Jin sunan wanda ya ambata yasa ta yi kamar ba za ta karɓa ba.
Sai kuma dai wata zuciya ta bata shawarar da ta karɓa.
Amsa ta yi ta warware tana karantawa kamar haka.
"Ban san ta in da zan neme yafiyar ki ba Afnan, kamar yanda ƙwayar idona ba za ta iya sake haɗa gani da taki ba.
Haƙiƙa ni na kasance butulu mai rama sharri da alkhairi. na san ban cancanci yafiyarki ba Afnan, saboda na cutar da ke mafi muninin cutarwa a rayuwa.
Amma dan Allah ina roƙon ki da ki dubi girman Allan da ya sauya miki da mutum mafi alkhairi a rayuwarki da ki yafe min abunda na aikata a gareki.
Haƙiƙa idan har ba ki yafe min ba rayuwata tana cikin haɗari babba.
Afnan ki sani wallahi ban taɓa son wata 'ya macce a duniya ba kamar yanda nake sonki, kuma na san ba komai ya sa haka ba sai irin zaluncin da na aikata a gare ki tun farko.
Dan Allah Afnan ki yafe min kuma ki taya ni roƙon Allah da ya sassautamin wannan musibar ta kaunarki da ta addabe zuciyata. Tabbas na ga jarabawa babba a rayuwa dan idan har Allah ya bar ni ma a haka nagode masa saboda ko ba komai ban nakasa duka ba Afnan.
Sannan kuma ina mai yi miki alƙawarin cewa zan tafi nesa dake in da ba za ki sake ganina ba sai idan wata ƙaddarar ce ta sake haɗamu. Amma insha allahu ba zan sake sada kaina da inda kike ba har Abada.
Sannan ina so ki sani cewa duniyar nan babu wata halitta da ta san ƙima da mutuncin ɗan adam kamar Yazeed. Dan Allah ki riƙesa amana ki kuma sosa kamar yanda yake son ki, duk da nasan kema kina son sa kamar yanda na fahimta a baya bayan nan duk da son zuciyata ya hana min yarda da hakan.
Tabbas na san cewa ni kaina ba zance ina miki son da Yazeed yake yi miki ba saboda cewa haka tamkar sake son kaina ne zan yi.
Daga ƙarshe kuma ina muku addu'a Allah ya kauda fitina tsakaninku, ya kuma ba ku zur'ia ɗayyaba mai albarka.
Afnan ina miki fatan alkhairi a duk in da rayuwa zata kai ki.
YASEER.
Wata irin zufa ce ta riƙa karyewa Afnan. Magangannun Yaseer sun shiga jikinta sosai sun haifar mata da wani al'amari mai girma a zuciya.
Sosai hawaye suka shiga zubowa daga idanuwanta tana mai tuna rayuwarta ta can baya da ta tsara cikin bijirewa wani umurni na ubangijinta a kanta. "RAYUWA KENAN" ta furta a hankali tare da shafe hawayen idanuwanta.
Amsar takardar hannunta Yazeed ya yi tare da yaga ta ya janyota jikinsa ya rungumeta sosai yana shafa bayanata.
"Ki yafe masa dan Allah tun da ya neme gafararki. Idan kika ga halin da yake ciki za ki tausaya masa Afnan just forget and forgive please" ya faɗa muryarsa ɗauke da wani yanayi na daban.
"Na yafe mishi Ya Yazeed har cikin zuciyata. Amma ba zan taɓa manta abunda ya rabani da shi mafi daraja ba a rayuwata ba.
Ya Yazeed ba zan taɓa mantawa da wannan zafin ba. Ko da yaushe na tuna na kan ji na tsane dukkanin duniyata Ya Yazeed."
Ta faɗa tana mai furzar da wani iska mai ɗauki da tsantsar zafin da take jin na taso mata a zuciya.
"I will make you forget it Afnan I promise." Ya faɗa tare da haɗe bakinsa da nata guri ɗaya. Sosai ya shiga sarrafa harshenta da laɓattan bakinta tamkar babu gobe.
Saida ya tabbatar da ya kashe mata dukkanin ƙuzari da ke tare da gangar jikinta sannan ya sanya hannu ya kashe wutar ɗakin.
Cikin ƙanƙanen lokaci ya fara karantar da ita wani darasi mai girma da faɗin da babu wanda yake fahimtar sa sai ma'auratan da so da ƙauna ya zama linzami mai girma a tare da su.
Asuba ta gari Yazafnah.
Washe gari tun da Yazeed ya tashi yake kallon Afnan dake ta sharar baccin wahala. Wani irin sonta da ƙaunarta ne ke ƙara mamaye dukanin wata gaɓa ta jikinsa.
A hankali ya duƙa tare da sumbatar laɓɓanta sannan ya tashi ya shiga bayi ya yi wanka tare da ɗoro alwala ya fito.
Ruwan hannunshi ya shiga yayyarfa mata a fuska.
Buɗe idanuwanta ta yi suka haɗa ido da shi.
Wani mayen murmushi ya jefe ta da shi mai nuna mata cewa ba ƙarya ko ɗaya cikin kalamansa na daren jiya da ya riƙa gaya mata.
Ƙara duƙunƙunewa ta yi saboda wata irin kunyarshi da take jin tana rufe sassan jikinta.
"Ki tashi kar lokacin sallah ya wuce mu. Ko sai na zo na taimaka miki?" ya faɗa yana mai takwankwahe hannayen rigarsa dan ɗaukarta idan ba za ta iya tashi ba kamar yanda yake hasashe.
Tana ganin ya nufo gefenta da niyar daukarta ta yi saurin dafa gado ta miƙe daƙayar ta yi hanyar bathroom tana sakin murmushi, shima murmushin ya yu tare da binta da kallo har ta shige.
Ko da ta fito har ya sallame sallarsa saboda gasa jikinta da ta tsaya yi. Sai dai jin an tada sallah wani masallaci yasa ta fahimce raka'atainil fajar ya yi.
Da sauri ta sanya kayanta ganin yana jiranta sunyi sallar.
bayanshi ta bi ya kabbarta asubar suka yi a tare.
Sai da suka ƙare azkar ɗinsu, sannan ya juyo ya kalleta tare da ɗora kansa saman kafaɗarta.
"Ina sonki sosai Afnan." Ya faɗa tare da sanya idanuwanshi cikin nata.
Ita ma kanta ta ɗora saman nasa.
"Ina son ka Ya Yazeed son da ban taɓa yi wa kowa kwatankwacin irinshi ba"
"Har da Yaseer?" Ya faɗa ba tare da ya san maganar ta fito ba. Amma tabbas yana da yaƙinin cewa maganar zuciyarsa ce da bai ba wa umurnin fitowa ba ta fito dan karan kanta.
Haɓarsa ta ɗaga da hannayenta tana mai ƙara sanya idanunta cikin nashi sosai dan ya fahimce yanda take jin sonsa cikin ranta.
"Ka daina kwatanta son da nake yi ma da wanda na yi wa Yaseer a baya.
Kai sonka nake yi tsantsar son da babu algussu a cikinsa Ya Yazeed. Yaseer kuwa mayaudaran kalamanshi da kyawunshi su suka ruɗa neni har na yi tunanin sonshi nake yi.
Amma wallahi Ya Yazeed ka yarda dani, kai ka ɗai nake yiwa son da nake jin tamkar ba zan iya rayuwa idan har babu gauruwar nunfashinka tare da nawa ba."
Kalamanta ba ƙaramin farin ciki da kashe masa jiki suka yi ba. Bai ƙi ta kwana tana gaya masa haka ba. Janyota ya yi jikinsa dukkaninta
Ya fara kissing ɗinta da dukkanin iyawarsa dan ya nuna mata yanda ƙaunarta ke tafiya da dukkanin nunfashinsa.
Wannan karon ita ma ba ta yi ƙasa a guiwa ba ta fara nuna masa yanda take jinsa a zuciyarta. Cikin ƙanƙanen lokaci wasa ta chanja.
Ganin haka ya sa na tarkato kayana na bar musu gidansu don su samu damar kwasar soyayyarsu da kyau da kyau ba tare da kowa ya sa masu ido ba.
A gurguje please.
Bayan wata biyu.
Ganin Daddy bai da niyar dawowa da Mamie, ko sake aure ya sa su Afnan ganin sun jajirce har ya sai da suka ga ya dai daita kansa da shi da Ammie.
Ba a ɗauki wani lokaci mai tsawo ba aka ɗaura auren Daddy da Ammie.
farin ciki gurin Yazeed baya ma faɗuwa ganin iyayen nasa a inuwa ɗaya matsayin ma'aurata abunda tun yana ɗan ƙanƙanensa bai gani ba.
Rayuwa juyi juyi.
Yaseer rayuwa ta chanja masa, sosai ya rungume ƙaddararsa yana jinyar kansa yanda ya kamata. Mahaifinsa da ba ƙarfi garesa sosai ba dole shi ya riƙa matsayin ginshiƙinsa.
Nan cikin dangin babansa ya samu wata yarinyar da ya ji ta kwanta masa a rai su ka dai daita kansu.
Mamie ma ta yi sa'a ta samu wani mai mata biyu ita ce ta uku ta aura duk da ba wani arziƙi ne da shi na azo a gani ba. Nabeela ma ana ta shirye shiryen bikinta wanda za a haɗe da na Yaseer wata mai zuwa.
Afanan kuwa rayuwa ta musu daɗi
loacin ma tana fama da yaron cikinta ɗan wata huɗu.
Sosai Yazeed ke nuna mata soyayya tamkar ya cinye su ita da abunda ke cikin cikinta.
Bayan wata tara ta sumɓulo yaronta kyakkyawa sak kamar ubanshi. ranar suna yaro ya ci sunan Mahaifinta suna mishi laƙani da Ammar.
Haka dai suka gudanar da rayuwarsu cikin soyayya da ƙaunar juna.
Tammat bi hamdulillahi.
Nan na kawo ƙarshen littafina Yazeed ko Yaseer. Allah ya yafe min kura kuran da na yi a ciki.
Fatan alkhairi ga dukkanin makarantata Allah ya bar ƙauna. nagode sosai da sosai. Sai kun ji ni a sabon littafina na gaba nan bada daɗewa ba insha Allahu
Taku har kullun
Ayshart one.
