Babi na talatin

614 47 1
                                        


Wata uwar ashar Mamie ta kwararo, tare da ɗora hannu a kai ta yi zaman 'yan bori.

Daddy bai ce mata komai ba ya kaɓa babbar rigarsa ya yi sama.

Wani irin kukan baƙin ciki take yi. Saboda baki ɗaya plan ɗinta na da take shiryawa shekara da shekaru yau ya rushe. Wata irin tsanar Afnan ta riƙa jin tana rufeta saboda ganin take yi duk itace sanadiyar komai. Dan da ta yi haƙurin abunda Yaseer ya yi mata da yanzu an wuce gurin. Ita yanzu ba ma ta Yaseer take yi ba ko Nabeela ta kanta take yi.

Tafi ƙarfin awa ɗaya zaune tana saƙawa da kwancewa a gurin.  Ganin bata samo wata mafita ba ya sanya ta ta tashi ta yi ɗakinta tana mai jin kamar duniyar nan ta kusa tsaya mata.

Ƙarin baƙin ciki tana shiga ɗakinta ta ci karo da Yaseer wanda ya kasa zaune ya kasa tsaye. jira kawai yake ya ji ance Afnan zata zama mallakinsa. Kallo ɗaya  Mamie ta yi masa sai ta ji  duk hankalinta ya sake  tashi saboda ita a halin da take ciki ba ta ma san ta inda zata fara yi masa bayani ba.

Shi kansa Yaseer yanda yaga Mahaifiyarsa ta shigo ɗakin ba ƙaramin ruɗewa ya yi ba nan take sai ya sha jinin jikinsa ya ce cikin ƙarfin hali.
"Mamie ya kuka yi da shi? Ya amince ni zai nemawa Afnan ɗin ko ya?" Ya yi tambayar cikin ruɗewa.

Zama kawai Mamie ta yi ta samu kanta da matsanancin tausayin ɗan nata ganin yanda  duk ya ɗaga hankalinsa kan wannan lamarin.

"Aikin gama ya riga ya gama Yaseer, mun riga da mun makaro."

"Me kike so ki gayamin ne Mamie?  Ba dai kina nufin kin kasa convincing Dad ba?"

Girgiza masa kai ta yi. "Ba haka ba ne Son wai an riga da an ɗaura auren Afnan da Yazeed yau ɗin nan"

Sai da ya yi mutuwar wucen gadi kafin ya sanya wata ƙara tare da zubewa ƙasa yana wani irin kuka mai cin rai da zuciya.

Hankalin Mamie ya yi masifar tashi, tunda take duniya bata taɓa ganin Yaseer ya shiga hali irin na yau ba.

Zubewa ta yi itama kusa da shi tana cewa. "Na shiga ukuna yau ni Zuwairah. Yaseer me kake son ka maida kanka ne kan wannan lamari? Wayyo ni Allah dan Allah Yaseer kada ka kashe kanka kan wannan. Wallahi na daukarmaka alƙawarin sai na kashe wannan auren ko da ina yawo tsirara."

Wani kallo ya yi mata da idanuwansa da suka rine suka fita ainihin kalarsu ta halitta.

"Ba zaki iya yi min komai ba Mamie. Amma wallahi  ki sani ni Yaseer sai na ɗauki mataki a hannuna ko da kuwa yana nufin zan halaka Yazeed ne. Afnan tawa ce ni kaɗai, ba shegen da ya isa ya rabani da ita most especially ma Yazeed. I hate him to the baddest level. I hate him Mamie he snatched  everything from me. Wannan karon Wallahi tallahi ba zan ƙyalesa ba"
Ya faɗa tare da tashi ya fita daga ɗakin kamar guguwa.

Biyar bayansa Mamie ta yi tana kiran sunansa saboda ta san zai iya aikata abunda zai sanya su kuka su dukansu.

               
A Bangaren Yazeed kuwa tunda aka shaida masa an daura aurensa da Afnan ya same kansa cikin wani cakuɗaɗden yanayi.
Yayan mahaifiyarsa Alhaji Aminu ke ba shi labarin yanda abun ya kasance a gidan Ammie da suka haɗu.

"Kaga ikon Allah kuma ko Yazeed daga zuwa neman aure sai aka daura aure. Ni lokacin da Alhaji ya kira ni kan za a je a nema ma aure sai na sanar da Sani. Ashe shima tare da Yayansa Alhaji Hamza da Tukur da kuma Amininsa Alhaji mukhtar suka je. In takaice maka dai kusan mu goma sha biyu muka je gidansu yarinyar nema maka aurenta.

Mahaifin yarinyar na ganinmu haka. Ya buƙace idan mun zo da kuɗdin sadaki ma za a iya daura auren a lokacin saboda dama zuwa jibi yake so a daura auren idan son samu ne.

Ka san Alhaji Sani da rashin son bid'a shi ma  dama akwai kuɗi a tare da shi nan take ya fitar da dubu ɗari ya bada matsayin sadaki kuma ya wakilce daurin auren ana sallame sallar la'asar aka ɗaura Aurenku nan masallacin da ke haɗe da gidansa.

Abun yayi matuƙar sha'awa cikin ba a gayyace mutane ba, amma idan ka ga taron da aka yi sai abun ya baka mamaki.

Yanzu kum maganar tarewa sai yanda kuka tsara kaida mahaifinka. Shi mahaifin yarinyar ya ce ko yaushe kuke da buƙata tarewarta ba damuwarsa ba ce.
Amma mahaifinka ya yi min magana wai yana tunanin nan zaka tare cikin gidanku sai ka z meauna part din ummanka kafin a karkare gyaran gidanka sai ku koma can har ita  Nabeelar da aka ce akwai maganar aurenta kanka idan ta kammala karatu."

Jin jina kai kawai Yazeed ya yi jin wannan al'amari mai kama da almara.
Ammie kanta ta yi mamaki sosai da ta ji wannan labarin.
Bayan Alhaji Aminu ya wuce. Yazeed ya daɗe sosai wurin Ammie suna fira.

Washe gari ma tun da sassafe Mamie ta isa gurin Na kan tudu. Saboda jiya da ita har Yaseer ba wanda ya runtsa.
dan ma Allah yasa ta samu ta shawo kan Yaseer da Allah kaɗai ya san ta'asar da zai aikatawa a jiyan.
 
Zaune take gurin bokan "Ranka ya daɗi ka ji jiya an daura auren  yarinyar ko?"

Wata irin dariya ya yi.  "Naga komai"

Wani kallo ta watsa masa. "Kuma shi ne ka gani amma ka kasa yin wani Abu akai?" ta yi magana cikin ɓacin rai.

Dariya ya sake kyalkyacewa da ita. "Al'amarin ne ya fi karfinmu"

Ƙara gyara zama ta yi
"Ban gane al'amarin ne ya fi karfinku ba."

Daure fuska ya yi sannan ya ci gaba da magana.
"Wannan al'amari da kike gani akwai wani boyayyen abu a tattare da shi, wanda ni kaina na kasa gane ko mi ye. Saboda waɗannan yaran iyayensu na tsaye a kansu musamman ma shi Yazeed kamar yanda kika sani mahaifiyarsa sam bata wasa gurin nema masa tsari.

Wani irin zufa ne ya karyewa Mamie idan bata mantaba wannan shine boka na uku da yake ce  mata haka game da Yazeed. Shi yasa ta daina kashe kuɗinta kansa sai dai mahaifinsa.  Dan da magani na cinsa da yanzu baya doron duniyar nan.

"Toh yanzu miye mafita. Saboda ni ina son auren nan ya mutu kafin yarinyar ta tare. kai ni boka koda ba za ta aure Yaseer ɗin ba a dai kashe auren. Saboda idan yarinyar nan ta tare har ta haihu da Yazeed to karyata ta ƙare."

Wata dariya bokan ya yi.
"Ba makawa sai ta tare tunda aka riga aka daura auren. Sai dai zan baki wani magani  ki zuba mata a ƙofar ɗakinta da zaran ta tsallaka maganin   to zata riƙa jin tsoronsa a gurin kwanciya.
Shi kuma za a sanya mishi wani magani a ruwa da ya sha za a sanya masa matsananciyar sha'awa da rashin haƙuri kan lamarin yarinyar. kwanda cikin ƙanƙanen lokaci zai iya sakinta ko kuma ya yi mata abunda iyayenta da kanta zasu raba auren.

"Toh ni boka idan ya nemeta ta ƙarfi fa?" Ta tambaya cikin damuwa.

"Kada ki damu namijin da ya san kansa baya neman mace ta ƙarfi. Ba zai taɓa nemanta ta ƙarfi ba saida amincewarta"

Wannan abun Sam bai yi ma Mamie daɗi ba. Dan dai ta san ba ayi ma  boka gardama ne kawai ya sanya ta Amshe maganin.........

Yazeed ko YaseerDove le storie prendono vita. Scoprilo ora