu Ibrahim ya bashi suka gaisa, yayin da momy ta gaidashi ya karɓa. Ita kuwa Afnan kallo kawai ta bishi da shi tana jin faɗuwar gabanta na ƙaruwar.
Dubansa Ibrahim ya yi tare da cewa "Dan Allah ko a ina za mu ga Yazid ne?"
"Yazid kuma! Ku kuwa me koke nema da Yazid?" Alhajin ya faɗa cikin tsananin mamaki yana mai jin wata fargaba na taso masa.
A hankali Mommy ta dubesa tare da cewa "ko kai ne mahaifinsa dan Allah"
Gyada musu kai ya yi yana mai tabbatar da zarginsa. "Tabbas kuwa ni ne mahaifinsa wani Abu ne ya faru?"
Ibrahim ya ce, "kwarai kuwa wani Abu ya faru mummuna kuwa saboda kanwata gata tana dauke da cikin shi na tsawon wata daya da kwanakki" ya faɗa yana nuna Afnan da ke tsaye kamar an dasa ta.
"What?" Ya fada da karfi, cikin tashin hanakalin da ya dade bai shiga ba. You most be mistaken, Yazid dina ba zai taɓa aikata wannan aikin ba, tun wuri ma ku je ku nemo wanda ya yi ma yarku ciki amma ba Yazid ba"
Afnan ta fashe da kuka. "Wallahi Allah shi ya min fyade Allah shi ne"
Jin maganar fyade da Afnan ta yi ba karamin tashin hankali Alhaji ya Ƙara shiga ciki ba,
Cikin mamaki ya sake kallon su "fyade fa ki ka ce?"
Afnana ta gyaɗa kai tana fyace majina,
Saida ya yi jim na lokaci ƙalilan sannan ya ce, "wannan magana bata yiyuwa a nan ku shigo daga ciki"
Ya juya suka bi bayan shi,
Falon shi suka shiga suka zazzauna. Ahankali ya sake dubin Afnan. "Kin dai tabbatar da abunda ki ka faɗi gskiya ne ko?"
Sake gyaɗa kai ta yi "eh gaskiya nake faɗa wallahi"
Wayar shi ya ɗauko ya kira Ɗan nashi. "Kazo yanzu ina falo ina nemanka"
Cikin mintunan da basu wuce biyu ba yaron ya sauko daga sama cikin tafiyar shi ta ƙasaita.
Hannuwansa duka biyu suna cikin aljihun wandonsa.
Sallama ya yi ba tare da ya kalle mutanen da ke zaune wurin ba.
Gun mahaifinsa ya nufa yana magana kamar baya son yi.
"Abba gani kana nemana"
Cikin nutsuwa mahaifin nashi ya dube shi tare da nuna masa Afnan. "Ka san yarinyar nan?"
Idanunsa ya sanya cikin nata ya ɗan kalleta kaɗan kafin ya ce. "Ban santa ba Abba"
Wani irin kallo mahaifinsa ya masa "kar ka raina ma mutane wayo. Baka santa ba ta yaya ta yi cikinka ta sanadiyar fyaɗe?"
Yanda ya sake duban Afnan kawai zai tabbatar maka da cewa kalaman mahaifin nasa ba ƙaramin ruɗa shi suka yi ba.
Ita kanta Afnan ɗin tana haɗa ido da shi tun a karon farko ta ji wata irin mumunar faɗuwar gaba. Saboda ganin al'amarin da ke shirin faruwa da ita. Saboda randa take duniya bata taɓa ganin halitta irin tasa ba a cikin duniyarta ba.
Haka Ibrahim da tune ya kasa ɓoye mamakinsa saboda ganin abokin aikinsa da ya yi.
Cikin tsananin tashin hankali Yazeed ɗin ya furta
"Dad fyaɗe fa ka ce? Why! when! I mean ni ban ma taɓa ganin wannan yarinyar ba how is this possible?" Ya jero kalamansa cikin ruɗani.
Rayuwar Ibrahim da ta gama ɓaci bai san lokacin da ya cakume wuyansa ba yana cewa.
"Karya ka ke yi macuci azzalumi dama shine dalilin da yasa ka ce ka fasa aurenta saboda ka ɓata mata rayuwa to wallahi kotu ce zata rabamu da kai. Kuma ka ci amanar amincin da ke tsakanina da kai macuci kawai"
Cikin tsananin ɓacin rai ya ture hannuwan Ibrahim daga jikinsa saboda ransa ya gama ɓaci, sai dai sosai yake ƙoƙarin danne ɓacin ran nasa. "dakata Ibrahim ka daina jifata da miyagun kalmomi kada ka yi danasani daga baya. Wallahi tallahi ban taɓa ganin wannan yarinyar ba" ya faɗa idanuwansa kan Afnan da keta kuka.
Kuka take sosai wanda bata yi irinsa ba tun faruwar abun. Tabbas ita kanta tasan bata taɓa ganinsa ba kamar yanda ya ce shima ba taɓa ganinta ba. ba toh amma me ke shirin faruwa da ita ne? ta yiwa kanta tambaya kafin ta yi magana "Ya Ibrahim ba shine ba"
Baki ɗaya kallon ta suke yi. Ibrahim ya yi kanta ya fara jibgarta tamkar wanda Allah ya aiko "don ubanki yau sai kin gaya min wanda ya miki cikin nan ko in kashe ki a huta" yanda yake yi mata ba ƙaramin tsorata halittun da ke wurin ya yi ba amma ko motsi kasawa suka yi su duka sai Mommy da ke kuka tana cewa. "Ku Kama min shi kada Ya illata ta"
Ba wanda ya yi yunƙurin yin hakan daga cikinsu ganin haka yasa cikin azaba Afnan ta ce.
"Wallahi shi ne ya yi min ya ce kuma idan na faɗa kashe ni zai yi"
Jin abunda ta sake faɗa ne ya sanya Ibrahim ya saketa cikin mutuwar jiki, ya koma kan kujera ya zauna yana dafe kansa da ke juyawa saboda tsananin tashin hankalin da yake ciki.
Yazid kansa cikin tashin hankali ya ce, "ni muka yi haka da ke?"
Gyaɗa kanta ta yi alamar eh.
Kafin kace, me tuni mahaifin shi ya kwashe shi da wani irin wawan mari, "irin wannan tarbiya na baka ko? Me yasa koda yaushe ka ke so ka ɓata min suna ne? Yanzu abun naka har yakai ga fyade da kuma gargaɗin yin kisa?" Cewar Mahaifinsa yana mai zaunawa shima ya dafe kai.
Afnan kam tsanani tausayin kanta da na yaron ne ya kama ta saboda ta san ta ci amanar shi ba kadan ba, sai dai dole ce ta sanya ta yi hakan don ta ceci kanta daga azabar Ibrahim.
Muryar da bazata taɓa mantawa a rayuwarta ba ta ji tana doso su. "Wai dad hayaniyar me ake yi ne?" Ya faɗa yana saukowa shima kan benen gidan.
Mikewa Afnan ta yi tsaye ba tare da ta san ta yi ba. Kukanta nan take ya tsaya cak ta shiga nuna mai yin maganar "wallahi wannan Yazid ɗin ne yamin fyaɗe. Nasan ban yi kuskure ba gidansu na zo. Ya Ibrahim wannan ne" ta faɗa tamkar mahaukaciya.
Baki ɗayan su kallonsa suka yi,
Cikin mamaki.
"Ikon Allah, YASEER ɗin ne kuma yanzu ya miki fyaden? Toh me ki ke nufi ne? Su fah ba 'yan biyu ba ne kuma basa Kama da juna. Kai wannan yarinyar Sam baki da gaskiya kawai ki faɗi tsakani da Allah wa ya yi miki fyaɗe a cikin su Yazeed ko Yaseer?.
Ni kaina abun ya ɗauren kai ya aka yi haka ne, wa ya mata fyaɗen YAZEED KO YASEER? Masu karatu ku duba min lamarin nan.
